Daga Shiga APC, Gwamna Ya Fadi Yawan Kuri'un da Zai Iya ba Tinubu a Zaben 2027

Daga Shiga APC, Gwamna Ya Fadi Yawan Kuri'un da Zai Iya ba Tinubu a Zaben 2027

  • Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa APC tare da alkawarin kawowa Bola Tinubu kuri'u
  • Oborevwori da mataimakinsa Monday Onyeme da tsohon gwamna Ifeanyi Okowa da sauran jiga-jigan PDP sun koma APC a jihar Delta gaba ɗaya
  • Sanarwar ta ce sauyin zai ƙarfafa APC a yankin Kudu maso Kudu, amma masana suna ganin samun kuri'un da gwamnan ke fata zai yi wahala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Asaba, Delta - Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya yi alkawarin samar wa Shugaba Bola Tinubu miliyoyin kuri'u a 2027.

Gwamna Oborevwori ya ce zai samar wa Bola Tinubu kuri'u miliyan 1.4 a zaben shugaban kasa da za a yi a shekarar 2027.

Gwamna ya sha alwashin kawo wa Tinubu jiharsa a 2027
Gwamna Sheriff Oborevwori ya ce zai ba Tinubu miliyoyin kuri'u a 2027. Hoto: Rt. Hon. Sheriff Oborevwori, Asiwaju Bola Tinubu.
Source: Facebook

APC ta kara ƙarfi a Kudu maso Kudu

Mista Oborevwori ya yi wannan alkawari ne a lokacin da ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC daga jam’iyyar PDP a hukumance, cewar Premium Times.

Kara karanta wannan

Da gaske gwamnonin APC 5 za su koma tafiyar Atiku? Gwamna Buni ya yi magana

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamnan ya koma APC tare da mataimakinsa Monday Onyeme, da tsohon gwamna kuma ɗan takarar mataimakin shugaban kasa na PDP 2023, Ifeanyi Okowa.

Sanarwar ofishin gwamnan ta bayyana cewa sauyin zai canza sa’ar APC a Kudu maso Kudu, inda suka bayyana wannan a matsayin ci gaba.

A cewar sanarwar:

“Tare da Oborevwori a APC yanzu, taswirar siyasar Kudu maso Kudu ta ƙara matsewa kuma hakan zai ƙara wa Tinubu dama.”
Gwamna ya yi wa Tinubu alƙawarin miliyoyin kuri'u
Gwamna Sheriff Oborevwori ya sha alwashin ba Tinubu kuri'u a zaben 2027. Hoto: Rt. Hon. Sheriff Oborevwori.
Source: Facebook

Aikin da ke gaban gwamnan a 2027

Sai dai masu lura da harkokin siyasa sun ce burin Mista Oborevwori yana da wahala saboda adadin kuri'u da zai samar da kuma dabi'ar kada kuri'a.

A zaben 2023, jihar Delta ta yi rajistar mutane 3,227,697 masu kada kuri'a, inda 2,989,514 suka karɓi katin zabe na dindindin.

Sai dai an kada kuri’u 615,341 kacal a zaben shugaban kasa, wanda ke wakiltar kaso 19 cikin dari na masu rijista.

Ko da yake Oborevwori ya lashe zaben gwamna da kashi 57 cikin dari, PDP ta samu kashi 26 cikin dari a zaben shugaban kasa a jihar.

Kara karanta wannan

"Za ta fashe": Kusa a PDP ya yi haashen hatsarin da ke tunkaro APC

Kokarin APC a zaben 2023 a Delta

APC ta samu kashi 15 cikin dari kacal, yayin da Peter Obi na jam’iyyar LP ya kada su da kashi 56 cikin dari.

Ko da haɗakar PDP da APC na iya taimakawa Oborevwori a burinsa, sakamakon 2023 yana nuna cewa hakan ba zai zama mai sauƙi ba.

Jam’iyyar APC ta sha kashi a yankin Kudu maso Kudu baki ɗaya a 2023, inda ta samu kashi 28 cikin dari na kuri'un yankin.

Masu lura da harkoki sun bayyana cewa Mista Oborevwori da abokansa suna da babban aiki a gabansu don cika alkawarin da suka ɗauka.

Hadimin gwamnan Delta ya yi murabus

Kun ji cewa Gwamnatin Delta ta fuskanci koma baya, Harrison Gwamnishu, mai ba gwamna shawara kan matasa da kungiyoyin farar hula, ya ajiye aikinsa.

Gwamnishu ya bayyana a wasikar murabus dinsa cewa duk kokarinsa na shawo kan Gwamna Oborevwori game da matsalar tsaro da ya ci tura.

A cewarsa, rashin yanke shawara mai ma’ana daga gwamnati ya sa ya kasa ci gaba da aiki da amana da nagarta kamar yadda ya yi alkawari.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.