Gwamna Dauda Ya Shiga Matsala, Ana So Tinubu Ya Ayyana Dokar Ta Baci a Zamfara
- Wata ƙungiyar Arewa ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a jihar Zamfara saboda tabarbarewar tsaro
- Kungiyar CAJ ta zargi gwamnatin Zamfara da yin salon mulkin 'kama karya' yayin da ta ce jihar ba ta samun wani ci gaba a yanzu
- NCAJ ta ce garuruwa sun koma biyan haraji ga ‘yan bindiga, jami’an gwamnatin jihar na amfana da haramtacciyar hakar ma’adinai
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kaduna - Wata ƙungiyar kare haƙƙin bil’adama a Arewa (NCAJ), ta bukaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a Zamfara.
Kungiyar ta ce ayyana dokar ta bacin ya zama dole saboda tabarbarewar tsaro, rushewar dimokuraɗiyya, da zargin haɗin kai tsakanin jami’an gwamnati da masu hakar ma’adinai.

Asali: Twitter
Kungiyar NCAJ ce ta bayyana hakan cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Juma’a, 11 ga Afrilu, a Kaduna, kamar yadda jaridar Punch ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kungiya ta zayyano rikice-rikicen Zamfara
Ta bayyana cewa halin da jihar Zamfara ke ciki ya wuce yadda za a warware ta ta siyasa, yayin da kungiyar ke zargin gwamnatin jihar da ƙarfafa take doka.
“Abin da ke faruwa a Zamfara ba mulki ba ne. Gwamnatin ta sauka daga turbarta na shugabanci,” in ji shugaban ƙungiyar, Malam Kabiru Sani Bako.
Mallam Bako ya bayyana cewa Zamfara ta rasa damarmaki da dama saboda majalisar jihar ba ta aiki yadda ya kamata, tun bayan dakatar da wasu 'yan majalisa 10.
Ya yi ikirarin cewa an dakatar da 'yan majalisar ne saboda sun soki gwamnati kan yadda take tafiyar da batun tsaro, yana mai fargabar cewa nan gaba jihar na iya fadawa cikin mulkin kama-karya.
“Babu wata siyasa da za ta iya kawo karshen tashin hankalin da ke faruwa a Zamfara. Abin da ke faruwa cin amana ne, ba wai siyasa ba,” in ji Bako.
Zamfara: Ana tilasta wa mutane biyan haraji
A cewar ƙungiyar, mazauna yankuna irin su Zurmi, Anka, Shinkafi, da Bukkuyum na biyan haraji ga ‘yan bindiga domin su samu damar noma ko yin tafiye-tafiye.
Jaridar The Guardian ta rahoto kungiyar ta bayyana Zamfara a matsayin “jihar da ke dulmiye wa a cikin tabon ta'addanci ba tare da kasar ta damu ba."
Mallam Bako ya kara da cewa:
“Ana sace mata, ana daukar yara ana shigar da su kungiyoyin ta'addanci, garuruwa na biyan haraji ga 'yan ta'adda yayin da jami’an gwamnati ke wuce gona da iri."
Har ila yau, ƙungiyar ta zargi wasu jami’an jihar da kare masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, tana mai cewa ribar da suke samu daga hakar ma'adanan na ƙarfafa ayyukan ‘yan ta’adda.
Mallam Bako ya yi ikirarin cewa wadanda ya kamata a ce su ne ke kare Zamfara, yanzu su ne suka koma suna cin dunduniyarta.
Ana so Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Zamfara

Asali: Twitter
NCAJ ta bukaci Shugaba Tinubu da ya kai dauki Zamfara cikin gaggawa ta hanyar ayyana dokar ta-baci da kuma nada wani shugaban riko da ba ya da hannu a rikicin jihar.
“Ba lokaci ba ne na dogon jawabi. Idan ba a ɗauki mataki nan take ba, Zamfara za ta koma sansanin ta’addanci na dindindin,” inji sanarwar.
Ƙungiyar ta ce tana shirin mika rahoto na musamman ga majalisar tarayya da kuma mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro don ganin korafinsu ya karbu.
Ana so Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Osun
A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon ministan ‘yan sanda, Oyewale Adesiyan, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a jihar Osun kan matsalar tsaro da rikicin siyasa.
Adesiyan ya zargi Gwamna Ademola Adeleke da kin mutunta umarnin kotu, yana mai cewa hakan ne ya jawo rikicin kananan hukumomi da kuma asarar rayuka.
Ya kuma bukaci a yi amfani da sashe na 305 na kundin tsarin mulki domin tabbatar da doka da oda da kuma dawo da zaman lafiya a fadin jihar Osun.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng