Bidiyo: Yadda Aka Yi Waje da Hoton Ganduje a Sakatariyar APC, Mutane Sun Yi Martani

Bidiyo: Yadda Aka Yi Waje da Hoton Ganduje a Sakatariyar APC, Mutane Sun Yi Martani

  • An ga bidiyon lokacin da ake yin waje da hoton Abdullahi Ganduje daga ofishin APC, lamarin da ya jawo cece-kuce a intanet
  • An cire hoton ne a ranar da Ali Bukar Dalori ya kama aiki a matsayin muƙaddashin shugaban APC, bayan murabus ɗin Ganduje
  • Yayin da wasu ke takaici kan yada bidiyon cire hoton Ganduje, wasu kuma na ganin cewa hakan dai-dai ne don komai da lokacinsa

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Wani bidiyo da ya yadu a kafofin sada zumunta a ranar Litinin ya jawo ce-ce-ku-ce, inda wasu ke zargin cewa "an karbo kwangilar rusa Arewa."

A cikin bidiyon, an ga wani sanye da kwat, wanda ake kyautata zaton jami'in tsaro ne, ya na sauke hoton Abdullahi Ganduje daga ofishin shugaban APC na kasa.

Kara karanta wannan

Yaƴan jagororin ADC da ke cikin jam'iyyun APC da PDP a yau

An yi waje da hoton Ganduje daga ofishin jam'iyyar APC da ke Abuja
Tsohon shugaban jam'iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Bidiyon da Shehu Tijjani Sherif ya wallafa a shafinsa na Facebook, ya nuna yadda aka yi waje da hoton Ganduje daga ofishin, 'yan kwanaki bayan ya sanar da murabus dinsa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wani mataki da ba a yi zato ba Abdullahi Umar Ganduje, ya yi murabus daga muƙamin shugaban APC na ƙasa, nan take.

Murabus ɗin Ganduje da zarge-zargen rashawa

Ganduje, tsohon gwamnan Kano, ya ambato dalilai na rashin lafiya a matsayin dalilin murabus dinsa, yana mai cewa yana buƙatar mai da hankali kan kula da lafiyarsa.

An zaɓi Ganduje shi a matsayin shugaban APC a watan Agusta, 2023, yayin da jam'iyyar ke fama da rikicin cikin, inji rahoton Premium Times.

Duk da cewa takardar murabus ɗin Ganduje ta danganta matakinsa ga matsalolin lafiya, majiyoyi sun nuna cewa takaddamar siyasa a jam'iyyar ne ya tilasta shi yin murabus.

An kuma danganta murabus din Ganduje da karkatar da kuɗin jam'iyyar, inda aka ruwaito wasu 'yan jam'iyyar suna nuna rashin amincewarsu da irin kuɗaɗen da ofishinsa ke kashewa.

Kara karanta wannan

"Ba a kama shugaban ADC yana cusa daloli a aljihu ba," Dalung ya wanke ƴan APC tas

Musamman ma, ƴan takarar ƙananan hukumomin Abuja sun koka game da tsadar kuɗaɗen da ake buƙata don samun tikitin jam'iyyar.

An cire hoton Ganduje daga ofishin APC

Ana tsakiyar tattaunawa kan dalilan murabus din Ganduje, sai kuma aka ga bidiyon da ke nuna cewa an cire hoton tsohon shugaban APC daga ofishin jam'iyyar.

Legit Hausa ta fahimci cewa an yi waje da hoton Ganduje ne a ranar da sabon mukaddashin shugaban APC na kasa, Ali Bukar Dalori ya kama aiki.

Mun ruwaito cewa, Ali Bukar Dalori ya jagoranci taron kwamitin gudanarwar APC na kasa (NWC) a karon farko, bayan karbar ragamar shugabancin jam'iyyar.

Yayin da Ali Bukar Dalori ke zaune a kan kujerar shugaban APC, wani jami'i ya zagaya ta bayansa, ya sauke hoton Ganduje, tare da fitar da shi daga dakin.

