'Za Ka Dawo kan Mulkin Rivers': Tinubu Ya Gindaya Sharuɗa 3 Masu Tsauri ga Fubara
- Shugaba Bola Tinubu ya amince da dawo da Gwamna Siminalayi Fubara kan mulki bisa wasu sharuda da ya gindaya
- Daga cikin sharudan akwai cewa ba zai nemi tazarce ba a zaben 2027 mai zuwa a jihar Rivers kuma zai biya yan majalisa
- Har ila yau, Nyesom Wike zai nada shugabannin kananan hukumomi 23, sannan Fubara zai biya hakkokin ‘yan majalisa 27
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya amince da dawo da Siminalayi Fubara a matsayin gwamnan Jihar Rivers bayan sanya dokar ta-ɓaci.
Sai dai bayan zaman sulhu da aka yi a birnin Abuja, ana rade-radin cewa Bola Tinubu ya gindaya masa sharuda kan dawowa mulki.

Source: Facebook
An yi zaman sulhu kan rikicin Rivers
Rahoton TheCable ya ce Tinubu ya amince a dawo da Fubara amma da sharadin ba zai tsaya takara a 2027 ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An cimma sulhun ne a wata ganawa ta sirri da aka yi a fadar shugaban kasa, inda Tinubu ya karɓi bakuncin Nyesom Wike, Fubara, da wasu 'yan majalisa.
Majiyoyi daga fadar shugaban kasa sun bayyana cewa wannan yarjejeniya na cikin kokarin dawo da tsarin dimokuradiyya a jihar Rivers.
A cewar wani jami’i, Fubara zai kammala wa’adin sa na shekara hudu, amma dole ne ya janye daga kokarin neman wa’adi na biyu a 2027.
Yadda Wike zai cigaba da iko a Rivers
Wata majiyar ta ce, cikin sharuddan sulhun, an yarda Wike zai dama wajen naɗa dukkan shugabannin kananan hukumomi guda 23 na jihar.
Majiyar ta kara da cewa hakan zai bawa Wike babban tasiri a siyasar jihar, ta hanyar dawo masa da iko daga tushe.
An kuma gano cewa Fubara ya amince zai biya dukkan alawus da hakkokin 'yan majalisar 27 da ke goyon bayan Wike da aka dakatar.

Kara karanta wannan
Rikici ya kare: Tinubu ya gana da Fubara, Wike da 'yan majalisar Rivers a Aso Villa

Source: Twitter
Matsayar yan majalisa bayan zaman sulhu
A maimakon haka, ‘yan majalisar ba za su yi yunkurin tsige shi daga mulki ba, kamar yadda suka yi barazanar a baya, cewar Vanguard.
Wadannan ‘yan majalisar ƙarƙashin jagorancin Amaewhule sun koma jam’iyyar APC yayin rikicin, amma sun ci gaba da riƙe kujerunsu.
Majiyoyi sun bayyana cewa ganawar da aka yi Alhamis da dare ta zama ci gaba ga Tinubu wajen sasanta Wike da gwamnan.
"Komai ya fito fili, babu wa’adi na biyu, babu ikon kananan hukumomi, amma zaman lafiya zai dawo."
“Shugaban kasa ya bayyana cewa Jihar Rivers ba za ta jure dogon rikici ba, wannan sulhu yana nufin kwanciyar hankali ya dawo, amma Fubara ya sadaukar da iko mai yawa domin ya tsira da siyasarsa.
“Wike ne ya fi cin moriyar wannan sulhu, ta hanyar sarrafa shugabannin kananan hukumomi, zai ci gaba da rike ikon siyasa a 2027.”
- Cewar wata majiya
An yi zargin dalilin kin dawo da Fubara
Kun ji cewa an yi ta hasashen cewa Bola Tinubu zai dawo da Fubara a ranar 29 ga Mayu ko ranar 12 ga Yunin 2025.
An yi tsammanin haka ne saboda matsayin ranar demokradiyya bayan shan matsin lamba daga yan Najeriya.
Sai dai ana zargin murna da magoya bayan Fubara ke yi ya fusata bangaren Nyesom Wike da ke da tasiri a lamarin.
Asali: Legit.ng

