'Miyarsa Yake Gyarawa,' Wike Ya Soki Masoyin Atiku kan Neman Maido Mulki Arewa

'Miyarsa Yake Gyarawa,' Wike Ya Soki Masoyin Atiku kan Neman Maido Mulki Arewa

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya bayyana cewa Dele Momodu yana goyon bayan Atiku Abubakar ne saboda kudin da yake samu daga gare shi
  • Hadimin Eike, Lere Olayinka ne ya fadi haka a matsayin martani ga kalaman mawallafin mujallar Ovation, Momodu na goyon bayan Atiku
  • Olayinka ya kuma karyata zargin da Dele Momodu ya yi na cewa Wike ne ya tilasta Peter Obi barin PDP, yana cewa Atiku ne matsalar PDP

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya zargi mawallafin mujallar Ovation, Dele Momodu, da mara wa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, baya ne saboda kudi.

Wannan na kunshe a cikin sanarwar da mai taimaka wa ministan na musamman kan harkokin sadarwa da kafafen sada zumunta, Lere Olayinka, ya fitar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

An gano kuskuren da ya jawo Atiku Abubakar ya fadi zaben 2023 a PDP

Atiku
Wike ya zargi Atiku da raba PDP Hoto: Nyesom Ezenwo Wike/Atiku Abubakar
Source: Facebook

Jaridar Punch ta wallafa cewa hadimin Wike ya kara da bayyana cewa Momodu na nuna kauna ga Atiku Abubakar ne saboda abin da ya ke samu a wajen tsohon dan takarar PDP.

Nyesom Wike ya caccaki Dole Momodu

Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa Olayinka ya kara da cewa Dele Momodu zai ajiye biyayyar da yake yiwa Atiku matukar kudi suka daina shiga aljihunsa.

Ya ce:

“Duka wannan hayaniya daga gare shi saboda Atiku ne ke ba shi kudin kashewa. Idan Atiku ya daina ba shi kudin, Oga Dele Momodu zai nemi inda zai fake.”

Da yake mayar da martani kan ikirarin da Momodu ya yi kwanan nan cewa Wike ne ya jawo Peter Obi, ya fice daga PDP, Olayinka ya ce wannan zargin ba shi da tushe balle makama.

Ya kara da cewa:

“Sai irin mutumin da baya da ilimi face wanda zai cika cikinsa, kamar Dele Momodu, ne zai ce wai Wike ne ya kore Peter Obi daga PDP.”

Kara karanta wannan

El-Rufa'i ya gano wanda ya fi dacewa ya mulki Najeriya a 2027

Nyesom Wike ya soki Atiku Abubakar

Hadimin Wike, Olayinka ya zargi Atiku da kasancewa mutumin da ke haddasa rabuwar kawuna a cikin PDP tun shekarar 2003.

Ya ce:

“Atiku ne makamin da aka dade ana amfani da shi wajen karya PDP tun lokacin da ya hana jam’iyyar cin zabe a jihar Legas a 2003.”
“Dele Momodu ya ce Atiku na son PDP ta tsayar da dan takara daga Kudu maso Gabas, amma ya yi shiru kan gaskiyar cewa Atiku tuni ya riga ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takara."
Dele Momodu
Kalaman masoyin Atiku sun fusata Nyesom Wike Hoto: Dele Momodu
Source: Facebook

Olayinka Lere ya ambaci ficewar wasu manyan jam’iyyar PDP, ciki har da tsohon daraktan yakin neman zaben Atiku a 2019, Gbenga Daniel, da kuma abokin takararsa a 2023, Dr. Ifeanyi Okowa.

Ya kara da cewa wannan na nuna rashin gamsuwa da salon jagorancin Atiku Abubakar da kuma tarin matsaloli da ya jawo wa PDP.

An gano gaskiya kan komawar Atiku APC

A wani labarin, mun wallafa cewa jigo a PDP, Dele Momodu, ya soki matakin tsohon gwamnan Delta kuma abokin takarar Atiku Abubakar, Ifeanyi Okowa, na sauya sheka zuwa APC.

Kara karanta wannan

Canza Naira: Kotu ta yanke hukunci a kan tuhumar da ake yiwa Buhari da Emefiele

Dele Momodu ya bayyana cewa hakan wani yunkuri ne na son kai, inda ya karyata ikirarin Okowa na cewa tsohon dan takarar shugaban kasa, Atiku zai sauya sheka zuwa APC.

Momodu ya ce Okowa ya rike mukamai da dama a PDP, ciki har da gwamna, Sanata, da sakataren gwamnati, kuma an ba shi damar zama mataimakin dan takarar shugaban kasa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng