Zaɓen 2027: Jam'iyyar LP Ta Yi Watsi da Haɗakarsu Atiku, Ta Caccaki Peter Obi
- Jam’iyyar LP ta nesanta kanta daga haɗakarsu Atiku Abubakar, inda ta bayyana cewa ba ta cikin shirin haɗaka da kowace jam’iyya
- Ta gargadi Peter Obi da sauran jiga-jigan jam’iyyar da su nesanta kansu daga ire-iren wannan haɗaka domin ba ta aiki kowa ba
- LP ta ce halartar Obi taron haɗin gwiwa ba tare da amincewar jam’iyya ba ya nuna raini ga shugabancin jam’iyyar da ƙin girmama doka
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Gabanin zaɓen 2027, jam’iyyar LP a ranar Litinin, 26 ga Mayu, ta ƙi yarda da kowace haɗin gwiwar siyasa da sauran jam’iyyun adawa.
Jam'iyyar LP ta ja kunnen ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, da sauran masu ruwa da tsaki a LP da su nisanci haɗin gwiwar da ake ta yayatawa.

Kara karanta wannan
ADC: Maganar hadakar adawa ta yi nisa, ana dab da cimma matsaya kan zaben jam'iyya

Source: Twitter
LP ta nesanta kanta daga hadakarsu Atiku
Wannan gargadin tare da nesantawar na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin LP, Obiora Ifoh, ya sa fitar a shafin jam'iyyar na X.
Tsagin jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Julius Abure ta jaddada cewa ba ta cikin wata tattaunawa ko shiri na haɗin gwiwa da kowace jam’iyya.
Ta ce saboda haka, ba ta goyon bayan mu’amalar da Peter Obi ke yi da jagororin shirin haɗakar adawa irin su Atiku Abubakar.
LP ta yi kira ga ‘yan jam’iyya da su kasance masu biyayya ga shugabancin LP na ƙasa, kwamitin amintattu, gwamnan jam’iyyar guda rak (Alex Otti) da sauran masu ruwa da tsaki da ke ƙoƙarin bunƙasa jam’iyyar.
LP ta ce Peter Obi ya raina shugabanninta
A cikin sanarwar, LP ta ce:
“Mai girma Peter Obi, sa’o’i kaɗan bayan ya bayyana niyyarsa ta tsayawa takara a ƙarƙashin jam’iyyar LP, an gan shi a ranar Lahadi, 25 ga Mayu, yana halartar wani taron ƙungiyar haɗin gwiwa a Abuja ba tare da izini ko amincewar shugabancin LP ba.
"Wannan abu ya daɗa rikita mu, kuma muna ganin Obi bai tabbatar da matsayinsa kan zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba.
"Mun sha faɗa cewa jam’iyyar LP ba za ta shiga kowace irin haɗakar siyasa kafin babban zaɓen 2027 ba, don haka ba za mu lamunci mu’amalar da Obi ke yi da waɗannan ƙungiyoyi ba.
"Wannan ƙalubale ne ga shugabancin jam’iyyar, kuma muna ganin hakan raini ne ga ikon jam’iyya na yanke shawara kan al’amuranta."

Source: Twitter
Jam'iyyar LP za ta ba Obi tikiti kai tsaye ba
Da wannan sanarwar ne LP ta bayyanawa ‘yan Najeriya cewa ba za ta ba Obi tikiti kai tsaye a 2027 ba, dole ne ya gwabza da masu sha'awar yin takara krkashin jam'iyyar.
Duk da dangantakarsa da jagororin ƙungiyoyin jam’iyyu masu adawa da ke ƙoƙarin kalubalantar APC a zaɓen 2027, tsohon gwamnan jihar Anambra ya shaida wa magoya bayansa cewa zai tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar LP.
Sai dai wannan sanarwar na iya zama wani kalubale a gare shi, domin dole ne ya gwabza da masu son yin takarar shugabancin kasar karkashin LP, idan yana son tikitinta.
Karanta cikakken jawabin jam’iyyar LP da ta wallafa a shafinta a ƙasa:
Peter Obi ya magantu kan hakura da takara
A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya bayyana lokacin da zai daina shiga harkar siyasa.
Obi ya ce zai sake tsayawa takara a 2027 a ƙarƙashin LP, amma yana iya ficewa daga siyasa gaba ɗaya bayan wannan yunƙurin.
Tsohon gwamnan jihar Anambra ya ce zai cika shekara 65 a 2027, kuma ba lallai ya sake sha’awar neman muƙamin gwamnati ba bayan wannan lokaci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

