Fadar Shugaban Kasa Ta Caccaki Mutanen Buhari da Suka Hade da Atiku a ADC
- Bayo Onanuga ya ce wasu daga cikin ‘yan ADC na yanzu sun bar APC mai mulki tun tuni kuma ba su da tasiri a jam’iyyar
- Ya zargi Rauf Aregbesola, Hadi Sirika, Abubakar Malami da Rotimi Amaechi da zama marasa biyayya ga APC tun kafin yanzu
- Onanuga ya ce sabon kawancen ba shi da manufa sai ƙiyayya da shugaba Bola Tinubu, kuma zai kare cikin rashin daidaito
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mai magana da yawun shugaba Bola Tinubu, Bayo Onanuga, ya ce kawancen jam’iyyun adawa da ke ƙoƙarin ƙwace mulki a 2027 ba zai yi nasara ba.
Onanuga ya ce dama tun tuni wasu daga cikin fitattun ‘yan siyasar da ke cikin kawancen sun bar jam’iyyar APC shekaru da watanni da suka gabata.

Source: Twitter
Legit ta tattaro bayanan da Bayo Onanuga ya yi ne a cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na X a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Onanuga ya bayyana haka ne yayin da rahotanni ke nuna cewa 'yan adawa za su yi amfani da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin fuskantar Tinubu.
Ya zargi ‘yan siyasar da suka shiga kawancen da ƙoƙarin ƙwace mulki ne kawai saboda son rai, ba don jinƙai ko ci gaban ‘yan Najeriya ba.
An caccaki mutanen Buhari da suka koma ADC
A cewar Bayo Onanuga, Rotimi Amaechi ya bar APC tun bayan faduwa a zaben fidda gwani na shugaban kasa a 2022, inda ya gaza samun tikitin jam’iyyar.
Haka kuma ya ce tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami ya daina nuna goyon baya ga APC tun bayan faduwar gwamnan Kebbi da yake mara wa baya.
Sai dai Legit Hausa ba ta da masaniyar Malami ya shiga takarar gwamna a jihar Kebbi, da farko ya nuna sha'awar kujerar, amma ya ki sauka daga minista.
Bayo Onanuga ya ƙara da cewa Hadi Sirika da ke fuskantar shari’a kan kwangila da zargin cin hanci, yana tare da ADC yanzu.
Ya bayyana cewa Aregbesola kuwa an kore shi daga APC saboda zagon ƙasa da ya yi wa jam’iyyar a zaben Osun na baya.
Hadimin shugaban kasar ya ce:
“Wasu daga cikin mutanen da ke cikin ADC yanzu ba su da wata alaka da APC, kuma tun tuni suka fita daga jam’iyyar.
"Bai kamata ‘yan Najeriya su bari a ruɗe su ba."
Onanuga ya ce ADC na kiyayya da Tinubu
Onanuga ya ce John Odigie Oyegun da Kashim Imam na daga cikin tsofaffin ‘yan siyasar da suka kauracewa APC saboda faduwa a siyasa.
Ya ce tuni Oyegun ya zama na gaba gaba a kawancen tun farko, yayin da Imam ya fice daga APC bayan kasa samun tikitin mataimakin shugaban kasa.
Bayo Onanuga ya bayyana cewa kawancen ba shi da wata sahihiyar manufa sai ƙiyayya da Tinubu.

Source: Twitter
A cewarsa, hakan na nuni da cewa ba za su iya jan ragamar ƙasar cikin gaskiya da rikon amana ba.
Ya ce mutanen na ƙoƙarin haɗuwa ne ba domin wani abu ba, sai ƙiyayya da Tinubu, kuma ba za su iya ci gaba da zama cikin jituwa ba.
Onanuga ya kara da cewa:
“Ina tabbatar muku, wannan kawancen zai rugurguje nan ba da jimawa ba, domin ba su da hadin kai ko maƙasudi guda da ke haɗa su sai son zuciya,”
Legit ta tattauna da Bilya Yahaya
Wani matashi dan jam'iyyar PDP a jihar Gombe, Bilyaminu Yahaya ya zantawa Legit cewa martanin fadar shugaban kasa alama ce ta jin tsoro.
Matashin ya ce:
"Ai duk abin da baka damu da shi ba, ba za ka yi magana a kan shi ba.
"Har yanzu ban yanke matsaya kan shiga ADC ba, amma lokaci ne zai nuna."
ADC ta ce za ta kawo sauyi a Najeriya
A wani rahoton, kun ji cewa sakataren masu hadaka a ADC kuma tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola ya yi jawabin fara aiki.
Rauf Aregbesola ya ce za su yi kokarin kawo sauyi a Najeriya idan suka samu nasara a zaben 2027 mai zuwa.
Tsohon ministan ya bayyana cewa za su samar da hanyoyin inganta ilimi da sauran abubuwan more rayuwa a Najeriya.
Asali: Legit.ng


