'Ba Zan Zabi APC ba': Sheikh Jingir Ya Kafa Sharadin Tallata Tinubu a Zaben 2027
- Sheikh Yahaya Jingir ya ce ba zai goyi bayan Bola Tinubu a 2027 ba idan ya ki sake daukar Kashim Shettima a matsayin mataimakinsa
- Malamin ya bayyana hakan a Jos, yayin da ya nuna damuwa kan jita-jitar da ake yadawa na rashin jituwa tsakanin Tinubu da Shettima
- Ya roƙi Tinubu ya toshe kunnensa daga masu cewa ya ajiye Shettima a 2027, inda ya jaddada cewa ba zai zabe shi ba idan ya yi hakan
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Filato - Shugaban majalisar malamai ta Jama’atu Izalatil Bid’a Wa’ikamatis Sunnah (JIBWIS), Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya yi magana kan zaben 2027.
Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya bayyana cewa ba zai goyi bayan Shugaba Bola Tinubu da jam'iyyar APC ba a babban zaɓen 2027 mai zuwa.

Source: Facebook
Sheikh Jingir ya yi magana kan zaben 2027

Kara karanta wannan
'Tinubu na mayar da Najeriya kamar Lagos': Sarkin Lafiya ya faɗi abin da suka gani a Ikko
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Sheikh Jingir ya ce hakan zai faru ne idan har Tinubu ya ki daukar Sanata Kashim Shettima, a matsayin mataimakin shugaban kasa.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sheikh Sani Yahaya Jingir ya bayyana wannan matsayar tasa ne a wani taron addini da aka gudanar a masallacin Yantaya da ke Jos, babban birnin jihar Filato.
Rahotanni sun bayyana cewa Sheikh Jingir ya goyi bayan zaɓen Shugaba Tinubu a shekarar 2023 kuma ya karfafa mabiyansa akan zaben Muslim-Muslim a lokacin.
Ana ganin cewa jita-jitar da ake yayata wa a cikin jam'iyyar APC kan makomar mataimakin shugaban kasar ce ta sa malamin addinin ya fito ya yi wannan gargadin.
Abin da zai hana Jingir zabar Tinubu a 2027
Da yake martani kan jita-jitar, Sheikh Jingir ya ce:
"Samun labarin cewa wasu marasa kishin al'umma da ke a ciki da wajen jam'iyyar APC suna ta kokarin haddasa husuma tsakanin Tinubu da Shettima.
"Suna yin hakan ne domin cimma wata manufarsu ta siyasa. Wannan babbar matsala ce da ke tunkarar shugaban kasa Tinubu.
"Ni da duk wadanda ke tare da shi, mun goyi bayan Tinubu da Shettima, kuma muna kara jaddada goyon bayanmu ga sake tsayawa takararku tare.
"Amma idan aka yi wani yunkuri na ajiye Shettima, to ba zan taba goyon bayan wannan tafiyar ba, saboda a tare ne muka san cewa za su yi takara."

Source: Twitter
Shawarar Sheikh Jingir ga Shugaba Tinubu
Fitaccen malamin addinin ya ce ya goyi bayan Shettima da Tinubu ba tare da ya karbi ko sisin kwabo daga wajensu ba, duk da cewa ya fi kusanci da Atiku Abubakar.
"Duk da cewa na fi kusanci da Atiku Abubakar, haka na rufe ido, na yanke wa kaina shawarar zabar Tinubu da Shettima.
"Akwai jita-jitar da ake yadawa, cewa akwai rashin jituwa a tsakaninsu, amma ni ban yarda da jita-jitar ba. A nawa ra'ayin, wannan wani makiricin makiyansu ne."
- Sheikh Sani Yahaya Jingir.
Jingir ya bukaci Tinubu da ya toshe kunnuwansa daga masu cewa ya ajiye Shettima a 2027, yana mai cewa masu irin wannna kiran makiyansa ne.
Sheikh Jingir ya sa Tinubu ya kashe N33bn
A wani labarin, mun ruwaito cewa, kokarin da Sheikh Sani Yahaya Jingir ya yi na fara gyaran hanyar Kaduna zuwa Jos da kansa, ya jawo hankalin fadar shugaban kasa.
Malamin ya bayyana cewa maimakon sukar gwamnati ko gudanar da zanga-zanga, ya dauki matakin gyaran titin da kansa, wanda hakan ya sanya gwamnatin tarayya ta shiga ciki.
A sakamakon wannan yunƙurin, gwamnatin tarayya ta ware sama da Naira biliyan 287 domin gyaran hanyoyi 14 a faɗin Najeriya, ciki har da hanyar Kaduna zuwa Jos.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

