Uba Sani Ya Yi Maganar Komawar El Rufa'i SDP da Hadakar Kifar da Tinubu a 2027

Uba Sani Ya Yi Maganar Komawar El Rufa'i SDP da Hadakar Kifar da Tinubu a 2027

  • Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya ce ‘yan Najeriya sun san bambanci tsakanin masu sukar gwamnati a kan gaskiya da masu neman mulki kawai
  • Uba Sani ya bayyana cewa gwamnatinsa ta fifita ci gaba da adalci fiye da fifita ‘yan jam’iyya tun bayan hawan shi kujerar gwamnan jihar Kaduna
  • Gwamnan ya ce hadakar da 'yan adawa suke kokarin yi domin kawar da gwamnatin APC da Bola Tinubu ba za ta tayar masa da hankali ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna - Uba Sani, ya ce yawancin masu sukar gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ba wai su na yi ne domin ci gaban kasa ba, illa kawai su na neman samun mulki ne.

Ya ce fitowa daga sahun gwagwarmayar kare hakkin dan Adam ya sanya shi fahimtar siyasar Najeriya sosai, kuma ‘yan Najeriya yanzu ba su yarda da maganar marasa gaskiya.

Kara karanta wannan

"Ba mu buƙatar albarkar shi kafin fatattakar Tinubu," Tsohon Sakataren gwamnatin Buhari

Uba Sani
Uba Sani ya ce hadakar 'yan adawa ba za ta yi tasiri ba. Hoto: Kaduna State Government
Source: Twitter

Gwamnan jihar Kaduna ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi a wani shiri na musamman na Trust TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Uba Sani ya ce yana adalci a Kaduna

Uba Sani ya bayyana cewa, tun daga lokacin da ya hau kan mulki, ya dauki alkawarin yin aiki da kowa a fadin Kaduna, ba wai kawai wadanda suka zabe shi ba.

Ya ce ya tabbatar wa mutanen Kudancin Kaduna – wadanda yawanci suka fi kada kuri’a ga PDP – cewa su ma za su ci gajiyar mulkinsa.

Uba Sani ya ce:

"A baya, wasu gwamnoni sukan fifita yankin da ya zabe su, amma ni na ce za mu raba ayyuka da albarkatu daidai a fadin jihar."

A cewarsa, hakan ne ma ya sa wasu ‘yan majalisar wakilai daga PDP suka koma APC domin goyon bayan manufarsa ta hadin kai da adalci.

Ya ce yana kallon mulki a matsayin nauyi ne da zai yi wa Allah bayanin yadda ya tafiyar da shi, kuma saboda haka yana aiki da kowa da kowa daidai, komai banbancin siyasa ko ra’ayi.

Kara karanta wannan

Lokaci ya yi: Hadimar Gwamna Sheriff ta riga mu gidan gaskiya, an fara zargin mijinta

Maganar hadaka da komawar El-Rufa'i SDP

Game da hadin kan 'yan adawa don kalubalantar APC a 2027, Uba Sani ya ce irin hadin kan galibi ba ya haifar da da mai ido.

Gwamnan ya ce:

"Idan hadin gwiwa ne don gyara Najeriya, to zan damu. Amma ban damu ba saboda ana kokarin haduwa ne domin karbe mulki ba tare da manufa ba."

Gwamnan ya ce bai damu da sauyin jam’iyya da tsohon gwamna Nasir El-Rufai ya yi ba daga APC zuwa SDP, domin a cewarsa:

“SDP ba ta da tasiri a siyasar Kaduna.”

Ya kara da cewa, a matsayin shi na dan gwagwarmaya a lokacin mulkin soja, ya san lokacin da gwagwarmaya ke da ma’ana da kuma lokacin da ake amfani da ita don son zuciya.

Ya ce gwamnatin Tinubu ta fi yawancin gwamnatocin baya sassauci kuma tana bai wa kowa damar bayyana ra’ayi.

Uba Sani
Uba Sani ya ce bai damu da hadakar 'yan adawa ba. Hoto: Nasir El-Rufa'i|Bayo Onanuga
Source: Facebook

Cin zarafi: Gwamnatin Kaduna ta kama mahaifi

Kara karanta wannan

"Za a kara dagula rashin tsaro," Gwamnan Jigawa ya soki shawarar Janar TY Danjuma

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnatin jihar Kaduna ta kama wani mahaifi kan zargin cin zarafin dansa.

Rahotanni sun nuna cewa gwamnatin jihar ta ce za a yi bincike a kan mahaifin yaron da kishiyar mamar shi domin daukar mataki.

Ana zargin mahaifin da kishiyar mahaifiyar yaron da yi masa horo a kan satar biskit wanda hakan ya jawo yanke mi shi kafafu a asibiti.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng