'Za Mu Hana Mutfwang Tazarce': Minista Ya Fadi yadda APC Za Ta Kwace Filato a 2027

'Za Mu Hana Mutfwang Tazarce': Minista Ya Fadi yadda APC Za Ta Kwace Filato a 2027

  • Ministan jin-ƙai, Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa PDP ba za ta iya ci gaba da mulki a Filato ba, don haka APC za ta karɓi mulki a 2027
  • Farfesan wanda ya kasance ɗan takarar gwamnan APC a zaɓen da ya gabata, ya ce APC ta shirya kwace mulki daga hannun Caleb Mutfwang
  • Ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai yi nasara a zaɓen 2027, ya na mai cewa gwamnatinsa ta samar da tsaro a jihar Filato da kewaye
  • Ministan ya ce zai dawo Filato don yi nemawa Tinubu kuri'u a 2027, ya tabbatar da cewa APC za ta yi nasara a jihar ba tare da kalubale ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Filato - Ministan harkokin jin-ƙai, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya bayyana cewa jam’iyyar PDP ba za ta iya samun tazarce a jihar Filato a babban zaɓen 2027 ba.

Kara karanta wannan

An ba Kwankwaso shawara kan shirin haɗakar Atiku, Peter Obi da El Rufai a 2027

Yayin da ya buga kirji da cewa APC za ta kwace mulki daga hannun Gwamna Caleb Mutfwang, Nentawe ya kuma ce Shugaba Bola Tinubu zai sake lashe zaɓe a 2027.

Nentawe Yilwatda ya yi magana kan shirin APC na kwace jihar Filato daga PDP a 2027
Ministan jin-kai, Nentawe Yilwatda ya jaddada shirin APC na kwace Filato a zaben 2027. Hoto: @nentawe1
Source: Twitter

2027: APC za ta karbe mulkin Filato daga PDP

Farfesan Yilwatda, wanda ya kasance ɗan takarar gwamnan Filato na jam’iyyar APC a zaɓen da ya gabata, ya ce jam’iyyarsu ta shirya karɓe mulki, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ministan ya yi wannan furuci ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a gidan rediyon Rhythm FM da ke Jos, babban birnin jihar, a ƙarshen makon nan.

“Babu wani ci gaba na a-zo-a-gani da gwamnatin PDP ta samar a jihar Filato. APC jam’iyya ce mai tausayin jama’a. Mu masu aiki da fada da cikawa ne, ba hayaniyar siyasa ba."

- Prof. Yilwatda.

"Tinubu zai lashe zaben Filato a 2027" - Minista

Ya ƙara da cewa zai dawo Filato lokacin yaƙin neman zaɓe, inda zai yi aiki tukuru domin ganin Shugaba Tinubu ya samu nasara a jihar.

“Zan dawo Filato a lokacin yaƙin neman zaɓe. Zan yi wa Tinubu kamfen a 2027, kuma zai yi nasara a jihar Filato,” inji Nentawe Yilwatda.

Kara karanta wannan

Fubara: Gwamnonin PDP sun nufi kotun koli kan dokar ta baci a jihar Ribas

Ministan ya jaddada cewa ko da yake Filato ba ta zaɓi Tinubu a 2023 ba, amma shugaban ƙasar ya yi kokari sosai wajen daƙile matsalar tsaro a yankin.

Yayin da ya ce yanzu manoma da dama sun fara komawa gonakinsu bayan dogon lokaci na fargaba, Yilwatda ya ce:

“Da irin ci gaban da aka samu a harkar tsaro, Shugaba Tinubu zai lashe jihar Filato a 2027, kuma za jajirce don tabbatar da hakan."

Shirin APC a zaben 2027 a Filato

A yayin da babban zaɓen 2027 ke kara kusantowa, jam’iyyar APC a jihar Filato ta fara shirin karɓe mulki daga hannun PDP, inda manyan shugabanninta ke bayyana kwarin gwiwa kan nasararta.

Ministan jin-ƙai, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya tabbatar da cewa jam’iyyarsu za ta yi nasara dumu-dumu a Filato, tare da nuna cewa gwamnatin PDP mai ci ba ta kawo wani gagarumin ci gaba ba a jihar.

Masu fashin baki kan siyasa sun bayyana cewa wannan furuci na Nentawe Yilwatda wata alama ce da ke nuna yadda APC ke ƙara samun kwarin gwiwa a siyasance, musamman ganin cewa ministan ya kasance ɗan takarar gwamna na jam’iyyar a 2023.

Kara karanta wannan

Kwana 1 da dakatar da Fubara, Gwamna ya yi wa Tinubu alkawari kan zaben 2027

Wasu na ganin cewa kasancewarsa a cikin gwamnatin Shugaba Tinubu zai ba shi damar samun goyon baya daga matakin tarayya don cimma burin APC a Filato.

A gefe guda, jam’iyyar PDP a jihar na fuskantar ƙalubale daga ‘yan adawa masu ra’ayin cewa gwamnatinta ba ta yi wani aiki na a-zo-a-gani ba tun bayan hawanta mulki.

Wasu jiga-jigan jam’iyyar APC sun bayyana cewa idan har PDP ba ta sauya salon mulkinta ba, to tabbas za ta fuskanci babban kalubale daga APC a 2027.

Ana so Tinubu ya ayyana dokar ta baci a Osun

A wani labarin, mun ruwaito cewa, tsohon minista, Oyewale Adesiyan, ya nemi ayyana dokar ta-baci a Osun saboda tabarbarewar tsaro da rikice-rikicen siyasa a jihar.

Ya zargi Gwamna Ademola Adeleke da kin bin hukuncin kotu, yana mai cewa hakan ne ya haddasa rikicin kananan hukumomi da kuma asarar rayuka.

Adesiyan ya bukaci a yi amfani da sashe na 305 na kundin tsarin mulki domin tabbatar da doka da oda tare da dawo da zaman lafiya a Osun.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com