"Abubuwa Sun Lalace," Peter Obi Ya Faɗi Hanya 1 da Ƴan Najeriya Za Su Kawo Karshen Mulkin APC
- Tsohon ɗan takarar shugaban kasa, Peter Obi ya sake cacakar gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu kan halin da Najeriya ke ciki
- Mista Obi ya bayyana cewa lokaci ya yi da ƴan Najeriya za su haɗa kansu wuri guda, su kayar da wannan gwamnatin a zaɓen 2027
- Tsohon gwamnan ya koka kan yadda mutane ke rayuka cikin talauci, yunwa da rashin tsaro, wanda a cewarsa kowa ya zama ɗan gudun hijirar ƙarfi da yaji
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi, ya ci gaba da sukar gwamnatin APC mai ci karkashin jagorancin Bola Ahmed Tinubu.
Peter Obi ya kuma yi kira ga ɗaukacin ƴan Najeriya da su dunƙule wuri ɗaya, sun taho a haɗa kai domin kawo ƙarshen mulkin APC a zaɓen 2027.

Source: Twitter
Obi ya bayyana cewa gwamnatin Tinubu ta gaza cika alkawuranta, yayin da har yanzu Najeriya ke fama da da manyan matslolin irinsu rashin tsaro, Tribune Nigeria ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wane manyan matsaloli Najeriya ke fuskanta?
A cewarsa, har yau Najeriya na fama da kashe-kashe, yunwa, hauhawar farashi, talauci, faɗuwar darajar Naira da rashin aikin yi, shekara biyu bayan kafa gwamnati.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya yi wannan jawabi ne a Abuja yayin bikin ƙaddamar da wani littafi mai taken “Obi, the Political Change Agent”, wanda gogaggen ɗan jarida, Mr. Ike Abonyi, ya rubuta.
A cewar Obi, a lokacin da ‘yan Najeriya ke mutuwa saboda rashin magani da kwanciyar hankali sakamakon yunwa da rashin tsaro, ita gwamnati na can tana gyara gine-ginen da ba su da tasiri a rayuwar talaka.
2027: Peter Obi ya kawo mafita ga ƴan Najeriya
"Wannan gwamnatin ce muke so mu kora. Idan muka ci gaba da aiki tare, za mu ga bayanasu. Ku koma cikin jama'arku ku gaya musu cewa ba za mu ci gaba da tafiya a haka ba, dole mu canza."
"Mu ba yaki ne ya ɓalle a kasarmu ba amma ƴan Najeriya sun zama tamkar ƴan gudun hijira. Wasu sun gudu zuwa Chadi, wasu sun tafi Kamaru kuma a haka ba yaƙi muke ba."
"Dalili shi ne ba mu da gwamnati da ta damu da ƴan kasarta. Ana kashe mutane kullum; babu wanda ke ziyartarsu ko ya ce, ‘ba mu ji daɗi ba’ Babu wanda ya damu.
-Peter Obi.

Source: Facebook
Mista Obi ya ƙara da cewa zaben 2027 zai zama daban da na baya domin za su duba kura-kuran da suka yi a baya, su kauce masu, rahoton Vanguard.
Obi ya soki yadda aka cire tallafin fetur
A wani labarin, kun ji cewa Peter Obi ya soki hanyar da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bi wajen cire tallafin man fetur.
Peter Obi ya ce da shi ne, zai cire tallafin man fetur amma ta hanyar da ta dace kuma ba tare da jefa mutane cikin wahala ba.
Ya jaddada cewa cire tallafin fetur yana daga cikin kudurorinsa tun kafin zaɓen 2023, amma zai aiwatar da shi ne ta hanya mai tsafta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

