Abin da Shettima Ya Fadi ga Abba Kabir yayin Ta'aziyya kan Bambancin Siyasa a Kano

Abin da Shettima Ya Fadi ga Abba Kabir yayin Ta'aziyya kan Bambancin Siyasa a Kano

  • Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya roƙi a zauna lafiya a Kano tare da janye bambance-bambancen siyasa da ke kawo rabuwar kai
  • Shettima ya yi wannan kira ne yayin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi da ya rasu
  • A cewar wata sanarwa daga Kakakin Gwamnan Kano, Mustapha Muhammad, Shettima ya bukaci 'yan siyasa su guji barin siyasa ta raba su
  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya godewa Shettima da ziyarar, inda wakilin iyalan marigayin ya roki Allah ya kawo hadin kai a Kano

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Kano - Mataimakin Shugaban Najeriya, Kashim Shettima, ya ziyarci jihar Kano domin ta'aziyya kan rashin da aka yi.

Yayin ziyarar rasuwar Galadiman Kano, Kashim ya roƙi a zauna lafiya a Kano tare da janye bambancin siyasa da ke kawo rashin jituwa.

Kara karanta wannan

Matasa sun yi babban rashi, an sanar da rasuwar hadimin Gwamna Abba a Kano

Kashim ya shawarci Abba Kabir kan siyasa a Kano
Kashim Shettima ya bukaci hadin kai da watsi da bambancin siyasa a Kano. Hoto: Kashim Shettima.
Source: Twitter

Wannan na cikin wata sanarwa da sakataren yada labarai na Gwamnan Kano, Mustapha Muhammad ya fitar wanda Abdullahi Ibrahim ya wallafa a X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Galadiman Kano ya yi bankwana da duniya

Hakan ya biyo bayan sanar da rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi wanda ya rasu ya na da shekaru 92 a duniya.

Masarautar Kano ta bayyana cewa ya rasu ne a daren Talata 1 ga Afrilu, 2025, bayan wata jinya mai tsawo.

An yi jana’izarsa a Fadar Sarkin Kano da ke Kofar Kudu da misalin karfe 10:00 na safe a washegarin Laraba.

Shettima ya shawarci ƴan siyasa a Kano

Shettima ya yi wannan kira ne lokacin ziyarar ta’aziyya ga iyalan marigayi Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, wanda ya rasu makonni biyu da suka gabata.

Shettima ya ce:

“Don Allah ka da ku bari siyasa ta raba ku, ya kamata ku kasance masu hadin kai.

Kara karanta wannan

2027: El Rufa'i, Al Mustapha sun karbi Sanata Ubale Shitu zuwa SDP a Abuja

“Kano zuciyar Arewa ce, kuma ni ma daga Arewa nake, ina addu’ar cewa, Allah ya kawo hadin kai a tsakaninku."
Abba Kabir ya yabawa Shettima bayan ziyara zuwa Kano
Kashim Shettima ya shawarci ƴan siyasa a Kano kan hada kansu. Hoto: Kashim Shettima, Abba Kabir Yusuf.
Source: Facebook

Abba Kabir ya yi godiya ga Shettima

A jawabinsa na maraba, Gwamna Abba Kabir Yusuf ya godewa Mataimakin Shugaban Kasa a madadin gwamnatin da al’ummar Jihar Kano baki ɗaya.

Ya ce:

“Muna godiya matuƙa da ka zo ka tausaya mana kan rasuwar uba, kaka, Muna rokon Allah Madaukaki ya mayar da kai gida lafiya."

Wakilin iyalan marigayi Galadiman Kano, Alhaji Sunusi Abbas, ya nuna godiya ga Mataimakin Shugaban Kasa bisa ziyarar ta’aziyya tare da addu’ar samun haɗin kai a Kano.

A cewarsa:

“Muna ci gaba da addu’a, Allah ya sa mutuwar Galadiman Kano ta zama hanyar haɗin kan ‘yan siyasar Kano."

APC ta gindaya sharuda ga Kwankwaso

Kun ji cewa jam’iyyar APC mai adawa a Kano ta bukaci Rabiu Musa Kwankwaso ya nemi gafara daga Bola Tinubu da Kashim Shettima kafin ya samu shiga.

Abbas ya ce suna maraba da Kwankwaso da sauran masu sauya sheka, amma sai sun bi wasu sharudda.

Shugaban APC ya ce jam'iyyar ba za ta karɓi duk wanda ya zagi shugabanninta ba tare da ya ba da hakuri a fili ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.