Gwamnonin PDP Sun 'Zagaya' Wike, Ministan Ya Kara Dagula Lamuran Rikicin Jam'iyyar
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa ya fice daga duk wata yarjejeniya da aka cimma cikin jam’iyyar PDP saboda cin amanar da ake yi
- Wike ya zargi Gwamna Seyi Makinde da Peter Mba da take yarjejeniyar da aka cimma a gidan Bukola Saraki, yana mai cewa hakan zai rusa jam’iyyar
- Ministan ya ce yana da hannu wajen nasarar gwamnonin PDP da dama, amma bai da wata bukata ta karan kansa, kuma zai ci gaba da gwabzawa da su
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike ya yi matsaya dangane da rikicin da ke addabar PDP, yana mai cewa ya gaji da cin amanar da wasu 'yan jam’iyyar ke yi.
Wike ya bayyana cewa tun bayan zaben 2023, jam’iyyar PDP ta tsinci kanta cikin rudani da rashin amincewa da yarjejeniyoyi, wanda ke kara haifar da rikici tsakanin shugabanninta.

Source: Facebook
Cikin wata sanarwa da ya fitar a Facebook, Wike ya yi bayani kan yadda abubuwa suka lalace da kuma matakin da ya dauka na ficewa daga duk wata yarjejeniya da aka cimma a baya.
Yarjejeniyar da Wike ya ce an kulla a PDP
Wike ya bayyana cewa bayan taron G5 a Legas, an ci gaba da wani babban taro a gidan Bukola Saraki a Abuja, inda aka cimma matsaya kan manyan batutuwa.
Daga cikin yarjejeniyoyin da aka cimma akwai tabbatar da Samuel Anyanwu a matsayin Sakataren PDP, janye duk shari’o’i da suka shafi Ribas da kuma daina saba alkawura.
Wike ya zargi gwamnoni da karya alkawari
Ministan ya ce kafin kwamitin sasanci da Bukola Saraki ke jagoranta ya fara aiki, Gwamna Seyi Makinde da Peter Mba sun karya yarjejeniyar da aka yi da gangan.
Wike ya zarge su da shirya wani taron shugabannin Kudu maso Gabas da nufin tsige Anyanwu daga mukaminsa.

Source: Facebook
Baya ga haka, Punch ta wallafa cewa Wike ya ce sun shirya sanya Mataimakin Sakataren PDP na Kasa a matsayin wanda zai rike mukamin na wucin gadi.
Wike ya ce zai cigaba da gwabzawa da PDP
Wike ya nuna takaicinsa kan yadda aka hana gudanar da taron zaben PDP a Jos bayan INEC ta ki halarta saboda rashin sa hannun Sakataren da doka ta amincewa da shi.
Ya ce ya dade yana sadaukar da kansa don ci gaban jam’iyyar tun daga 1998, amma wasu daga cikin shugabannin yanzu sun mayar da jam’iyyar tamkar mallakarsu
Wike ya ce shi ne ya taimaka wajen nasarar yawancin gwamnonin PDP a zabe, amma bai taba neman wani abu na kai tsaye daga gare su ba.
Ya bayyana cewa yanzu ya yanke shawarar janye daga duk wata yarjejeniya da aka yi, kuma zai ci gaba da gwagwarmaya har sai gaskiya ta yi halinta a jam’iyyar PDP.

Kara karanta wannan
Duk da gargaɗin Tinubu ga masu sauya sheƙa, ɗan majalisa ya tattara kayansa zuwa APC
Kwamitin sulhun PDP ya yi zama a Enugu
A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Abubakar Bukola Saraki ya jagoranci zaman kwamitin sulhun PDP a Enugu.
Abubakar Bukola Saraki ya hadu gwamna Peter Mba na jihar Enugu tare da wasu sanatocin jam'iyyar.
Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo ya ce za su cigaba da tattaunawa domin kawo karshen rikicin jam'iyyar kuma za su yi taro a Kano.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

