Ana Raɗe Raɗin Gwamna Zai Koma APC, Ƴan Majalisa 2 Sun Sauya Sheƙa zuwa PDP
- Jam'iyyar PDP ta ƙara samun ƙaruwa a jihar Enugu ƙasa da awanni 24 bayan ɗan Majalisar Tarayya, Hon. Dennis Agbo ya fice daga LP
- Wasu ƴan majalisa biyu, Hon. Mark Chidi Obetta da Hon. Malachi Okey Onyechi sun sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP mai mulkin jihar
- Shugaban PDP ya karɓe su hannu bibbiyu, inda aka ji yana cewa akwai ƙarin jiga-jigan siyasa da za su rungumi laima nan ba da jimawa ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Enugu - Kasa da awanni 24 bayan Hon. Dennis Agbo, ɗan majalisar wakilai, ya fice daga jam’iyyar LP zuwa PDP, wasu ‘yan majalisa biyu sun bi sahunsa.
Waɗanda suka koma PDP sun haɗa da mamba mai wakiltar mazaɓar Nsuƙka/Igbo-Eze ta Kudu a Majalisar Wakilan Tarayya, Hon. Mark Chidi Obetta.

Source: Facebook
Sai kuma Hon. Malachi Okey Onyechi, ɗan majalisar dokokin jihar Enugu mai wakiltar Nsukka ta Yamma, kamar yadda Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
PDP ta karbi ƴan Majalisa 3 a hukumance
Jaridar Leadership ta tattaro cewa an karɓi ‘yan majalisar guda uku a hukumance a hedkwatar PDP da ke Unguwar GRA a jihar Enugu.
Ficewarsu ta biyo bayan sauya sheƙar ɗan takarar gwamna na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Barista Chijioke Edeoga, wanda ya tattara ya koma PDP.
Edeoga ya yabawa Gwamna Peter Mbah bisa ɗumbin ayyukan ci gaba da yake gudanarwa tare da alƙawarin tallafa wa PDP a jihar.
Yadda jiga-jigan siyasa ke shiga PDP
Tun farko jagora a kwamitin yakin neman zaɓen shugaban ƙasa na LP a Jihar Enugu a 2023, Prince Emeka Mamah, ya sauya sheƙa zuwa PDP.
Mamah ya bayyana cewa kyakkyawan shugabancin Gwamna Mbah ne ya ja shi zuwa jam’iyyar PDP mai mulki a Enugu.
Haka kuma, tsohon sakataren yaɗa labarai na jam’iyyar LP a jihar da kuma ɗan takarar kujerar shugaban ƙaramar hukumar Igboeze ta Arewa, Barista Titus Odo, ya bi sahunsu zuwa PDP.
PDP ta ce duk aikin Gwamna Mbah ne
Da yake maraba da sababbin masu sauya shekar, shugaban PDP a Enugu, Dr. Martin Chukwuweike, ya yi ikirarin cewa jam'iyyun adawa a Enugu na rushewa a hankali a hankali.
Ya ce ayyukan alherin da Gwamna Mbah ke zuba wa al'umma ya sa PDP ta ƙara ƙarfi, yayin da manyan jam'iyyun adawa, APC da LP suka kama hanyar mutuwa a jihar.

Source: Twitter
Chukwuweike ya ƙara da cewa PDP za ta ci gaba da karɓar ‘yan siyasa masu ƙima daga sauran jam’iyyu, yana mai cewa wasu ƙarin jiga-jigai na dab da shigowa jam'iyyar.
“Ina jin daɗin yadda abubuwa ke tafiya daidai da yadda gwamnanmu ke so. Shi ne ya tsara komai, mu namu aiwatarwa," in ji shi.
Tsohon shugaban APC ya bar jam'iyyar
A wani labarin, kun ji cewa tsohon shugaban APC reshen jihar Enugu, Dr. Ben Nwoye ya yi murabus daga matsayin da mamban jam'iyyar.
Dr. Nwoye ya bayyaja cewa ya yanke shawarar ficewa daga APC ne bayan ya tattauna da magoya baya da abokanansa na siyasa.
Ya kuma soki shugabannin APC na shiyyar Kudu maso Yammacin Najeriya, yana mai cewa ga su da burin kara faɗaɗa jam'iyyar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

