Asiri Ya Tonu: Tsohon Gwamna da Ya Bar APC Ya Fallasa Shirin INEC na Murde Zaben 2027

Asiri Ya Tonu: Tsohon Gwamna da Ya Bar APC Ya Fallasa Shirin INEC na Murde Zaben 2027

  • Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya ce Najeriya ta lalace kuma tana buƙatar cikakken canjin shugabanci na-gari
  • Amaechi ya ce ya yi murabus daga APC a daren Talata, yana mai zargin 'yan jam'iyyar da satar kudin jama'a ba tare da mafadi ba
  • Rotimi Amaechi ya kuma zargi jam'iyyar APC da hukumar INEC da haɗin baki domin ganin sun murde zaɓuka masu zuwa a ƙasar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - A ranar Laraba, tsohon ministan sufuri, Mai Girma Rotimi Amaechi, ya bayyana cewa Najeriya ta lalace gaba ɗaya kuma tana buƙatar cikakken canji.

Amaechi, wanda tsohon gwamnan jihar Rivers ne, ya kuma zargi jam'iyyar APC mai mulki da hukumar INEC da haɗin baki domin murde zaɓuka masu zuwa a ƙasar.

Tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi ya zargi INEC da APC da shirin murde zabuka masu zuwa
Tsohon gwamnan Rivers, kuma tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi. Hoto: @ChibuikeAmaechi
Source: Facebook

Rotimi Amaechi ya ce Najeriya ta lalace

Kara karanta wannan

Haɗaka: Bayan ficewar Malami, ministan Buhari, Amaechi ya watsar da jam'iyyar APC

Ya yi wannan zargin ne yayin da yake magana da manema labarai jim kadan bayan kaddamar da kwamitin riko na jam'iyyar ADC a Abuja, inji rahoton Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tsohon ministan ya ce abubuwa sun tabarbare har ta kai 'yan Najeriya ba za su iya samun abinci ba saboda rashin kuɗi, yana mai cewa hauhawar farashi na kara karuwa.

Amaechi, wanda ya ce ya yi murabus daga APC a daren Talata, ya ce yayi mamaki yadda jam'iyyar ba ta kore shi ba duk da ya gargade ta cewa kada a sake tura masa goron gayyata zuwa tarurruka.

Amaechi ya zargi INEC, APC da murde zabe

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya yanke shawarar yaki da gwamnati tare da taimaka wa 'yan adawa su canja gwamnati a 2027, Amaechi ya ce:

“A’a, ba wai batun canza gwamnati ba ne, idan batun canza gwamnati ne, babu buƙatar canza gwamnati ai, yanzu muna magana ne a kan canza Najeriya ne.
“Najeriya ta lalace. Mutane ba za sa iya cin abinci. Mutane ba sa iya siyan abinci. Babu kuɗin siyan abincin. Komai ya kare yanzu. Hauhawar farashi yana kara karuwa.

Kara karanta wannan

Ministan Buhari, Malami ya fice daga APC, ya zaɓi sabuwar jam'iyyar haɗaka

"Kuma gwamnatin tarayya tana shagaltar da kanta tana ƙoƙarin ƙwace zaɓe. INEC tana taimaka musu wajen murde zaɓe."
Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi ya sanar da ficewarsa daga APC zuwa ADC
Rotimi Amaechi ya ce ba zai iya zama cikin APC ba, inda ya koma ADC. Hoto: @ChibuikeAmaechi/X
Source: Twitter

Amaechi ya zargi 'yan APC da sata

Da aka tunatar da shi cewa yana cikin gwamnatin APC kuma ya shafe shekaru biyu a jam'iyyar ƙarƙashin Shugaba Bola Tinubu, ya ce ya miƙa takardar murabus ɗinsa daga jam'iyyar a daren Talata.

Amaechi ya ce:

“Na bar APC a daren jiya. Ban taɓa halartar taro ko ɗaya ba. A karo na ƙarshe da suka gayyace ni, na gargade su. Na ce, idan kuka sake gayyata ta zuwa wani taro, to za ku ga abin da zan yi.
"A gaskiya, na yi mamaki ma cewa ba a kore ni ba domin na gargade su a rubuce, kuma ba su sake gayyata zuwa wani taro ba."

Amaechi ya ce ba zai iya ci gaba da zama a cikin jam'iyyar da mafi yawan 'ya'yanta barayi ba ne, kuma babu wanda zai iya cewa komai a kai.

Abin da Amaechi ya fadawa Tinubu a zaben 2023

Kara karanta wannan

Maryam Shetty ta tofa albarkacin bakinta kan murabus ɗin Ganduje daga shugabancin APC

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Rotimi Amaechi ya ce tun farkon lokacin yakin neman zaɓen 2023 ya sanar da Bola Tinubu cewa ba zai mara masa baya ko ya zaɓe shi ba.

A cewarsa, ya tsaya kan wannan matsaya ne saboda a ra’ayinsa, Tinubu ba shi da ƙwarewar da ake bukata domin jagorantar Najeriya yadda ya dace.

Tsohon gwamnan jihar na Rivers kuma tsohon ministan sufuri ya ƙara da cewa bai ɓoye wannan ra’ayi ba, domin ya faɗa wa Tinubu a fili cewa ba zai goya masa baya ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com