'Ba Tinubu ba ne': An Fallasa 'Yan Siyasa 2 da Ke Haddasa Rikici a Jam'iyyar LP
- Tsagin LP na Julius Abure ya wanke gwamnatin tarayya daga rikicin jam'iyyar, inda ya zargi Peter Obi da Alex Otti da haifar da rikicin
- Jam'iyyar LP ta dage cewa rikicin shugabanci ya fara ne bayan da Obi da Otti suka kafa kwamitin riko, duk da wa'adin Abure bai kare ba
- Umar Farouk Ibrahim ya kalubalanci Obi ya kawo hujjar zargin gwamnati, yana mai cewa ya gaza bayar da jagoranci ga jam'iyyar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsagin jam’iyyar LP da Julius Abure ke jagoranta ya wanke gwamnatin Shugaba Bola Tinubu daga zargin haddasa rikici a cikin jam'iyyar.
Julius Abure ya zargi tsohon dan takarar LP a zaben 2023, Peter Obi, tare da gwamnan Abia, Alex Otti, da haddasa dukkanin rikicin da ke addabar jam’iyyar.

Source: Twitter
An zargi Obi, Otti da haddasa rikicin LP
Jam'iyyar LP ta dage cewa ba gwamnatin tarayya ko APC mai mulki ne suka jefa ta a cikin rikicin shugabanci da take fama da shi ba, inji rahoton The Nation.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
LP ta ce ta kasance cikin zaman lafiya har sai da Obi da Otti suka kafa wani kwamitin riko, alhali har yanzu wa’adin shugabancin Abure bai kare ba.
A wata hira da yayi a talabijin na kasa a ranar Litinin, Obi ya dora alhakin rikicin LP a kan gwamnatin tarayya, yana zarginta da amfani da ‘yan leƙen asiri domin tarwatsa jam’iyyar.
“Rikicin da ke addabar jam'iyyar LP a halin yanzu na da nasaba da shisshigi da kuma son cusa kai na gwamnatin da ke kan mulki."
- Peter Obi.
LP ta ce babu ruwan gwamnati a rikicinta
Sai dai a wata sanarwa da sakataren LP na kasa na bangaren Abure, Umar Farouk Ibrahim, ya fitar a jiya, ya kalubalanci Obi da ya fito da hujjoji da ke nuna cewar gwamnatin APC ce ke da hannu a cikin rikicin jam’iyyar.
Jaridar Tribune Online ta rahoto sanarwar ta kara da cewa:
“Rikicin da ke cikin jam'iyyar LP ba shi da wata alaka da gwamnatin tarayya. A gaskiya, rikicin na da alaka da Peter Obi da kuma Gwamna Alex Otti na jihar Abia, wanda ke fuskantar dakatarwa daga LP bisa zargin aikata laifin cin amanar jam’iyya.
“Muna kalubalantar Obi da ya fito da kowacce irin shaida, ta gani ko ta saurare, da ke nuna cewar Abure na da wata alaka da gwamnatin APC ko yana aiki da ita a boye.

Source: Facebook
"Peter Obi ya gaza jagorantar jam'iyya" - LP
Yayin da sanarwar ta ce babu wanda ya fi karfin ya aikata kuskure, ta ce:
"Amma ya kamata shugaba mai nagarta ya kasance mai iya amincewa da kuskurensa. Obi ya gaza bayar da jagoranci ga jam’iyyar, kuma wajibi ne ya dauki alhakin hakan.
“Don haka, abin takaici ne ga Obi da Dr. Otti su ci gaba da zargin gwamnatin tarayya da shisshigi a harkokin jam’iyyar, lamarin da ke ci gaba da bata sunan LP a idon jama’a.”
Tsagin jam’iyyar ya kuma tuna irin jajircewar da LP ta yi domin ba Obi dama ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023, yana mai cewa abin takaici ne ganin yadda abubuwa suka koma.
2027: Obi ya fadi jam'iyyar da zai yi takara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Peter Obi, ya tabbatar da aniyarsa ta sake tsayawa takarar shugaban kasa a zaɓen 2027 a ƙarƙashin jam'iyyar LP.
Peter Obi ya bayyana cewa gwamnatin tarayya na da hannu a rikicin da ke addabar jam'iyyun adawa na LP da PDP a Najeriya.
Obi ya yi kira ga matasa da su kasance masu jajircewa don tabbatar da cewa an kirga kuri'unsu yadda ya kamata a zaɓe mai zuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


