Sanata a Majalisar Dattawa Ta 9 Ya Kara Jiƙawa PDP Aiki, Ya Fice daga Jam'iyyar

Sanata a Majalisar Dattawa Ta 9 Ya Kara Jiƙawa PDP Aiki, Ya Fice daga Jam'iyyar

  • Tsohon ɗan Majalisar Dattawa, Sanata Istifanus Gyang ya fice daga PDP a jihar Filato da jam'iyyar ta ke mulki tun watan Mayun 2023
  • Sanata Gyang, wanda ya wakilci Filato ta Arewa a Majalisar Dattawa, ya tabbatar da haka ne a wata wasiƙa da ya aike wa shugaban PDP
  • Ya ce ya ɗauki wannan matakin ne saboda PDP ta sauka daga aƙidar dimokuraɗiyya kuma ba ta damu da buƙatun jama'a ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Plateau - Sanata Istifanus Gyang, wanda ya wakilci jihar Filato ta Arewa a Majalisar Dattawa ta tara, ya fice daga jam’iyyar PDP.

Tsohon ɗan Majalisar Tarayyan ya zargi jam’iyyar PDP da kaucewa akidun dimokuraɗiyya da rashin mayar da hankali kan bukatun jama’a.

Istifanus Gyang.
Tsohon sanatan Filato ta Arewa ya fice daga jam'iyyar PDP Hoto: Senator Istifanus Gyang
Source: Facebook

Sanata Gyang ya bayyana hakan ne a wata wasika mai kwanan wata 26 ga Mayu, 2025, da ya aika wa shugaban PDP na Gundumar Rafan, a Karamar Hukumar Barkin Ladi, jihar Filato, cewar rahoton Leadership.

Kara karanta wannan

Kujerar ɗan Majalisar Tarayya ta fara tangal tangal, PDP ta buƙaci kotu ta tsige shi

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me yasa Sanata Gyang ya fita daga PDP?

Ya ce ya shafe tsawon shekaru yana yi wa PDP aiki tare da bayar da gudummuwa a zaɓe domin nasarar jam'iyyar, amma a yanzu lokaci ya yi da zai bar ta.

A cikin wasikar, Sanata Gyang ya ce:

"Bayan shekaru akalla 10 ina ba da cikakken goyon bayana ga PDP tare da gudummuwa wajen samun nasarar jam'iyyar musamman a zaɓen 2023, lokacin tafiyata ta yi.
"A yanzu PDP ta sauka daga tsarin dimokuraɗiyya kuma ba ruwanta da muradan jama'a, wannan ya sa na ga ya dace na tattara kayana na bar ta."

Tsohon sanatan ya kara da cewa duk da PDP ta karɓi mulki a Filato, amma ta gaza samar da tsari a cikin gida ta yadda za a samu damarmaki da kwarin gwiwar kare muradun al'umma.

Sanata Gyang.
Sanata Gyang ya ce PDP ta sauka daga tubalin da aka kafa na bunƙasa tsarin dimokuraɗiyya Hoto: @CJPAM1
Source: Twitter

PDP ta rasa babban jigo a Filato

Gyang ya jaddada cewa dole ne ya yi ƙoƙarin kare adalci, daidaito, haɗin kai, da kyakkyawan mulki, tare da tabbatar da cewa siyasa ta kasance fili da kowa zai iya shiga ba tare da tsangwama ba.

Kara karanta wannan

Malami: Ministan Buhari yi yi wa Tinubu, Ganduje da 'yan APC rubdugu kan tsaro

Sanata Gyang na daya daga cikin manyan jiga-jigai na PDP a Filato, ya riƙe kujerar Ɗan Majalisar Wakilai mai wakiltar Barkin Ladi da Riyom da Mataimakin Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dattawa.

Ficewarsa daga PDP na iya haifar da babban giɓi a jam'iyyar ta jihar Filato, saboda kasancewarsa mutum mai tasiri da ƙarfi a harkokin siyasa, rahoton Punch.

Abba Moro ya musanta rushewar PDP

A wani labarin, kun ji cewa shugaban marasa rinjaye na Majalisar Dattawa, Sanata Abba Moro ya ce jam'iyyar PDP ba za ta rushe ba kafin 2027.

Sanata Abba ya kuma tabbatarwa ƴan Najeriya ba za su bari ƙasar nan ta koma hannun jam'iyya ɗaya kaɗai ba.

Jagoran ƴan adawa a Majalisar Dattawa ta 10 ya ce da zarar jam'iyyar PDP ta zaɓi sababbin shugabanni, jam’iyyar za ta farfaɗo daga halin da ta tsinci kanta a ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262