Malamin Musulunci Ya Gano Hanya, Ya Jagoranci ’Yan PDP da APC Zuwa SDP
- Malamin addini, Imam Nura Gwanda ya jagoranci masu sauya sheka daga jam'iyyun APC da PDP zuwa SDP a Katsina
- Malamin ya ce ya kamata malamai magada Annabawa su shiga siyasa don tsaftace ta daga munanan halaye da son zuciya
- Imam Aliyu wanda ya yarda da SD ya ce mulki ya gaza kawo sauyi, ya na mai nuna wahala da matsalar tsaro a Katsina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Katsina - Wani malamin addinin Musulunci a Jihar Katsina, Imam Nura Gwanda, ya jagoranci daruruwan masu sauya sheka zuwa jam’iyyar SDP daga APC da PDP.
Imam Nura Aliyu, wanda ya yi magana a madadin masu sauya sheka, ya ce dole ne malamai su shiga siyasa domin tsaftace tsarin mulki.

Asali: Facebook
Malami ya samu magoya baya, sun koma SDP
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jam'iyyar SDP a jihar ta wallafa a shafin na Facebook a jiya Litinin 24 ga watan Maris, 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Malamin ya shawarci al'umma da sauran malamai kan shiga siyasa duba da yadda ake kallonta a matsayin na lalatattun mutane.
Ya ce:
“Lokaci ya yi da za mu daina zama mu kalli siyasa tana lalacewa, dole ne mu shiga domin kawo sauyi mai kyau.”
Ya kuma gargadi mutane da su guji ‘yan amshin shata, yana mai cewa:
“Idan za mu tsaida dan takara, ya zama mutum mai kima da gaskiya.”
“Mun kasance cikin wahala duk da cewa Katsina jiha ce da Musulmi suka fi yawa, wadanda aka dorawa nauyin rage wahala sun kara mana matsala."
Imam Aliyu ya bayyana takaicinsa kan halin da ake ciki a Katsina, yana mai cewa al’umma sun dade suna neman sauyi ba tare da samun shi ba.

Asali: Facebook
Musabbabin komawar malamin Musulunci SDP
Punch ta ce malamin ya bayyana cewa bayan nazarin jam’iyyar SDP, sun yanke shawarar shiga cikinta saboda su na da yakinin ita ce jam’iyyar da za ta taimaka musu.
Malamin addinin ya ce ba don neman abin duniya yake shiga siyasa ba, sai don kokarin ceto al’umma daga wahala da matsaloli.
Ya kara da cewa:
“Talauci, rashin tsaro da yunwa sun addabi mutane, har a cikin birane, Shugabanni sun gaza, shi ya sa muka shiga SDP."
“Tun daga 1999 muna cikin siyasa, ba don amfanin kanmu ba, sai don jin dadin jama’a, yanzu za mu yi aiki tukuru domin nasarar SDP."
Ya ce tun daga PDP, ANPP, CPC, da APC ya ke cikin siyasa, kuma manufarsa ita ce taimakawa jama’a, ba neman riba ba.
Shugaban jam'iyyar SDP na Katsina, Bello Safana, ya tarbi sabbin mambobin, yana mai cewa jam’iyyar tana samun goyon baya saboda gaskiya da adalci.
Ya ce:
“A yau da rana, mun samu sababbin mambobi 400 daga APC, PDP, PRP, da NNPP, kuma yawan masu sauya sheka yana karuwa kullum.”
Safana ya ce mutanen APC sun daina yarda da jam’iyyar saboda rashin cika alkawari, wanda hakan ya sa suka koma SDP.
Tsohon dan takarar gwamnan Kano ya koma APC
A wani labarin, Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya karɓi manyan jiga-jigan jam’iyyar SDP da suka koma APC.
An ce mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa, Injiniya Yusuf Buhari, da ɗan takarar gwamnan Kano, sun koma APC tare da shugabanni 38.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng