Desmond Elliot ya baiwa wata mata wacca bata da gida sabon gida.
Babban dan was an Nollywood kuma Daracta mai suna Desmond Elliot ya baiwa wata mata wacca bata da gida kyautan sabon gida da aka sanya sabbin kayayyaki a ciki.
Desmond Elliot dai dan wasan Nollywood ne, haka kuma Daracta ne a masana’antar, domin kuwa sananne ne a kaffafen talabiji dakuma sauran sauran wasannin da akeyi a talabiji. Wanda daga baya ya shiga harkar siyasa.
Desmond, a kwanakin baya ya bayyana a shafinsa na tweeter irin ayyukan da yayi. Inda ya baiwa wata matan data yabeshi dangane da wasu ayyuka da yayi na wasu fanfunan birtsatse, inda ya baiwa matar kyautar sabon gida da akariga akasa komai da komai aciki.
Wannan yana daga cikin alkawuran da yayi aokacin da yake yakin neman zabe, wanda suka hada da bada gudun mayarsa domin a kyara wutar lantarkin dake jahar Legas. Haka kuma magoya bayansa sun yaba da irin ayyukan da yayi na alheri a yankin, inda sukaci gaba da yin bayani mai kyau a kansa.
Asali: Legit.ng