Daga bisani, aka sake ganin jami'in ya dawo, ya matsar da hoton Ali Bukar Dalori zuwa inda aka cire hoton Ganduje, kamar dai karin maganar Bahaushe, 'mai wuri ya zo, mai tabarma ya nade.

Kara karanta wannan

'Na raina albashin': Hadimin Sanata ya yi murabus daga muƙaminsa bayan shekaru tare

Sabon mukaddashin shugaban APC na kasa, Ali Bukar Dalori ya kama aiki a ranar Litinin
Sabon mukaddashin shugaban APC na kasa, Ali Bukar Dalori ya jagoranci taron NWC a Abuja. Hoto: @OfficialAPCNg
Source: Twitter

Martanin mutane kan cire hoton Ganduje

Legit Hausa ta tattaro kadan daga cikin martanin 'yan Arewa kan cire hoton Ganduje daga ofishin APC:

Abdulkarim Muhd Sani:

"Sauke shi ko yana so ko ba ya so."

Mustapha Dan Hajiya Kr:

"Wai an ɗauko kwangilar rusa Arewa, to su su Ganduje su ne masu gina ta dama ke nan ko ya ya?"

Matukin Adaidaita Sahu:

"Yanzu sai dai a kai masa hoton gidansa kenan."

Evraheem Mu'azzam Bichi II

"Baba ina za ka ne, mulki an yi an gama."

Abdul'aziz Siniya Kura:

"Allah mun tuba, ya Allah kai mana kyakkyawan karshe."

A zantawar Legit Hausa da Sanusi Kobi, shugaban kungiyar masu goyon bayan PDP ta PDPMSF, ya ce:

"Dama haka siyasa ta gada, yau kai ne gobe ba kai ne ba. Shi ma Ganduje a lokacin da ya shiga ofis, ai hoton wani ne a ciki, aka cire aka sanya nasa, yanzu shi ma an cire nasa an sanya na wani.

Kara karanta wannan

Maryam Shetty ta tofa albarkacin bakinta kan murabus ɗin Ganduje daga shugabancin APC

"Mu a jam'iyyar PDP, mun riga da mun san hakan, shi ya zaka same mu masu biyayya ga jam'iyya ba wai shi karan-kansa shugaba ba, domin ana canja shugaba, amma ba a canja jam'iyya.
"Shawarata ga Ganduje shi ne, ya yi tsam ya yi nazari, ya fahimci ina siyasarsa ta dosa. Idan gwamnatin APC ba za ta sake ba shi wata dama ba, to ya dawo PDP, mu za mu iya ba shi dama."

Shi kuma Abba Hassan Gezawa, daga jihar Kano, ya ce murabus din da Ganduje ya yi baga-tatan akwai lauje cikin nadi, domin sun samu jita-jitar dalilin ajiye aikinsa.

"Wai mun ji ana cewa shugaban kasa ne ya tilasta shi murabus saboda zarge-zargen rashawa a jam'iyyar. To mu dai abin da muke cewa shi ne Ganduje dai ya yi wa APC rana ba kadan ba.
"Nasarori da APC ta samu a jihohin da PDP ke mulki shaida ne kan kwarewarsa a shugabanci. Duk wani dan siyasa yana da kashi a gindinsa, indai a kan rashawa ne."

- Abba Hassan Gezawa.

Kalli bidiyon a nan kasa:

An ji wulakancin da aka shirya wa Ganduje

Kara karanta wannan

Murabus ɗin Ganduje: An bayyana matakin farko da sabon shugaban APC ya dauka

A wani labarin, mun ruwaito cewa, wani jigon APC a Kano a ya bayyana cewa murabus ɗin Abdullahi Ganduje dabara ce don kauce wa kunyata shi da tilasta masa sauka.

Ya ce akwai wani ɓoyayyen shiri da aka kitsa don kawar da Ganduje daga kan shugabancin idan har ya ƙi bin umarnin fadar shugaban ƙasa.

Jigon ya ƙara da cewa Ganduje ya taka rawar gani wajen ƙarfafa jam'iyyar APC da jawo ‘yan siyasa da dama, don haka ya cancanci girmamawa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com