Ana Shirin Zaɓe, Gwamna Ya Yi Martani kan Zargin Ziyartar Boka domin Neman Zarcewa

Ana Shirin Zaɓe, Gwamna Ya Yi Martani kan Zargin Ziyartar Boka domin Neman Zarcewa

  • Gwamna Charles Chukwuma Soludo na Anambra ya musanta zargin cewa ya tuntuɓi boka don neman nasarar zaɓe na ranar 8 ga Nuwamba
  • Mai magana da yawun gwamnan, Christian Aburime, ya ce bidiyon da ke yawo na barkwanci ne da wani ɗan kwaikwayo ya yi a taro
  • Ya ƙara da cewa Soludo na kokarin bunkasa tattalin arzikin jihar, kuma jama’a su ƙaurace wa yaɗa labaran ƙarya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Awka, Anambra - Gwamnan jihar Anambra, Farfesa Charles Chukwuma Soludo, ya yi martani kan zargin zuwa wurin boka game da zaɓen jihar da za a yi.

Gwamna Soludo ya karyata rade-radin da ake masa na cewa ya tuntuɓi boka kan batun neman tazarce.

Gwamna ya magantu kan zargin tuntubar boka
Gwamna Soludo ya musanta zargin zuwa wurin boka kan zabe. Hoto: Prof. Charles Chukwuma Soludo.
Source: Twitter

Hakan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa, Christian Aburime, ya fitar a ranar Laraba, cewar rahoton Tribune.

Kara karanta wannan

Gwamna ya karrama jami'in NIS da ya ki karbar N10m wajen bokan da aka kama

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar hukumar INEC kan zaben Anambra

Hakan na zuwa ne yayin da ake ta shirye-shiryen gudanar da zaɓen gwamnan Anambra da za a yi a watan Nuwambar 2025.

Hukumar INEC ta fitar da sanarwa game da shirye-shiryen zaɓen inda ta bukaci jam'iyyu su fara shirin gudanar da kamfe.

A cikin sanarwar, hukumar ta bukaci a fara kamfen daga ranar 11 ga watan Yuni har zuwa 6 ga watan Nuwambar 2025 ana saura kwana biyu zaben gwamnan jihar.

Zabe: Gwamna Soludo ya musanta ziyartar boka

Sanarwar ta bayyana zargin a matsayin karya tsagwaronta da babu kamshin gaskiya ko kadan a ciki.

Gwamnatin Charles Soludo ta ce bidiyon da ke yawo yana nuna wai Gwamna yana magana da boka, an ɗauke shi ne a wajen taro da masu kirkire-kirkire.

Aburime ya ce:

“A yayin taron, ɗaya daga cikin masu halartar ganawar ya gabatar da kwaikwayo, wanda hanya ce ta nishadi da mutane ke yi a Najeriya.”

Kara karanta wannan

Atiku: "Talakawa za su kada kuri'ar raba gardama kan gwamnatin Tinubu"

An fara shirin gudanar da zaben Anambra
Gwamna Soludo ya yi martani kan zargin ziyartar boka kan zabe. Hoto: Prof. Charles Chukwuma Soludo.
Source: Twitter

Rokon da Gwamna Soludo ya yi ga al'umma

Gwamnatin ta ce ba ta ji daɗin yadda masu adawa ke watsa bidiyon da gangan ba don yaɗa ƙarya da yaudarar jama’a, The Nation ta ruwaito.

“Shaidar gwamna Soludo wajen bunƙasa harkar nishaɗi a jihar ita ce 'Solution Fun City' da aka ƙaddamar kwanan nan.
“Muna roƙon jama’a su yi watsi da wannan ƙarya kuma su dinga tantance gaskiyar kowanne labari kafin yaɗawa.
“Gwamna Soludo ya mayar da hankali wajen cigaban jihar Anambra da aiwatar da shirinsa na 'Solution Agenda' a halin yanzu.”

- Cewar sanarwar

Tinubu ya yabawa Gwamnan Anambra, Soludo

Mun ba ku labarin cewa Shugaban kasa, Bola Tinubu ya bayyana cewa yana aiki kafada da kafada da Gwamna Charles Soludo domin ciyar da jihar Anambra.

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da ya kai ziyarar aiki ta farko zuwa jihar tun bayan da ya karbi ragamar jagorancin Najeriya.

Shugaban ya bayyana jin dadinsa da ci gaban jihar, har ya bayyana burinsa na samun fili domin gina gidan ritaya a Anambra.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.