Rikicin Shugabanci: Jam'iyya Ta Dakatar da Gwamna da Ƴan Majalisar Tarayya 5 Nan Take

Rikicin Shugabanci: Jam'iyya Ta Dakatar da Gwamna da Ƴan Majalisar Tarayya 5 Nan Take

  • Rikicin shugabanci da ya dabaibaye jam'iyyar LP ya ƙara tsanani yayin da tsagin Julius Abure ya dakatar da gwamnan Abia da ƴan Majalisa 5
  • A wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren LP na ƙasa, Umar Farouk Ibrahim, ya ce an dakatar da su ne bisa zargin cin amanar jam'iyya
  • Umar Farouk ya ce daga yanzu waɗanda aka dakatar ba za su ƙara wakiltar jam'iyyar ko amfani da sunanta a kowane wuri ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Rikicin cikin gida da ke addabar jam’iyyar Labour LP ya dauki sabon salo a ranar Laraba, 7 ga watan Mayu, 2025.

Tsagin jam’iyyar LP karkashin jagorancin Julius Abure ya sanar da dakatar da Gwamnan jihar Abia, Dr. Alex Otti, bisa zargin ayyukan cin amanar jam'iyya.

Kara karanta wannan

An fara kera makaman yaki a Najeriya, sufeton 'yan sanda ya ziyarci masana'antar

Gwamna Alex Otti.
LP ta dakatar da Gwamna Alex Otti da Ƴan Majalisar Tarayya 5 Hoto: Alex C. Otti
Source: Facebook

Hakan na kunshe ne a wata sanarwa da LP ta wallafa a shafinta na X mai ɗauke da sa hannun sakatarenta na ƙasa, Umar Farouk Ibrahim.

LP ta dakatar da gwamna da ƴan Majalisa

Haka zalika, jam’iyyar LP ta dakatar da wasu ‘yan majalisar tarayya guda biyar da suka hada da Sanata Ireti Kingibe da Sanata Darlington Nwokocha.

Sauran su ne, Hon. Victor Afam Ogene; Hon. Amobi Ogah da Hon. Seyi Sowunmi, bisa zargin aikata irin wannan laifi na cin amanar jam'iyya.

Sakataren LP ya ce Kwamitin Zartarwa na Kasa (NEC) na LP ya kafa kwamitin ladabtarwa mai mutum biyar ranar 2 ga Mayu, karkashin jagorancin mataimakin shugaban jam’iyyar na kasa, Dr. Ayo Olorunfemi.

Meyasa LP ta dakatar da gwamnan Abia?

Umar Farouk ya ce an kafa wannan kwamiti ne domin gudanar bincike kan zarge-zargen da ake wa Gwamna Otti da sauran mambobin da lamarin ya shafa.

Bayan gudanar da bincike, kwamitin ya gabatar da rahotonsa, kuma jam’iyyar LP ta amince da rahoton tare da yanke hukuncin dakatar da mambobin da aka ambata.

Kara karanta wannan

Gwamna Zulum ya haramta sayar da barasa a jihar Borno, ya zargi jami'an tsaro

LP ta aika saƙo ga INEC da NGF

“Daga yau, Gwamna Alex Otti da sauran mambobin da aka ambata ba za su sake wakiltar jam’iyyar LP ko yin aiki da sunanta ba.
"Muna buƙatar dukkan masu ruwa da tsaki ciki har da Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Majalisar Tarayya, INEC da jami’an tsaro su dauki wannan sanarwa da muhimmanci.”

- Umar Farouk Ibrahim.

Abure.
Jam'iyyar LP aika sako ga INEC kan dakatar da Gwamna Otti da ƴan Majalisa Hoto: @LabourNG
Source: Twitter

LP ta kuma ƙara da cewa sunan shugaban kwamitin riko da tsohon dan takarar shugaban kasa, Mista Peter Obi, ya kafa wato Nenadi Usman, bai shiga cikin jerin wadanda aka dakatar ba saboda ba ƴar jam'iyya bace.

Wannan mataki ya ƙara nuna yadda rigimar shugabanci a LP ke ƙara tsananta yayin da babban zaben 2027 ke gabatowa.

LP ta nesanta kanta daga haɗakar ƴan adawa

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar LP ƙarƙashin jagorancin Julius Abure ta bayyana cewa ba za ta shiga ƙawance da ake shirin yi gabanin zaɓen 2027 ba.

Kara karanta wannan

Ndume ya dakata da sukar Tinubu, ya kwararo yabo ga shugaban kasa

Wannan na daga cikin abubuwa 12 da aka cimma a taron kwamitin zartarwa (NEC) na jam’iyyar da aka yi a Abuja.

Abure ya bayyana shakku kan tattaunawar kawance da ke faruwa, yana cewa wadanda ke jagoranta ba su da kwarewa kuma ba amintattu ba ne.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262