Haɗakar Adawa: El Rufai Ya Jero Ƙusoshin Ƴan Siyasar da Ke Yaƙar Tinubu da APC

Haɗakar Adawa: El Rufai Ya Jero Ƙusoshin Ƴan Siyasar da Ke Yaƙar Tinubu da APC

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce hadin gwiwar da ake tattaunawa yanzu ba ta da alaka da kowace jam’iyyar siyasa
  • El-Rufai ya bayyana cewa shugabanni ne na kungiyoyi daban-daban ke jagorantar tattaunawar da ake yi domin yin taron dangi
  • Ya ce yana cikin tattaunawar a karan kansa ba wakilin SDP ba, kuma hadin kai ne tsakanin shugabannin adawa ba tsakanin jam’iyyu ba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kaduna - Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya sake tabo batun hadakar jam'iyyun adawa a Najeriya domin kwace mulkin Bola Tinubu.

Malam El-Rufai ya yi magana kan yadda suka hada tafiyar inda ya ce tattaunawar ba ta da alaka da jam'iyyun siyasa kamar yadda mutane da dama ke zato.

El-Rufai ya fayyace shirinsu na kwace mulkin Tinubu
Nasir El-Rufai ya fadi wadanda suka shirya tafiyar haɗaka saboda Tinubu. Hoto: Nasir El-Rufai, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Twitter

El-Rufai ya jero yan siyasa da suke hadaka

Kara karanta wannan

"Abin da ya sa muke shirin ƙirƙiro jam'iyyar ADA kafin 2027," El Rufai ya yi bayani

El-Rufai ya bayyana haka ne a cikin wani bidiyo yayin hira da Arise TV da aka wallafa a shafin YouTube a jiya Litinin 23 ga watan Yunin 2025 da muke ciki.

A cikin bidiyon, El-Rufai ya fayyace yadda suka hada mutane a matsayin shugabanni domin tattauna shirin kwace mulki a zaben 2027.

Tsohon gwamnan ya ce hadakar ba ta da alaka da jam'iyyu illa sun hada wasu jagorori ne da suke da mambobi da yawa a karkashinsu.

Ya ce:

"Matsalar ita ce mutane sun yi tsammanin muna son yin irin abin da muka yi a 2013 ne da APC, ba haka ba ne, jam'iyyu ba su cikin wannan tattaunawar.
"Daidaiku ne ke jagorancin kungiyoyin da ke hadaka, Atiku yana da mabiyansa da suka fito daga PDP har ma da APC.
"Sannan akwai kungiyoyin karkashin jagorancin Rauf Aregbesola da Emeke Nwajiuba da Abubakar Malami.
El-Rufai ya jero wadanda suke shirya hadaka
Nasir El-Rufai ya fayyace yadda tsarin haɗakarsu take kan zaben 2027. Hoto: Nasir El-Rufai.
Source: Twitter

A hirar da aka yi da shi, 'dan siyasar ya nuna cewa irinsu Rotimi Amaechi su na cikin wannan yunkuri na ganin bayan APC a zabe mai zuwa.

Hakan yana nufin akwai akalla ministocin Muhammadu Buhari hudu a kokarin hadakar.

Kara karanta wannan

"Ba su da maraba," Hakeem Baba ya kwatanta shugabannin hadakar su Atiku da APC

El-Rufai ya fadi matsayin SDP a tafiyar haɗaka

Nasir El-Rufai ya ce jagororin da suke tattaunawa da su suna da mambobi a karkashinsu da dama daga jam'iyyu daban-daban.

Shi kansa ya ce yana cikin tattaunawar ne a karan kansa ba wai yana wakiltar jamiyyarsa ta SDP ba ne duba da yadda sauran jagororin suke wakiltar mutanensu.

"Wadannan kungiyoyi suna da mambobi daga dukan jam'iyyu, Peter Obi yana da mutanensa daga LP da PDP da sauransu.
"Saboda haka shugabannin wadannan kungiyoyi ne ake tattaunawa da su ba jawo jam'iyyu saboda haɗaka muke yi ba.
"Ina cikin wadanda ake tattaunawa da su amma ba wai ina wakiltar SDP ba ne, ina ciki ne a karan kaina."

- Cewar Nasir El-Rufai

El-Rufai ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu

Kun ji cewa tsohon gwamna, Nasir El-Rufai ya sake sukar gwamnatin caccakar Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yayin da suke shirin hadaka.

Mallam El-Rufai ya bayyana cewa saɓanin abin da ake tunani bai taɓa kasancewa na kusa da Tinubu ba a siyasance tun a farko.

Tsohon gwamnan ya nuna cewa Allah ne ya taimake shi daga shan kunya shiyasa bai tsinci kansa a gwamnatin Tinubu ba bayan goyon bayanta ta hau karagar mulki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.