2027: Ana Zargin Shirin Kirkiro Sabuwar Jam'iyya Ya Firgita APC, An Taso INEC a Gaba
- Kungiyar TNN ta bayyana damuwa kan jinkirin da aka samu tun da ta miƙa bukatar yi mata rijista a matsayin jam'iyyar siyasa
- Mai magana da yawun TNN, Dr. Mohammed Adah Shaibu ya yi ikirarin cewa wasu ƴan APC ne suka hana a yi wa jam'iyyar rijista saboda fargaba
- Ya ce za su zuba ido su ga matakin da INEC za ta ɗauka kan lamarin domin ta haka za su gane ko hukumar zata iya shirya sahihin zaɓe a 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Kungiyar Team New Nigeria (TNN) ta bayyana damuwarta kan jinkirin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC) wajen yi mata rajista a matsayin jam’iyyar siyasa.
TNN ta yi zargin cewa wasu daga cikin masu riƙe da madafun iko ne suka matsa wa INEC lamba domin ka da ta amince da rijistar sabuwar jam'iyyar.

Source: Getty Images
Hakan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Dr. Mohammed Adah Shaibu, ya fitar, kamar yadda Leadership ta kawo.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce TNN ta mika bukatar yi mata rajista a matsayin sabuwar jam'iyyar siyasa da za ta goga kafaɗa da sauran jam'iyyu tun ranar 27 ga Mayu, 2024.
A cewar Dr. Mohammed, INEC ta tabbatar masu da cewa takardun neman rijistar sun isa hannunta, amma har yanzu ba a ba su amsa ba.
Ya bayyana takaicinsa kan yadda duk kokarinsu na tuntubar shugaban INEC, Farfesa Mahmoud Yakubu, ya ci tura, duk da cewar wa’adin kwanaki 90 da doka ta gindaya ya wuce.
An zargi ƴan APC da hana yi wa TNN rijista
Mohammed Shaibu ya zargi wasu ƴaƴan jam’iyyar APC da ke aiki a hukumar INEC da kokarin hana a yi wa TNN rajista
Ya ƙara da cewa ƴan APC sun matsa kada a yi wa TNN rijista ne saboda suna fargabar tasirin da jam’iyyar za ta yi wanda ka iya kawo masu cikas a zaben 2027.
“INEC na fuskantar matsin lamba daga wasu ‘yan APC da abokan huldarsu domin hana TNN samun rajista,” in ji shi.
TNN ta bukaci INEC da ta tsaya kan doka, ta guji nuna bangaranci domin ka da ta rasa yardar jama'a.

Source: UGC
Ƙungiyar TNN ta taso INEC a gaba
Ƙungiyar ta ce yadda hukumar zabe ta tafiyar da batun rajistar TNN zai tabbatar da ko za a iya dogaro da ita wajen gudanar da sahihin zabe a 2027.
A karshe, kungiyar ta bukaci magoya bayanta da su ci gaba da zama cikin lumana da bin doka da oda yayin da suke jiran hukuncin karshe daga INEC kan rajistar jam’iyyar.
INEC na shirin kawo sabon tsari a 2027
A wani labarin, kun ji cewa hukumar INEC ta fara shirin ba da damar kaɗa kuri'a ga waɗanda ba su da katin zaɓe watau PVC a zaben 2027.
Shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya fara tada wannan magana tun a watan Disamban 2024 a wani taron tattaunawa da kwamishinonin hukumar a Abuja.
Mahmud Yakubu ya ce duk da cewa katin PVC zai ci gaba da amfani ga waɗanda suka mallake shi, akwai yiwuwar masu zaɓe su iya amfani da takardun da INEC za ta ba su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

