'Abin da Ya Sa APC Ke Ƙoƙarin Jawo Kwankwaso Ya Haɗe da Tinubu kafin Zaɓen 2027'
- Yusuf Sharaɗa ya bayyana cewa ba komai ya sa APC ke son Rabiu Kwankwaso ya haɗe da Tinubu ba sai don samun goyon bayan talakawa
- Sharaɗa wanda mabiyin Sanata Kwankwaso ne ya ce kowa ya san tsohon gwamnan Kano yana da mabiya masu biyayya gare shi
- Ɗan Kwankwasiyyar ya ce APC ta rasa farin jininta a Kano da Arewa maso Yamma, shi yasa suke kokarin jawo Kwankwaso
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Yayin da ƴan siyasa ke ci gaba da shirin tunkarar babban zaɓen 2027, batun zawarcin da APC ke wa jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Kwankwaso ya ƙara jan hankali.
Yusuf Sharada, mabiyin Kwankwaso, ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP a 2023, ya ce APC na son jawo tsohon gwamnan domin Shugaba Bola Tinubu ya ci Kano a 2027.

Kara karanta wannan
ADC: An bayyana wanda zai jagoranci haɗakar su Atiku zuwa fadar shugaban ƙasa a 2027

Source: Twitter
Sharada, wanda shi ne shugaban ƙungiyar Project Save Nigeria, ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Sunrise Daily na Channels TV a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dalilin APC na ƙoƙarin jawo Kwankwaso
Ya ce jam’iyyar APC ta rasa farin jininta a jihar Kano, wacce ta fi kowace jiha yawan masu kada ƙuri’a a Najeriya, hakan ya sa ta fara kulla alaka da Kwankwaso da kuma tafiyarsa ta Kwankwasiyya.
Hadimin gwamnan Kano, Sharada ya ce:
“Sun dade suna ƙoƙarin jawo Sanata Kwankwaso zuwa APC, saboda sun san tarihin gwamnatinsa da yawan magoya bayansa. Tabbas, hakan na daga cikin dabarun siyasarsu.
“Sanata Kwankwaso ya guji APC ne saboda abubuwan da suke yi a matsayin gwamnati sun saɓawa da aƙidunsa, yanzu sun matsa suna so ya shiga APC.
"Siyasa lissafi ce, kuma sun san yana da ɗumbin mabiya, musamman daga Kano da yankin Arewa maso Yamma.”
Jigon NNPP ya zargi APC da ɓoye manufarta
Ƴan Kwankwasiyya na ganin saukar Abdullahi Ganduje daga shugabancin APC na iya zama wani ɓangare na dabarar APC domin jawo Kwankwaso daga NNPP.
A rahoton Daily Post, Sharada ya ƙara da cewa:
“Watakila APC ta gama tsara dabarunta, tana neman mabiya ne saboda manufofinta da suka cutar da talakawa; yanzu talakawan Najeriya ba sa tare da su.
“Don haka, suna neman mutum wanda talakawan ƙasar nan ke ƙaunarsa domin su samu adadin mutanen da suke bukata, musamman daga wannan yanki na ƙasa.”

Source: Twitter
'Yan Kwankwasiyya na da biyayya ga Kwankwaso'
Sharada ya ce mabiyan Kwankwaso watau ƴan Kwankwasiyya sun sadaukar da kansu ga tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar, kuma suna jiran umarninsa kan jam’iyyar da za su mara wa baya a 2027.
“Abin da ya kamata mutane su fahimta game da magoya bayan Sanata Kwankwaso shi ne suna daraja shi fiye da kowace jam’iyya ko dandali da yake ciki.

Kara karanta wannan
ADC: Haɗakar Atiku ta fara ƙarfi, tsohon shugaban Majalisar Dattawa ya fice daga PDP
“Don haka, mutane suna sauraron abin da zai faɗa; suna jiran umarnin da zai bayar domin su bi," in ji shi.
Malam Sa'id Abdu, wani ɗan Kwankwasiyya ya shaidawa Legit Hausa cewa wannan jita-jita da ake yaɗawa ta ƙara nuna ƙima da darajar maigidansu.
A cewarsa, ƴan APC da sauran ƴan Najeriya na ganin Kwankwaso zai ƙarawa Tinubu farin jini idan ya ɗauke shi a matsayin abokin takara a 2027.
Malam Sa'id ya ce:
"Wallahi ina jin daɗin abin da ake yaɗawa, a fili ya ƙara nuna cewa Kwankwaso bawan Allah ne mai mabiya, wanda ke kishin talakawa.
"Bari na tuna maka wasu maganganun mak gida, ya ce idan ka gyara gidanka sai na waje ya riƙa sha'awa, amma idan ka ɓata shi, na ciki ma gudunka za su yi, abin da ke faruwa kenan,"
An fara neman haɗewar Kwankwaso da Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa mai magana da yawun NNPP, Ladipo Johnson ya ce ƴan APC na son Kwankwaso ya zama abokin takarar Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan
Kwankwaso zai koma APC bayan Ganduje ya yi murabus? Shugaban NNPP na Kano ya yi bayani
Johnson ya ce NNPP a shirye take ta yi haɗaka, matuƙar za ta yi daidai da manufofinta na samar da daidaito da ci gaban al'ummar Najeriya.
Ya ƙara da cewa wasu daga cikin mambobin jam’iyyar APC sun tuntube shi kan yiwuwar haɗin gwiwa tsakanin Kwankwaso da shugaba Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
