Akpabio Ya Fadi Abin da Ya Sani kan Yunkurin Hallaka Sanata Natasha
- Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya zargi Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan da shirga masa ƙarya domin ta ɓata masa suna
- Ya ce zargin da Natasha ta yi na cewa ya bada umarnin a kashe ta, ya yi masa mummunar illa, don haka zai nemi hakkinsa ta hanyar shari'a
- Shugaban majalisar ya shigar da ƙara zuwa ofishin Sufeto Janar na ‘Yan sanda, Kayode Egbetokun, domin a ɗauki matakin a kan Natasha
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja –Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya kai ƙara ga Sufeto janar na ‘yan sanda, Kayode Egbetokun kan zargin kisan gilla da Natasha Akpoti-Uduaghan ta yi masa.
A ranar 1 ga Afrilu da Natasha ta ziyarci garinta ne ta zargi Akpabio da haɗa baki da gwamnan jihar Kogi na yanzu, Usman Ododo, da tsohon gwamna, Yahaya Bello, domin a kashe ta.

Asali: Facebook
Daily Trust ta ruwaito cewa Natasha, yayin da take jawabi ga magoya bayanta a gaban gidanta da ke Kogi, ta ce an tsara yadda za a kashe ta, sannan a ɗora laifin hakan kan mutanen mazabar da take wakilta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Akpabio ya karyata zargin yunkurin hallaka Natasha
Jaridar Punch tawallafa cewa ta cikin takardar ƙarar da aka rubuta a ranar 3 ga Afrilu, Sanata Akpabio ya musanta zargin da Natasha ke masa.
Ya kuma buƙaci rundunar ‘yan sanda ta gudanar da bincike tare da gurfanar da ita gaban kotu bisa zargin ɓata masa suna ta hanyar yaɗa ƙarya.
Sanata Akpabio ya ce:
"Na rubuto ne domin sanar da ku wannan batu cikin gaggawa, tare da neman a gudanar da bincike da gurfanar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, wacce aka dakatar daga Majalisar dattawa, kan zargin da ta yi min a ranar 1 ga Afrilu, 2025. Wannan zargi an yaɗa shi sosai a gidajen rediyo, talabijin, jaridu da kuma shafukan sada zumunta."
"A cikin wannan furuci nata da ta yi a jihar Kogi, Natasha ta yi ƙarya ta hanyar cewa na umarci tsohon gwamnan Kogi, Alhaji Yahaya Bello, da ya ‘kashe ta a jihar Kogi maimakon a Abuja’ da nufin ya zama kamar mutanen mazabar ta ne suka aikata laifin."
Akpabio na so a binciki Sanata Natasha
A cikin ƙarar, wadda aka tura ta ga Ministan shari’a kuma Babban lauyan gwamnatin tarayya, Lateef Fagbemi, Akpabio ya bayyana zargin da Natasha ta yi masa a matsayin zunzurutun ƙarya.

Asali: Facebook
Ya ce:
"Wannan furuci ba wai kawai ƙarya ba ce mai muni, amma da gangan aka yi shi da nufin ɓata mani suna, kawo barazana ga rayuwata da tsaron lafiyata, da kuma tayar da zaune tsaye a harkokin siyasa."
Akpabio ya ce zargin da Sanatar daga Kogi ta yi masa yana da alaƙa da siyasa kuma an shirya shi domin tayar da rikici da kuma ɓata masa suna.
Akpabio ya kalubalanci kotu a kan Natasha
A wani labarin, kun ji cewa Godswill Akpabio, ya kalubalanci hurumin Babbar kotun tarayya kan sauraron karar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan ta shigar gabanta.
Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, wacce aka dakatar daga Majalisar dattawa ta shigar da kara gaban kotun tana kalubalantar ladabtar da ita da Majalisar Dattawa ta yi.
Baya ga Akpabio, wadanda Natasha ke kara sun hada da Majalisar dattawa baki dayanta da kuma Shugaban Kwamitin Majalisar Dattawa kan Hakkoki, Ladabtarwa da Korafe-korafe.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng