Makusancin Ganduje, Bakwana Ya Yi Watsi da APC, Ya Dawo Wajen Kwankwaso

Makusancin Ganduje, Bakwana Ya Yi Watsi da APC, Ya Dawo Wajen Kwankwaso

  • Mustapha Bakwana Makusancin Shugaban APC, Abdullahi Ganduje, ya sauya sheƙa daga APC zuwa tafiyar Kwankwasiyya a Kano
  • Wannan mataki na nufin cewa ya yi watsi da mukaminsa a ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin
  • Bakwana ya zargi APC da nuna halin ko-in-kula gare su da mutanensu duk da irin wahalar da su ka yi wa Abdullahi Umar Ganduje

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Mustapha Hamza Buhari Bakwana, ɗaya daga cikin na hannun daman shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya sanar da sauya sheka zuwa NNPP. Bakwana ya yi watsi da mukaminsa na hadimin majalisar dattawa da ke kula da harkokin majalisa na ofishin Sanata Barau I Jibrin.

Kara karanta wannan

2027: Barau ya yi magana bayan an nemi Tinubu ya ajiye Shettima ya dauke shi

Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Ganduje
Makusancin Ganduje ya koma wajen Kwankwaso Hoto: Rabiu Musa Kwankwaso/Salihu Tanko Yakasai
Source: Facebook

A wata hira da ya yi da manema labarai wadda aka wallafa a shafin Facebook na Express Radio, Bakwana ya zargi Ganduje da nuna halin ko-in-kula da su bayan sun yi masa hidima.

Bakwana ya yi bankwana da Ganduje da APC

Solacebase ta ruwaito cewa Mustapha Bakwana ya bayyana cewa ba su taɓa samun sabani da tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ba.

A cewarsa:

"Saboda rigimar Ganduje, mu ka rabu da Kwankwaso, Ni ban taba sabani da Kwankwaso ba, lokacin a kan rigimarsa, mu ka bar shi."
"To yau, mun zo mun bi wannan din, mun yi biyayyar, mun yi hakurin. Amma a tsarin da ake kai, sun nuna ba sa kaunarmu, ba sa kaunar mutanenmu."

Ya kara nanata cewa saboda haka sun yi bankwana da tafiyar tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje zuwa inda su ke zaton za a tafi da su.

Kara karanta wannan

An kashe yaran Sheikh Ibrahim Khalil a Benue, gwamnan Kano ya yi magana mai zafi

Bankwana ya fadi halayyar kirkin Kwankwaso

Bakwana ya ci gaba da cewa mutanensu sun fi kowa dabarar yadda ake gudanar da zaɓe 'ko da tsiya, ko da arziki' domin samun nasara.

Ya ce babu wani laifi da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya yi musu, saboda haka suka ga dacewar watsi da APC da Abdullahi Umar Ganduje.

A cewarsa:

""Kwankwaso ba ya karya, Kwankwaso ba ya cin amana, Kwankwaso ba ya yaudara."
Mustapha Hamza Buhari Bakwana da Barau Jibrin
Bankwana ya kuma ajiye mukaminsa a ofishin Barau Jibrin Hoto: Mustapha Hamza Buhari Bakwana
Source: Facebook

Ya kara da cewa :

"An dama mana kunu da kwalba, an zuba mana tsakuwa, an zuba mana yashi, an zuba mana kasa, an ba mu mun sha."

Ya ƙara da cewa hakurin da su ka yi da APC ba ya nufin akwai wanda suke tsoro, illa biyayya domin a gudu tare a tsira tare.

Sai dai Bankwana ya ce sun lura biyayyar ba za ta haifa masu da mai ido ba, saboda haka sun ajiye APC domin ci gaba da aikin inganta NNPP a Kano.

Kara karanta wannan

'Tinubu ba zai kai labari ba,' El-Rufa'i ya fadi abubuwan da za su hana APC nasara a 2027

Ana hasashen Tinubu zai jawo Kwankwaso APC

A baya, kun ji rahotanni na cewa shugaban kasa Bola Tinubu na duba yiwuwar sauya mataimakinsa, Kashim Shettima, da Rabi’u Musa Kwankwaso a zaben 2027.

Majiyoyi sun bayyana cewa wannan na daga cikin abubuwan da suka jawo shugaban jam’iyyar APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, bai ambaci sunan Shettima a taronsu ba.

Majiyar ta bayyana cewa batun sanya Kwankwaso a matsayin sabon mataimakin shugaban kasa ya samu karɓuwa a tsakanin wasu manyan ‘yan jam’iyyar APC don tazarcen Tinubu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng