"Mace mai Kamar Maza": Ƴar Takarar Mataimakiyar Gwamna a 2023 Ta Koma APC

"Mace mai Kamar Maza": Ƴar Takarar Mataimakiyar Gwamna a 2023 Ta Koma APC

  • Tsohuwar ƴar takarar mataimkiyar gwamnan jihar Kuros Riba a inuwar PDP, Dr Emana Ambrose-Amawhe ta sauya sheka zuwa APC
  • Ƴar siyasar ta tabbatar da komawa APC ne a wani taro da aka shirya a yankin ƙaramar hukumar Akpabuyo ranar Juma'ar da ta wuce
  • Drn Emana ta ce ba neman muƙami ya sa ta rungumi APC ba, sai dai tana son aiki tare da jam'iyya mai mulki don kawo wa al'umma ci gaba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Cross River - Tsohuwar ‘yar takarar mataimakiyar gwamnan jihar Kuros Riba a inuwar PDP a zaben 2023, Dr Emana Ambrose-Amawhe, ta sauya sheƙa zuwa jam'iyar APC.

Tsohuwar ƴan takarar, mace mai kamar maza ta tabbatar da komawa APC ne a taron da aka shirya a Edem Odo da ke ƙaramar hukumar Akpabuyo ranar Juma'a.

Kara karanta wannan

Buhari da tsofaffin ministoci na shirin ficewa daga APC kafin 2027? Gwamna Sule ya yi magana

Dr Emana Ambrose-Amawhe.
APC ta samu karuwa a jihar Cross River Hoto: Barrister Alphonsus Ogar Eba
Source: Facebook

Dr. Emana ta bayyana cewa ci gaban da APC ke samu a jihar da kuma matakin tarayya ne ya sa ta yanke shawarar komawa jam’iyyar, kamar yadda Punch ta kawo.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya ja hankalin ƴar takarar zuwa APC?

A kalamanta, toshuwar ƴan takarar ta ce:

“Na yanke shawarar komawa APC ne bayan ganin ayyukan alheri da gwamnan Kuros Riba, Sanata Bassey Otu, ke yi.
"Idan mutum bai gani ba, to zai ji. Ayyuka sun bayyana a fili kowa na gani, kuma na ji daɗin kasancewa cikin iyalin APC.
"Ni ce tsohuwar ‘yar takarar mataimakiyar gwamna ta PDP, kuma ‘ya ce ta yankin Kudancin Kuros Riba."

Game da halin ƙuncin da ake ciki a ƙasa karƙashin mulkin APC, ƴar siyasar ta buƙaci jama'a su kara haƙuri domin babu wani abu mai kyau da ake samunshi a dare ɗaya.

Tsohuwar ƴan takarar PDP ta ba jama'a haƙuri

A ruwayar Leadership, Dr. Emana ta ce:

Kara karanta wannan

'SDP za ta wawushe manyan 'yan siyasa,' El-Rufa'i ya yiwa jam'iyyarsa albishir

“Wasu na cewa abubuwa sun yi tsanani, amma ku sani babu wani abu mai kyau da ke zuwa a dare ɗaya. Shugaban ƙasa ya sanya mutanen da suka dace a wuraren da suka dace. A hankali komai zai wanye."
“Ba yunwa ko son mukami ne ya sa na sauya sheka ba. Ina son aiki tare da waɗanda ke kan mulki domin kawo ci gaba."
Jam'iyyar APC.
Tsohon ƴan takara a inuwar PDP ta koma APC a Kuros Riba Hoto: @OfficialAPCNig
Source: UGC

APC ta karbi ƴar siyasar hannu biyu

A nasa jawabin, sakataren APC na jihar Cross River, Patrick Asikpo, ya gargadi sababbin ‘yan jam’iyyar da su kasance masu kishin ci gaba ba masu kawo rarrabuwar kai ba.

“Daga yau, duk wani haƙƙi da ‘yancin da ‘ya APC ke da shi, ku ma kuna da su. Babu tsohuwar APC ko sabuwar APC. Dukkan ku ‘ya’yan jam’iyya ne daga yau.”

Gwamnan Osun na shirin fita daga PDP?

A wani labarin, kun ji cewa Ademola Adeleke na jihar Osun ya tabbatarwa masu ruwa da tsakin PDP cewa ba zai bar jam'iyyar, ya koma APC ba.

Gwamna Adeleke ya tabbatarwa dukkan masu ruwa da tsaki da shugabannin jam'iyyar cewa yana nan daram a PDP, ba zai jr ko'ina ba.

Wannan dai na zuwa ne yayin da ake raɗe-raɗin Adeleke na duba yiwuwar komawa APC domin cika burinsa na yin tazarce a zaɓen Osun na 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262