"Ka Zama Ginshiƙi," An ba Gwamna Shawara kan Batun Sauya Sheka zuwa APC kafin 2027
- Ayodele Fayose ya shawarci gwamnan jihar Abia, Alex Otti ya hakura ya zauna a jam'iyyar LP duk da rigingimun cikin gidan da suka addabe ta
- Fayose, tsohon gwamnan jihar Ekiti ya ce Otti ya zama ginshiƙi a LP, don haka bai kamata ya ruɗu da waɗanda ke tururuwar komawa APC ba
- Ya ce duk da bai cika yabon ɗan siyasa ba amma ayyukan da Gwamna Otti ya yi a jihar Abia cikin shekaru biyu sun nuna nagartarsa a fili
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Abia - Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya shawarci Gwamnan Abia, Alex Otti, da kada ya sake ya sauya sheka daga jam’iyyar LP zuwa wata.
Ayo Fayose ya buƙaci Gwamna Otti ya daure ya ci gaba da zama a LP duk da rikice-rikicen siyasa da tururuwar sauya shekar da ake yi a Najeriya.

Kara karanta wannan
"Ku bari na nemi zaɓin Allah," Gwamna ya yi magana kan yiwuwar tsayawa takara a 2027

Source: Facebook
Fayose ya bayyana hakan ne a ranar Lahadi yayin wata ziyara ta musamman da ya kai gidan Gwamna Otti da ke garin Nvosi, karamar hukumar Isiala Ngwa ta Kudu, Channels tv ta rahoto.
Fayose ya roki Gwamna Otti ya zauna a LP
Ya yabawa kokarin da Otti ke yi a jihar Abia, yana mai cewa gwamnan ya riga ya zama wata "cibiya mai tasiri" a jam’iyyar LP, wanda ya kamata ya tsaya duk rintsi a cikinta.
"Mai girma gwamna, kada ka sauya sheka. Kai wani ginshiƙi ne a nan, idan muka duba bambance-bambancen Najeriya, muna bukatar tsarin jam’iyyu da yawa.
"Ko da ace kowa ya bar jam’iyyar LP, ina ba da shawari kai ka zauna. Kai ne shugaban jam’iyya na kasa a nan,” in ji Fayose.
Gwamna Otti na shirin komawa APC?
A watan Afrilu, Gwamna Otti ya musanta jita-jitar cewa yana shirin sauya sheka zuwa jam’iyyar APC, yana mai bayyana rahotannin da, “karya mara tushe ballantana makama.”

Kara karanta wannan
Wike ya cika baki kan batun korarsa daga PDP, ya kalubalanci jiga jigan jam'iyyar
Game da kiraye-kirayen da magoya baya ke masa na ya tsake neman takara karo na biyu a 2027, Gwamna Otti ya buƙaci a ba shi lokaci ya nemi shawara da zabin Allah tukuna.
A lokacin zamansa a Abia, Fayose ya ziyarci wasu daga cikin muhimman ayyukan da gwamnatin Otti ke aiwatarwa a biranen Umuahia da Aba.

Source: Facebook
Tsohon gwamna ya yabawa Alex Otti
Ya jinjinawa kokarin gwamnatin Abia wajen inganta hanyoyin mota, kiwon lafiya, da ilimi.
“Talakan Abia na more ayyuka masu amfani da inganci, na ga yadda ake kokarin inganta rayuwar jama’a tare da kawo masu ci gaba.
"Abin da na gani ya gamsar da ni matuka. Na ga cibiyoyin kiwon lafiya na al’umma da aka gyara, wasu kuma sababbi ne.
"Duka ayyukan da muka ziyarta, abin burgewa ne. Ba ni da dabi’ar yawan yabo, amma cikin shekaru biyu kacal, dole a ba wa Gwamna Otti makin nasara saboda namijin kokarinsa.”
Gwamna Otti zai maida gidan gwamnati otal
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Alex Otti ya bayyana shirin gwamnatinsa na mayar da gidan gwamnatin Abia zuwa katafaren otal.
Kwamishinan yaɗa labarai, Okey Kanu ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin Abia lokacin da ya kai ziyara wurin gine-ginen gidan gwamnatin.
Kanu ya kara da cewa za a gina sabon ofishin gwamna da masauki a cikin tsohon gidan gwamnatin da ake amfani da shi yanzu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
