2019: Obasanjo ya zabi Jam’iyyar da zai shiga
Kungiyar tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ‘CNM’ ta zabi ta hade da jamiiyyar ADC domin gogayya da sauran jam’iyyu a zabuka masu zuwa.
Idan ba a manta ba an Kaddamar da sabuwar Kungiyar da tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya kafa mai suna ‘Coalition for Nigeria’ ranar 31 ga watan Janairu a dakin taro na gidan Shehu Musa ‘YarAdua’, Abuja bayan kunne da ya ja wa shugaban Buhari da kada ya nemi tsayawa takara a 2019.
Tsohon gwamnan jihar Osun Olagunsoye Oyinlola ne shugaban kungiyar.
Gwamnoni 10 da tsoffin da ‘yan siyasar kasar nan duk sun nuna goyon bayan su.
A halin da ake ciki, Obasanjo ya bayyana cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari da jam’iyyarsa ta All Progressives Congress (APC) dake tafiyar da mulki sun dauki Najeriya a matsayin wawaye.
KU KARANTA KUMA: 2019: Kungiyar Dattawan Arewa za ta yi taron makomar siyasar yankin
Obasanjo yayi korafin cewa arzikin yan Najeriya da dama ya lalace a shekaru uku da suka shige duk da ikirarin aasin haka da Buhari da APC sukayi, yayi kira ga mutane da suyi kokarin korarsu a 2019.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng