"Ka Rungumi Ƙaddara, Allah bai Rubuta Za Ka Mulki Najeriya ba," Hadimin Tinubu ga Atiku
- Daniel Bwala ya shawarci Atiku Abubakar ya hakura da neman mulki saboda alamu sun nuna ba zai shugabanci Najeriya ba a rayuwarsa
- Hadimin shugaban ƙasar ya ce Allah ke ba da mulki ga wanda ya so amma ga dukkan alamu Allah ba zai ba Atiku damar shugabancin kasar nan ba
- Ya buƙaci Atiku ya haɗa kai da shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu domin cika burinsa na inganta Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Mai ba wa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan sadarwa, Daniel Bwala ya shawarci Atiku Abubakar ya rungumi ƙaddara.
Bwala ya ce da yiwuwar babu mulkin Najeriya a kaddarar da Allah ya tsarawa tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar a rayuwarsa.

Source: Facebook
Hadimin Tinubu ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na TVC a ranar Litinin, 5 ga watan Mayu, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Daniel Bwala ya tattauna batutuwan da suka shafi mulki da kuma makomar siyasar ƴan adawa a ƙasar nan, kamar yadda The Cable ta tattaro.
Hadimin Tinubu ya ba Atiku shawara
Ya ce lokaci ya yi da Atiku zai rungumi kaddara, ya gane cewa da yiwuwar Allah bai tsara zai shugabanci Najeriya ba a rayuwarsa.
“Idan na samu damar ganinsa ido-da-ido, abin da zan faɗa masa shi ne: ‘Mai girma Alhaji Atiku Abubakar, ka yarda da kaddara."
“Allah ke ba da mulki ga wanda ya ga dama kuma duba da yadda abubuwa ke tafiya, alamu na nuna cewa shugabancin Najeriya ba ya cikin kaddararka.”
- Daniel Bwala.
Bwala ya bukaci Atiku ya haɗe da Tinubu
Ya shawarci Atiku da ya haɗa kai da gwamnatin Tinubu domin bada gudummawa wajen gina ƙasar, koda kuwa hakan zai tabbata ne ta hannun wani.
“Ina ganin akwai hanyoyi da dama da zaka iya bayar da gudummawa. Tun da ka kasance abokin Tinubu tsawon shekaru, ku haɗa kai ku cika burin da kuke da shi na kyautata Najeriya.
“Idan ka yarda da hakan, to za ka bar abin da za a tuna da kai a ƙarshen siyasarka, za ka cika wani ɓangare na burinka, ko da ta hannun abokinka ne.”

Source: Facebook
Matasa sun fara barin jikin Atiku
Amma ya ja hankalin Atiku da cewa, idan ya nace kan takarar shugaban ƙasa, to da yiwuwar ƙarshen siyaarsa ba za ta yi kyau ba.
“Yanzu haka, daga cikin mutanensa na siyasa, ya riga ya rasa kaso mai yawa, watakila kashi 60 zuwa 70 cikin 100, in ji shi.”
Bwala ya bayyana cewa matasan 'yan siyasa da suka yi wa Atiku aiki a baya, yanzu suna neman mulki da kansu kuma ba su da niyyar ja da baya.
Hakeem Baba-Ahmed ya shawarci Atiku
A wani labarin, kun ji cewa tsohon hadimin mataimakin shugaban ƙasa, Dr. Hakeem Baba-Ahmed ya buƙaci Atiku Abubakar ya haƙura da neman zama shugaban Najeriya.
A kwanakin baya ne Hakeem Baba Ahmed ya yi murabus daga kujerar mai ba mataimakin shugaban ƙasa shawara kan harkokin siyasa.
A cewarsa, ya kamata Atiku, wanda ya tsaya takara har sau shida a tarihi ya matsa gefe ya ba matasa dama, ya cire burin zama shugaban kasa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

