"Mulkin Tinubu Ya Fi na Buhari," Fayose Ya Yi Tsokaci kan Ƙoƙarin Gwamnatin APC

"Mulkin Tinubu Ya Fi na Buhari," Fayose Ya Yi Tsokaci kan Ƙoƙarin Gwamnatin APC

  • Tsohon gwamnan Ekiti, Ayodele Fayose ce halin da ake ciki a gwamnatin Bola Tinubu ya fi lokacin Muhammadu Buhari
  • Babban 'dan adawar yana yabon gwamnatin Tinubu ne a lokacin da wasu ke rade-radin zai iya sauya sheka zuwa APC mai-ci
  • Fayose ya ce yabon gwamnatin APC ba shi da nasaba da batun sauya sheka, domin ba zai taba rabuwa da PDP ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Tsohon gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose, ya ce a halin da Najeriya ke ciki a yanzu karkashin mulkin Bola Tinubu ya ɗara na Muhammadu Buhari ci gaba.

Fayose, wanda jigo ne a babbar jam'iyyar adawa ta PDP ya ce dama yana da yaƙinin za a samu ci gaba a gwamnatin da Bola Tinubu zai jagoranta.

Kara karanta wannan

Bayan ganawarsa da Tinubu, tsohon gwamna ya yi maganar yiwuwar barin PDP

Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari da Bola Tinubu
Tsohon gwamnan Ekiti ya ce mulkin Tinubu ya fi na Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Nigerian Tribune ta ruwaito Fayose ya ce a lokacin gwamnatin da ta gabata tattalin arziki ya karye, amma yanzu ana kokarin daidaita lamura a jagorancin Tinubu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ayo Fayose ya yabi mulkin Bola Tinubu

Jaridar Vanguard ta ruwaito Fayose ya yabi Tinubu ne a yayin da yake zantawa da manema labarai bayan ya kai wa shugaban kasa ziyarar Barka da Sallah a Legas.

Da aka tambaye shi dalilin ziyarar tasa ga shugaban kasa duk da kasancewarsa jigo a jam’iyyar hamayya, Fayose ya ce tun yana gwamna karkashin PDP yana da imani da jagorancin Tinubu.

A kalamansa:

“Tun ina gwamna a jam’iyyar PDP, ban boye goyon bayana ga Tinubu ba. Har yanzu ina da wannan imanin. Kuma abin da ya kamata mu yi a matsayin shugabanni shi ne mu ci gaba da karfafa masa gwiwa, domin mutane su gane yadda mulki ke da wahala.
“Tattalin arzikin da ya ruguje yanzu ana kokarin gyarawa. Amma kokarin da gwamnati ke yi wajen daidaita darajar kudin kasa ya sa aka ɗauki wasu matakai."

Kara karanta wannan

'Ndume ba ya iya bakinsa,' Fadar shugaban kasa ta yi zazzafan martani ga Sanatan Borno

Dalilin Fayose na ziyartar Tinubu

Fayose ya bayyana cewa ziyarar tasa ba ta da nasaba da wata alaka da sauya sheka ko sauyin jam’iyya, inda ya ce ta kashin kansa ne kawai, don karfafa gwiwar shugaban kasa.

Fayose ya ziyarci Tinubu
Fayose ya ce Najeriya ta fara dawo wa hayyacinta Hoto: @OlayinkaLere
Source: Twitter

Ya ce:

Dole ne mu yaba da abin da shugaban kasa ya riga ya aikata. Na taba yin suka sosai a kan gwamnatin da ta gabata, amma ba za a iya kwatanta halin da ake ciki yanzu da lokacin baya ba.”
“Na zo ne domin yin amfani da wannan dama ta dawowar sa gida domin karfafa masa gwiwa ya ci gaba da kokarin da yake yi wa ‘yan Najeriya.”

Game da rade-radin ko zai sauya jam’iyya, Fayose ya yi watsi da hakan, yana mai cewa ziyarar tasa ba ta da alaka da sauya sheka, kuma ba zai taba barin PDP ba.

ACF ta soki tallata shugaba Tinubu

A wani labarin, kun ji kungiyar ACF, ta nuna damuwa game da yadda wasu mutane ke fara kamfen din neman wa’adi na biyu ga shugaban kasa Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Hadimin Tinubu ya ajiye aiki, ya fadi dalilin rabuwa da gwamnatin APC

ACF ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwar barka da Sallah da sakataren ta na kasa, Mallam Murtala Aliyu, ya fitar a ranar Lahadi, 9 ga watan Yuni.

Kungiyar ta bayyana cewa abin da ya fi dacewa shi ne a ba shugaban dama ya kammala aikinsa na farfaɗo da tattalin arzikin kasa da samar da tsaro ga yan Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng