'Saura Kaɗan a Ƙona Ni da Raina': Ɗan Majalisa Ya Sha da Ƙyar Yayin Zanga Zanga

'Saura Kaɗan a Ƙona Ni da Raina': Ɗan Majalisa Ya Sha da Ƙyar Yayin Zanga Zanga

  • Tsohon ɗan wasan kwaikwayo, Desmond Elliot ya bayyana yadda aka kusa kona shi a ofishinsa a Surulere lokacin zanga-zangar EndSARS a 2020
  • Elliot wanda dan majalisa ne a Lagos ya ce ya kasa komawa gida saboda dokar hana fita, ya kwana a ofishinsa inda wasu suka kai masa hari da kwalba mai wuta
  • Ya ce wata matashiya ’yar mai gidan da ke kusa da ofishinsa ce ta fitar da shi daga cikin haɗarin da ya kusa kashe shi

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Ikeja, Lagos - Ɗan majalisar jihar Lagos ya sha da kyar yayin da ake gudanar da zanga-zanga a shekarar 2020.

Tsohon ɗan fim, Desmond Elliot, ya bayyana yadda Allah ya tseratar da shi daga kona shi da aka yi niyyar yi a lokacin.

Kara karanta wannan

Bill Gates: Mai kudin duniya na 13 zai kyautar da gaba ɗaya dukiyarsa, ya sanya lokaci

Dan majalisa ya sha da kyar a zanga-zanga
Yadda dan majalisa ya sha da kyar yayin zanga-zanga. Hoto: Desmond Elliot.
Source: Instagram

Zanga-zanga: Barazanar da dan majalisa ya fuskanta

Elliot ya ce ya fuskanci barazana lokacin zanga-zangar EndSARS a shekarar 2020 da aka yi a Lagos, cewar Vanguard.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin wata hira da aka yi da shi a shirin 'Nollywood On Radio', dan majalisar jihar Lagos ya ce ya makale a ofishinsa da ke Surulere saboda dokar hana fita.

Ya ce ba zai iya komawa gidansa da ke Lekki ba, hakan ya sa ya zauna a ofishin domin kwana, lamarin da ya rikide zuwa haɗari.

Elliot ya ce:

“Lokacin dokar hana fita a lokacin EndSARS, samari marasa tarbiyya sun shigo Surulere, kuma ba zan iya komawa gida ba.
“Ina makale a Lekki, na kasa komawa gida, sai na koma ofishina da ke Surulere."
Dan majalisa ya tsallake rijiya da baya a zanga-zanga
Dan majalisa ya tsira da kyar a zanga-zanga. Hoto: Desmond Elliot.
Source: Instagram

Yadda dan majalisa ya sha da ƙyar lokacin zanga-zanga

Ɗan siyasar mai shekara 51 ya ce yana kallo ne a talabijin yana shirin kwana lokacin da rikici ya ɓarke wanda ya tayar da hankalin gwamnatin kasar.

Kara karanta wannan

Abin boye ya fito: Rundunar tsaro ta faɗi wadanda ke kai hare hare a jihohin Arewa

A cewarsa, lamarin ya ƙara dagulewa ne lokacin da ya ji hayaniya a wajen ofis din da yake, The Nation ta ruwaito.

Ya kara da cewa:

“Ina cikin ofis ba tare da sanin wani abu zai faru ba, na kasance ina kallon talabijin saboda niyyar kwana na yi.
“Na ji ’yar mai gidan mu tana ihun cewa ni ba mazaunin can ba ne."

Lamarin ya zama hadari bayan ɗan lokaci, ya san akwai matsala ne lokacin da aka jefa kwalba mai ɗauke da mai da wuta cikin ofis.

“Na kira shugaban ma’aikata domin neman taimako. Ban taɓa jin tsoro haka ba a rayuwata, abin ya firgita ni sosai."

- A cewar Elliot

Desmond Elliot ya ba mata sabon gida

Kun ji cewa tsohon ɗan wasan Nollywood kuma darakta mai suna Desmond Elliot ya ba wata mata kyautar sabon gida da aka sanya sababbin kayayyaki a ciki.

Desmond Elliot dai a wancan lokaci dan wasan Nollywood ne, haka kuma darekta ne a masana’antar, kafin daga bisani ya nemi takarar dan majalisa a Lagos.

Wannan yana daga cikin alkawuran da yayi a lokacin da yake yakin neman zabe, wanda suka hada da ba da gudunmawarsa domin a gyara wutar lantarkin da ke jihar Lagos.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.