'Ku Tsame Sunan Kwankwaso': NNPP Ta Gargaɗi Alaƙanta Jagora da Tinubu a 2027
- Shugabannin bangarori biyu na NNPP a Kano sun yi magana kan rade-radin cewa ana son ba Rabiu Kwankwaso muƙamin mataimakin shugaban kasa
- Shugabannin sun gargadi jama’a ka da su jawo sunan Kwankwaso cikin batun mataimakin Bola Tinubu a zaben 2027
- Sun bayyana cewa Kwankwaso bai da niyyar shiga APC, kuma kiraye-kirayen da ake yi masa bisa cancanta ne ba wai shiri ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugabannin tsagin jam'iyyar NNPP biyu a jihar Kano sun yi martani kan rade-radin takarar Rabiu Kwankwaso da Bola Tinubu a 2027.
Shugabannin biyu, Hashimu Dungurawa da Sanata El-Jibril Doguwa, sun gargadi mutane kan rade-radin.

Source: Twitter
Rahoton Punch ta ce sun yi gargadi kada a jawo Rabiu Kwankwaso cikin muhawarar batun mataimakin Bola Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan
'An taso Kashim Shettima a gaba': Ƴan Borno sun jefo zargi bayan murabus ɗin Ganduje
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Haka kuma, sun karyata rahotannin da ke cewa Kwankwaso na shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC mai mulki.
Jita-jitar cewa Tinubu zai tafi da Kwankwaso
A cikin ‘yan kwanakin nan, rade-radin siyasa sun kara karfi inda wasu ke danganta Kwankwaso da kudirin sake tsayawa takara na Tinubu a 2027.
Rade-radin sun kara karfi ne bayan saukar shugaban APC na kasa, Abdullahi Ganduje, wanda wasu ke ganin ana so a cusa Kwankwaso ne a tawagar Tinubu.
Tinubu/Kwankwaso: Shugabannin NNPP sun magantu
Amma a hirarsu da yan jaridu ranar Asabar, wasu abokanan Kwankwaso sun yi gargadi kan muhawarar da ake yi kan zaben mataimakin shugaban kasa.
Sun ce duk da cewa Kwankwaso ya cancanci kujerar mataimaki, tayar da batun yanzu na iya haddasa rudani a wasu sassan kasar.
Doguwa ya ce ko da yake Kwankwaso na da kwarewa, bai kamata a matsa wa Tinubu ya yanke hukunci cikin gaggawa kan wanda zai zama mataimakinsa ba.
Doguwa ya ce:
“Kwankwaso na da cancantar rike kowane mukamin siyasa a kasar nan, babu shakka. Amma kar mu matsa wa Shugaban Kasa ya dauki mataki da wuri.
“Idan lokaci ya yi, kuma ya yi la’akari da tsarin siyasa a kasar nan, abubuwa za su daidaita. Mu yi hakuri.
“Har yanzu Kwankwaso ba ya cikin APC, Tinubu kuwa yana cikin APC. Akwai masu ganin su ma sun cancanci kujerar mataimaki.

Source: Facebook
NNPP ta yi gargadi kan hada Kwankwaso, Tinubu
A nasa bangaren, Dungurawa ya siffanta rade-radin da ke danganta Kwankwaso da APC da cewa “bata-garin siyasa ne kawai ke yada hakan.
Dungurawa ya jaddada cewa Kwankwaso na da karbuwa da suna a siyasance, abin da ke jawo irin rade-radin da ake danganta shi da Tinubu.
“Babu wani irin yunkuri da ake yi. Kwankwaso ba ya shirin shiga jam’iyyar APC."
“Yawan rade-radin da ake yi yana faruwa ne saboda mutunci da farin jinin da jagorarmu ya gina tsawon lokaci."
- Cewar Dungurawa
An alakanta murabus din Ganduje da zuwan Kwankwaso
Kun ji cewa wani jigo a jam’iyyar APC ya yi hasashen cewa murabus din Abdullahi Ganduje na iya bude kofar shigar Rabiu Kwankwaso jam’iyyar.
Jigon ya ce dama Abbdullahi Ganduje na rike ne da kujera ce da aka ware wa yankin Arewa ta Tsakiya, kuma hakan ya yi kokarin kawo rikici.
Ya bayyana cewa akwai yiwuwar Kwankwaso ya karɓi shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa idan har ya sauya sheka zuwa cikinta.
Asali: Legit.ng

