Zaben 2027: Dattawan Arewa Sun Dira a kan Masu Tallata Tinubu tun Yanzu
- Kungiyar ACF ta bukaci Shugaban kasa, Bola Tinubu da ya mayar da hankali kan gyaran tattalin arziki da tsaro maimakon kamfen na 2027
- ACF ta bayyana damuwa kan hauhawar farashin abinci, faduwar darajar Naira da kuma matsin lambar rayuwar da talakawa suke ciki a yau
- Sai dai ta bayyana takaicin yadda duka wadannan matsaloli ba su damu gwamnati ba, har aka mayar da hankali kan yakin neman zabe
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kaduna – Kungiyar Arewa Consultative Forum (ACF) ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya mayar da hankali kan farfado da Najeriya da kuma tattalin arzikinta da ke tangal-tangal.
Kungiyar ta ce wannan shi ne mafi muhummanci a yanzu, a maimakon fara kamfen na neman tazarce a 2027.

Kara karanta wannan
'Jam'iyya 1 ba za ta iya ba,' Tsohon dan takara ya fadi yadda za a kwace mulki daga Tinubu

Source: Facebook
Punch ta wallafa cewa wannan kira na ACF na zuwa ne a daidai lokacin da ake kara nuna damuwa kan yadda ƙasar ke tafiya da kuma gazawar gwamnati wajen shawo kan kalubalen da ke addabar ta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma a yayin babban taron APC na ƙasa, gwamnonin jam’iyyar, shugabannin majalisar dokoki, sun amince da Tinubu a matsayin ɗan takarar shugaban ƙasa na APC a 2027.
ACF ta soki fara yiwa Bola Tinubu Kamfe
BBC ta wallafa cewa, Sakataren Yada Labaran ACF na ƙasa, Farfesa Tukur Muhammad-Baba, ya nuna damuwa matuƙa kan matsalolin da ƙasa ke fuskanta.
A sanarwar da ya fitar, ya ce matsalolin da suka fi damun kasar sun hada da tabarbarewar tattalin arziki da tsadar abinci da kuma faduwar darajar Naira.

Source: Facebook
A cewarsa:
“Mun damu ƙwarai da yadda tattalin arzikin ƙasar ya tabarbare da kuma wahalar da 'yan Najeriya ke fuskanta. Muna kira ga Shugaba Tinubu da manyan hadimansa da su daina mayar da hankali kan kamfen na 2027, su dage wajen inganta rayuwar talakawa.”

Kara karanta wannan
Bangarori 3 da yan adawa da kungiyoyi ke ganin gazawar gwamnatin Tinubu a shekaru 2
Manyan Arewa sun ce kasa ta lalace
Kungiyar ta kuma zargi gwamnati da nuna halin ko-in-kula da matsalolin tsaro, hauhawar farashin kayan masarufi, ƙarancin wutar lantarki, da matsalolin kiwon lafiya da ilimi.
Sakataren kungiyar ya bayyana cewa, duk da wadannan kalubale, jam’iyyar APC ta fi mayar da hankali kan shirin sake tsayawa takara na Tinubu a 2027, wanda ya ce lokaci bai yi ba.
Ya ƙara da cewa:
“'Yan Najeriya na cikin wahala, kuma lokaci ya yi da gwamnati za ta tashi tsaye domin gyara ƙasa.”
ACF ta bukaci Shugaba Tinubu da ya daina kallon makomarsa a siyasa kawai, ya mayar da hankali kan sauƙaƙa rayuwar 'yan ƙasa da kuma ɗaukar matakan gyara ƙasar da ta yi rauni.
ACF ta bayyana damuwa kan rashin tsaro
A baya, mun wallafa cewa Kungiyar ACF ta bayyana damuwarta kan yadda rashin tsaro ke kara tabarbarewa a yankin Arewa, tare da jaddada cewa lamarin na zama babbar barazana ga shiyyar.
Shugaban kwamitin amintattun kungiyar, Alhaji Bashir Muhammad Dalhatu, ya bayyana hakan, tare da bayyana fargabar cewa rayuwar mazauna yankin na cikin halin ni 'ya su.
Alhaji Dalhatu, ya yi takaicin yadda a Arewa maso Gabas, ana fama da yan tayar da kayar baya, a Arewa maso Yamma akwai 'yan bindiga, a Arewa ta Tsakiya kuma ana ta rikicin makiyaya da manoma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
