Kujerar Ɗan Majalisar Tarayya Ta Fara Tangal Tangal, PDP Ta Buƙaci Kotu Ta Tsige Shi

Kujerar Ɗan Majalisar Tarayya Ta Fara Tangal Tangal, PDP Ta Buƙaci Kotu Ta Tsige Shi

  • Jam'iyyar PDP ta maka ɗan Majalisar Tarayya mai wakiltar Obokun/Oriade daga jihar Osun, Hon. Oluwole Oke a gaban kotu saboda ya koma APC
  • PDP ta buƙaci kotun ta tilasta wa kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ayyana kujerar ɗan Majalisar a matsayin babu kowa a kanta
  • Tun farko dai Hon. Oke ya fice daga PDP zuwa APC ne saboda rikicin da take fama da shi kamar yadda ya ambata a wasiƙar sauya shekarsa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Jam’iyyar PDP ta maka ɗan majalisar tarayya daga jihar Osun, Oluwole Oke, a kotu, tana neman a tuɓe shi daga kujerarsa bayan ya sauya sheka zuwa APC.

Hakan na kunshe ne a wata kara da lauyan jam’iyyar reshen Osun, Raphael Oyewole, ya shigar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja a madadin PDP.

Kara karanta wannan

Sanata a Majalisar Dattawa ta 9 ya ƙara jiƙawa PDP aiki, ya fice daga jam'iyyar

Hon. Oluwole Oke.
PDP ta kai ƙarar ɗan Majalisar Tarayya gaban kotu, ta bukaci a tsige shi Hoto: Hon. Oluwole Oke
Source: Twitter

Rahoton Punch ya tattaro cewa jam’iyyar ta nemi a tilasta wa Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ya ayyana kujerar Oke a matsayin babu kowa a kanta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

PDP ta karanto hujjoji daga kundin tsarin mulki

PDP ta yi nuni da cewa hakan zai tabbatar da bin tanadin sashe na 68(1)(g) da (2) na Kundin Tsarin Mulki na 1999 (wanda aka gyara).

A cewar PDP, sashen ya bayyana cewa duk mamban da ya sauya jam’iyya ba tare da rikici ko ɓangaranci a cikin jam’iyyar da ta kai shi kan kujerar ba, to lallai ya rasa kujerarsa.

Hon. Oke, mai wakiltar Obokun/Oriade ta jihar Osun a Majalisar Wakilai, ya sauya sheka daga PDP zuwa APC ne bisa shawara da ya ce ya yi tare da abokan siyasa, dangi, da masu ruwa da tsaki.

A wasikar murabus dinsa mai kwanan wata 16 ga Afrilu, Oke ya aika wa shugaban PDP na gunduma ta 7 a Karamar Hukumar Obokun tare da kwafinta zuwa ga shugabannin jam’iyyar na jiha da na kasa.

Kara karanta wannan

Su wanene ke juya akalar gwamnatin Shugaba Bola Tinubu? Minista ya koro bayani

Jam'iyyar PDP ta taso ɗan Majalisar Wakilai

Yayin da take martani, PDP ta jero Oke, Kakakin Majalisar Wakilai, magatakardan Majalisa, da Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) a matsayin waɗanda take ƙara.

Ta shigar da karar da lamba FHC/ABJ/CS/1040/2025, inda jam'iyyar ta gabatar da tambayoyi bakwai da bukatu takwas kan sauya sheƙar Hon. Oke.

Tutar PDP.
PDP ta nemi a dakatar da biyan Oke albashi da alawus Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Facebook

PDP ta nemi kotu ta umurci Kakakin Majalisa da INEC da su bi tanadin kundin tsarin mulki, su shirya zaɓen cike gurbi a mazabar Obokun/Oriade.

Jam’iyyar ta kuma bukaci a dakatar da Oke daga karbar albashi da duk wasu alawus, kamar yadda Premium Times ta rahoto.

Bugu da kari, PDP ta roki a tilasta masa mayar da duka albashi, alawus, da sauransu da ya karba tun daga ranar da ya fice daga PDP har zuwa ranar da kotu za ta yanke hukunci.

Wike: Rikici ya ƙara ɓarkewa a PDP

A wani labarin, kun ji cewa abubuwa na kara rikirkicewa jam'iyyar PDP a lokacin da jam'iyyun siyasa ke shirin zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

"Ba zan iya ci gaba da zama ba," Ɗan Majalisar Tarayya ya sauya sheƙa zuwa APC

Ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike ya ce daga yanzu ya tsame hannunsa daga duk wata yarjejeniya da aka cimma a PDP saboda cin amana ta yi yawa.

Tsohon gwamnan ya zargi Gwamna Seyi Makinde da Peter Mba da saɓa wa yarjejeniyar da aka cimma a gidan Sanata Bukola Saraki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262