Gwamnan PDP Ya Fara Shan Yabo da Ya ba Shugaban APC Kyautar Danƙareriyar Mota
- Gwamnan Akwa Ibom, Fasto Umo Eno, wanda har yanzu ɗan PDP ne ya ba shugaban APC na jihar, Obong Stephen Ntukekpo kyautar mota
- Wannan kyauta dai ta ja hankalin APC, inda ta fito tana yabawa salon mulkin Gwamna Eno na adalci ba tare da nuna banbancin siyasa ba
- An miƙa kyautar motar a wurin bikin cikar gwamna Umo Eno shekaru biyu a gadon mulki a cibiyar ƙasa da ƙasa da ke Uyo
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom - Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya fara shan yabo da ya gwangwaje shugaban jam'iyyar APC da kyautar danƙareriyar mota Prado Jeep.
Duk da cewa ba jam'iyyarsu ɗaya ba, Gwamna Eno na PDP ya ba shugaban APC na jihar, Obong Stephen Ntukekpo, wannan kyauta ne a wani yunkuri na haɗa kan manyan mutanen Akwa Ibom.

Source: Twitter
APC ta karɓi kyautar motar hannu biyu
Jaridar Leadership ta tattaro cewa APC ta jihar Akwa Ibom ta yaba wa gwamnan bisa wannan karamci, kuma ta karɓi kyautar hannu biyu.
Da yake yaba wa gwamnan kan wannan abin da ya kira da dabara mai nuna kwarewa a siyasa, sakataren yada labaran APC a jihar, Barista Otoabasi Udo, ya ce jam’iyyar ta karɓi kyautar da farin ciki.
Kakakin APC ya kuma bayyana kyautar motar a matsayin alamar da ke nuna cewa Gwamna Eno ya rungumi siyasar wayewa da karimci.
“Jam’iyyar APC ta jihar Akwa Ibom na godiya matuƙa ga gwamnanmu mai farin jini, Fasto Umo Bassey Eno, bisa wannan kyautar motar SUV Prado Jeep da ya bai wa shugabanmu na jiha, Obong Stephen Leo Ntukekpo,” in ji shi.
Gwamna Eno ya miƙawa shugaban APC mota
An gano cewa an mika kyautar motar ne yayin bikin cikar shekara biyu da gwamnan ya yi a ofis, wanda aka gudanar a ɗakin taro na ƙasa da ƙasa da ke Uyo.
Gwamna Eno ya yi amfani da wannan damar wajen nuna wasu daga cikin manyan ayyukansa a cikin ƙaramin lokacin da ya ɗauka a kan mulki.
Baya ga haka, gwamnan ya yi bayani kan zaman lafiya da kwanciyar hankali da aka samu a jihar karkashin mulkinsa, wanda ya ce su ne tushe na ci gaba da nasarorin da ake samu a Akwa Ibom.

Source: Facebook
Gwamna Umo Eno na shirin komawa APC
Gwamna ya jaddada cewa jam’iyyar siyasa, ko A ko B, wata mota ce kawai da ɗan siyasa ke amfani da ita don kai wa ga manufofinsa na ci gaban al’umma.
Kakakin APC ya shawarci jama’a da kada su tayar da ƙura ko ɗaga jijiyar wuya dangane da yiwuwar sauya shekar da mai girma gwamna zai yi, rahoton Vanguard.
Gwamna Eno yana shirin komawa APC
A wani labarin, kun ji cewa Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya tabbatar da shirinsa na ficewa daga PDP zuwa jam'iyyar APC.
Fasto Eno ya ce duk da ya ci zabe a 2023 karkashin PDP, yanzu alamu sun nuna jam’iyyar ba ta da tsari mai ɗorewa da zai tabbatar masa da nasara a 2027.
Gwamnan ya ce yana son zama a PDP, amma dole zai hakura ya bar ta saboda rikicin shugabanci da ke addabarta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

