2027: Barau Ya Yi Magana bayan an Nemi Tinubu Ya Ajiye Shettima Ya Dauke Shi

2027: Barau Ya Yi Magana bayan an Nemi Tinubu Ya Ajiye Shettima Ya Dauke Shi

  • Sanata Barau Jibrin ya ce bai dace a rika kiransa ya zama mataimakin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 ba
  • Mataimakin shugaban majalisar ya bukaci matasa su mayar da hankali wajen mara wa Shugaba Tinubu baya a aikin ceto Najeriya
  • Ya bayyana goyon bayansa ga Tinubu da manufofin da ya ce ya kawo domin habaka tattalin Najeriya da inganta rayuwar 'yan kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya magantu game da kiran da ake yi masa da ya zama ɗan takarar mataimakin shugaban kasa a 2027.

Wata kungiya ce ta fito da bayani inda ta nemi a ajiye Kashim Shettima a 2027 domin tafiya da Sanata Barau, amma ya ce babu bukatar hakan a yanzu.

Kara karanta wannan

An kaure a Arewa kan kujerar Kashim Shettima, an roƙi Tinubu ya ɗauki Dogara

Barau ya nesanta kan shi da maganar neman kujerar Shettima a 2027
Barau ya nesanta kan shi da maganar neman kujerar Shettima a 2027. Hoto: Barau I Jibrin|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Daily Trust ta wallafa cewa Sanatan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da mai ba shi shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai, Ismail Mudashir, ya fitar.

Ismail Mudashir ya bayyana cewa Sanata Barau Jibrin ya bukaci masu kiran su daina wannan yunkuri.

A cewar rahoton Aminiya, lamarin na cigaba da haifar da muhawara, musamman ganin yadda ake tunanin ko Tinubu zai sake tsayawa da Kashim Shettima ko kuma ya sauya shi.

Sanata Barau ya dakatar da kiran NNPYA

Sanata Barau ya ce hankalinsa ya kai ga wasu sakonni da kungiyoyi irin su NNPYA ke wallafawa a kafafen sada zumunta da jaridu, suna kiran a ɗaukesa takarar mataimakin shugaba a 2027.

Ya ce wannan batu bai dace da lokacin da ƙasa ke ciki ba, inda ya bukaci dukkanin masu irin wannan tunani su janye kuma su mayar da hankalinsu kan goyon bayan Shugaba Tinubu.

Kara karanta wannan

Shettima: Yadda Tinubu ya yi aiki da mataimaka 3 da ya ke gwamnan Legas

A cewarsa:

"Ina rokon NNPYA da sauran kungiyoyi su daina wannan kira daga yanzu.
"Maimakon haka, su mayar da kokarinsu wajen goyon bayan shugaban ƙasa domin magance matsalolin da ƙasa ke fuskanta."

Barau ya jaddada goyon bayansa ga Tinubu

Sanata Barau, wanda shi ne Mataimakin Kakakin Majalisar ECOWAS, ya bukaci masu goyon bayansa da su daina yayata kiran tare da hada kai wajen ceto ƙasar karkashin Tinubu.

"Ina rokon duk masu kauna ta da su dakatar da wannan batu, su rungumi tafiyar farfado da martabar ƙasarmu a ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu,"

Inji shi.

Ya kara da cewa lokaci ne na goyon bayan shugabanci, ba na neman mukami ba:

"Wannan ba lokaci ba ne da ya dace da irin wannan lamari. Abu mafi muhimmanci garemu yanzu shi ne ganin nasarar shugaban ƙasa."
Barau ya ce yanzu lokacin aiki ne ba siyasa ba
Barau ya ce yanzu lokacin aiki ne ba siyasa ba. Hoto: Barau I Jibrin
Source: Twitter

Sanata Barau ya jaddada cewa Tinubu yana da kyakkyawan niyya da shiri na farfado da Najeriya, tare da bukatar goyon baya daga kowane ɗan ƙasa.

Kara karanta wannan

Ajiye Shettima: Fadar shugaban kasa ta ce Tinubu zai sanar da mataimaki a 2026

Gwamna zai ba Tinubu miliyoyin kuri'u a 2027

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan Edo ya yi wa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu alkawarin kuri'a miliyan 2.5.

Gwamnan jihar ya bayyana haka ne yayin karbar wasu 'yan jam'iyyar PDP da suka sauya sheka zuwa APC.

Ya bayyana cewa shugaban kasa Bola Tinubu ya nuna kauna ga mutanen jihar Edo kuma dole ne su saka masa da alheri a 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng