Tinubu Ya Kara Karfi gabanin 2027, Sanatan Jam'iyyar LP Ya Sauya Sheka zuwa APC

Tinubu Ya Kara Karfi gabanin 2027, Sanatan Jam'iyyar LP Ya Sauya Sheka zuwa APC

  • Sanata Neda Imasuen ya sauya sheka daga LP zuwa APC saboda rikicin cikin gida da kuma buƙatar kyautatawa al'ummar mazabarsa
  • Ya bayyana cewa matakin ya biyo bayan shawarwarin da ya yi da al'ummarsa da manyan 'yan siyasa, duk don samar da wakilci na-gari
  • Imasuen ya yi alƙawarin ci gaba da jajircewa wajen yi wa jama'arsa hidima da kuma nemo masu romon dimokuraɗiyya karkashin APC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Sanata mai wakiltar Edo ta Kudu, Sanata Neda Imasuen, ya sanar da murabus dinsa daga LP tare da komawa jam'iyyar APC.

Ya bayyana cewa rikicin cikin gida na jam'iyyar LP da kuma buƙatar samun gindin zama a siyasance ga al'ummar mazabarsa ne suka sa ya ɗauki wannan matakin.

Sanata Neda Imasuen ya sanar da ficewarsa daga jam'iyyar LP zuwa APC a zauren majalisar dattawa
Sanata Neda Imasuen, dan majalisar dattawa da ke wakiltar Kudancin Edo. Hoto: @SenNedaImasuen/X
Source: Twitter

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ne ya karanta wasikar sauya shekar sanatan a zaman majalisar dattawa na ranar Laraba, inji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

2027: Barau ya yi magana bayan an nemi Tinubu ya ajiye Shettima ya dauke shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dalilan sauya shekar Sanata Imasuen

A cikin wasikar, Sanata Imasuen ya ce sauya shekarsa ya biyo bayan "shawarwari masu zurfi" da ya yi da al'ummar mazabarsa da manyan 'yan siyasa a Edo ta Kudu.

"Na rubuta wannan wasika don sanar da majalisar dattawa ta ofishin shugaban majalisar dattawa game da murabus dina daga jam'iyyar LP da kuma shawarata ta komawa APC a hukumance."

- Inji wasikar da Akpabio ya karanta.

Ya bayyana cewa ya ɗauki matakin ne don samar wa mazabarsa damar samun gindin zama da kuma samun dama mai girma a ƙarƙashin jam'iyya mai mulki.

Sanatan ya kara da cewa:

"Wannan matakin ya biyo bayan shawarwari masu zurfi da na yi da al'ummar mazabata, da manyan 'yan siyasa na, da kuma magoya bayana a duk faɗin mazabar Edo ta Kudu.
"Kuma dukkaninsu sun bayyana muradinsu na ganin na shiga jam'iyyar da za ta ba su muhimmanci a matakin ƙasa da kuma samun damarmaki a siyasar ƙasar."

Kara karanta wannan

'Ba abin kunya ba ne': Farfesa da ke sayar da kayan miya ya fadi sirrin rayuwarsa

Matasaloli a LP sun kori Sanata Imasuen

Sanata Imasuen ya kuma ambaci matsalolin cikin gida da kuma kalubalen shugabanci a cikin LP a matsayin babban dalilin da ya sa ya yanke shawarar barin jam'iyyar.

Ya ce waɗannan matsalolin sun hana shi damar wakiltar jama'a da kuma cika ainihin manufar wakilci ga al'ummar Edo ta Kudu yadda ya kamata.

Ya bayyana cewa komawarsa APC za ta kara masa karsashin wakilci da kuma goyon bayan kudurin Renewed Hope Agenda na gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Sanata Neda Imasuen ya ce zai yi aiki tukuru don nemawa al'ummar mazabar Edo ta Kudu romon dimokuradiyya
Sanata Neda Imasuen, dan majalisar dattawa da ke wakiltar Kudancin Edo. Hoto: @SenNedaImasuen/X
Source: Twitter

Sanata Imasuen ya yi wa al'ummarsa alkawari

Vanguard ta rahoto cewa, Sanata Imasuen ya tabbatar wa al'ummar mazabarsa cewa zai ci gaba da jajircewa wajen yi masu hidima da kuma kiyaye ƙa'idojin dimokuraɗiyya.

"Zan ci gaba da jajircewa wajen yi wa al'umata hidima da kuma nema masu romon dimokuraɗiyya yayin da nake cikin majalisar dattawa," inji sanatan.

Sauya shekar dan majalisar dattawan ya ƙara yawan 'yan majalisar tarayya da ke ci gaba da barin jam'iyyar LP yayin da ake tunkarar babban zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

2027: Gwamnoni 4 da ƴan majalisa da ake zargin suna harin kujerar Kashim Shettima

Gwamnati ta hango sauya shekar Sanata Imasuen

Tun da fari, mun ruwaito cewa, mai ba gwamnan Edo shawara kan siyasa, Eugene Utubor, ya ce Sanata Neda Imasuen na LP zai shiga APC.

Utubor ya bayyana cewa sun gana da sanatan, kuma alamun da ya gani, sun nuna masa cewa Sanata Imasuen ya shirya tsaf domin canza sheƙa daga LP zuwa APC.

Neda Imasuen ya sha ƙin yin magana kan ci gaba da zamansa a LP wacce ke fama da rikicin cikin gida a matakin jiha da na ƙasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com