Obi, Okowa da Mutanen da Atiku Ya Jawo Jiki, amma Suka Fice daga PDP Suka bar Shi

Obi, Okowa da Mutanen da Atiku Ya Jawo Jiki, amma Suka Fice daga PDP Suka bar Shi

Bayan kammala zaben shugaban kasa na 2023, siyasar jam’iyyar PDP ta fuskanci sauye-sauye da rikice-rikice da dama, ko da yake, an fara samun wasu na barin Atiku kafin zaben.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Daga ciki akwai sauya sheka da wasu daga cikin makusantan tsohon dan takarar shugaban kasar PDP, Atiku Abubakar suka yi.

Wasu daga cikin wadannan mutane sun taka muhimmiyar rawa wajen yakin neman zaben Atiku ko kuma suna cikin amintattun da suka tsaya masa a baya.

Peter
Wasu amintattun Atiku Abubakar sun sauya tafiyar siyasa Hoto: Mr. Peter Obi/Dr Ifeanyi Arthur Okowa
Source: Facebook

Ga jerin sunayen wasu daga cikin makusantan Atiku Abubakar da suka bar PDP bayan ganin nasarar jam'iyyar PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Tsohon abokin takarar Atiku ya bar PDP

Ifeanyi Arthur Okowa, tsohon gwamnan Delta kuma abokin takarar Atiku Abubakar a zaben 2023 ya ba kowa mamaki bayan ya bayyana sauya sheka zuwa jam'iyya a mulki a kwanan nan.

Kara karanta wannan

'Miyarsa yake gyarawa,' Wike ya soki masoyin Atiku kan neman maido mulki Arewa

Okowa, wanda Atiku Abubakar ya zabi ya yi tafiya da shi a maimakon Nyesom Wike ya ajiye jam'iyyar PDP ne tare da daukacin gwamnatin jiharsa ta Delta.

An samu rahotanni masu karo da juna bayan ficewarsa daga PDP, inda da farko aka ruwaito yana mai nadama da tsayawa takara da Atiku, amma daga baya, ya musanta fadin haka.

2. Daniel Bwala ya bar tafiyar Atiku

The Cable ta wallafa cewa Daniel Bwala, wanda ya kasance kakakin yakin neman zaben Atiku a shekarar 2023, ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma APC a watan Yuli 2024.

Bayan ganawa da shugaban kasa Bola Tinubu a fadar shugaban kasa, ya bayyana cewa yanzu yana da cikakken biyayya ga Tinubu da jam’iyyar APC.

Daniel Bwala
Bwala ya bar tafiyar Atiku ya koma ta Tinubu Hoto: Daniel Bwala
Source: Twitter

Ya kuma wanke kansa daga zargin zazzafar adawa da ya yi da shugaban kasa da jam'iyyarsa ta APC a baya, inda ya ce dama haka adawa ta gada.

Bayan komawarsa APC mai mulki, gwamnatin Bola Tinubu ta nada shi a matsayin mashawarcin shugaban kasa a kan harkokin yada labarai.

3. Yadda Gbenga Daniel ya rabu da Atiku

Kara karanta wannan

'Gari ya yi zafi,' Tsohon Sanata ya fadi halin da ake ciki bayan barin majalisa

Tsohon gwamnan jihar Ogun da kuma daraktan yakin neman zaben Atiku a 2019, Gbenga Daniel, ya koma APC tun a watan Fabrairun 2021.

Ko da yake hakan ya faru kafin zaben 2023, hakan ya nuna cewa ya dade yana samun tayin cewa ya dace ya koma jam'iyya mai mulki ta APC.

A sanarar da ya fitar, Daniel ya ba PDP da sauran makusantansa hakurin sanar da su aniyarsa ta ficewa daga PDP a kurarren lokaci.

4. Peter Obi ya bar tafiyar Atiku

Jaridar Punch News ta wallafa cewa tsohon mataimakin dan takarar Atiku a zaben 2019, Peter Obi, ya fice daga PDP a watan Mayu 2022 ya koma jam’iyyar LP.

Obi ya tsaya takarar shugaban kasa a karkashin LP a zaben 2023, lamarin da ya nuna ya yanke dangantaka da tafiyar Atiku baki daya.

Har yanzu, ana ganin Peter Obi na kai ziyara ga Wazirin Adamawa, yayin da ake sa ran tafiyar hadakar jam'iyyu da shi.

An gano matsalar da Atiku ya samu a 2023

A baya, mun wallafa cewa Sanata mai wakiltar mazabar Binuwai ta Kudu a majalisar dattawa, Abba Moro, ya bayyana cewa PDP na da damar lashe zaben shugaban kasa na 2023.

Kara karanta wannan

An gano kuskuren da ya jawo Atiku Abubakar ya fadi zaben 2023 a PDP

A cewarsa, babban kuskuren da jam’iyyar PDP ta yi shi ne zaben tsohon gwamnan jihar Delta, Ifeanyi Okowa, a matsayin mataimakin dan takarar shugaban kasa ga Atiku Abubakar.

Sanata Moro ya bayyana haka ne awanni bayan an samu rahotannin cewa Ifeanyi Okowa da kansa ya fito ya bayyana nadamarsa na yin tafiya da Atiku Abubakar a zaben 2023.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng