Abin da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima Ke Bukata daga Ƴan Arewa

Abin da Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima Ke Bukata daga Ƴan Arewa

  • Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima na bukatar goyon baya daga al'ummar Arewacin Najeriya
  • Tsohon sanatan Kaduna ya ce Shettima ne mutumin da ke rike da muƙamin siyasa mafi girma daga Arewa, don haka ya na bukatar haɗin kan jama'arsa
  • Kwamared Sani ya buƙaci ƴan Arewa kama daga malamai, ƴan kasuwa, shugabanni masu ci da tsofaffi su su kira zama don yin tsarin ceto yankin

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Tsohon Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Kwamared Shehu Sani, ya yi kira ga al’ummar Arewacin Najeriya da su mara wa Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, baya.

Shehu Sani ya bayyana Kashim Shettima a matsayin wakilin Arewa lamba ɗaya a matakin tarayya kuma jajirtaccen mutum mai kamun kai da ƙaunar yankinsa.

Shehu Sani.
Shehu Sani ya bukaci yan Arewa su marawa Kashim Shettima baya Hoto: Shehu Sani
Asali: Twitter

Tsohon sanatan ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Laraba, 9 ga watan Afrilu, 2025.

Kara karanta wannan

Ana batun hadaka, shugaba a APC ya fadi tagomashin da Arewa ta samu a mulkin Tinubu

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abin da Kashim Shettima ke buƙata

Kwamared Sheu Sani, ɗan gwagwarmayar kare haƙƙin ɗan adam kuma masanin harkokin siyasa ya bayyana cewa Shettima na da muhimmanci ga Arewa.

Ya buƙaci shugabanni da ɗauƙacin ƴan Arewa su girmama Shettima kuma su ba shi cikakken goyon baya.

“Shettima shi ne mai rike da mukamin siyasa mafi girma daga Arewa. Ya na gudanar da aikinsa da girmamawa, natsuwa, da ɗabi'a ta kishin ƙasa.
"Don haka ya kamata mu jawo namu a jiki, mu mutunta shi tare da ba shi goyon baya domin ya kare muradunmu na doka da tsarin mulki.”

Ya kamata shugabannin Arewa su haɗa kai

Shehu Sani, wanda ya wakilci Kaduna ta Tsakiya a Majalisar Dattawa ya jaddada buƙatar haɗin kai a Arewa tare da tsara yadda za a fuskanci kalubalen da ke addabar yankin.

Tsohon sanatan ya ƙara da cewa yana fatan wata rana Arewa za ta haɗa dukkan masu ruwa da tsaki tun daga malamai, shugabanni, ƴan kasuwa da sauransu domin tunkarar matsalolin yankin.

Kara karanta wannan

Ndume ya tono fada kan sukar Tinubu, fadar shugaban kasa ta yi martani mai zafi

A cewarsa, ƴan Arewa na bukatar zama domin tsara yadda za a fidda yankin daga ƙalubalen talauci, ta'addanci da koma bayan da ake fuskanta.

“Ina fatan ganin ranar da Arewa za ta zauna a wuri guda; shugabanni masu ci da tsofaffi, ’yan kasuwa, masana, malamai, ’yan fim, ’yan wasa da matasa, domin fitar da ingantaccen tsarin ci gaba wanda zai fidda yankin daga cikin talauci, rashin ci gaba da matsalar ta’addanci."

Shehu Sani zai tsaya takara a zaɓen 2027

A wani rahoton, kun ji cewa Kwamared Shehu Sani ya bayyana cewa ya na da niyyar sake neman takarar kujerar sanatan Kaduna ta Tsakiya a zaɓen 2027 mai zuwa.

Tsohon sanatan, wanda bai daɗe da komawa jam'iyyar APC ba, ya ce zai yi aiki tuƙuru domin tabbatar da cewa Gwamna Uba Sani ya koma wa'adi na biyu a mulkin Kaduna.

Shehu Sani ya kara da cewa duk da ya na da burin neman takara amma bai kai muhimmancin tazarcen Malam Uba Sani ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng