An ba Kwankwaso Shawara kan Shirin Haɗakar Atiku, Peter Obi da El Rufai a 2027
- Yayin da ƴan adawa ke shirin haɗaka domin kayar da Bola Tinubu a 2027, jigon NNPP ya gargadi Rabiu Musa Kwankwaso
- Asiwaju Moshood Shittu ya bukaci Sanata Kwankwaso ya kula da motsinsa na siyasa, ka da ya yanke shawara cikin gaggawa
- Ɗan siyasar ya ke cewa gaggawar haɗakar siyasa ce ta haifar APC wadda ta zama mafi muni bayan kayar da Goodluck Jonathan
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano - Jigo a jam’iyyar NNPP, Asiwaju Moshood Shittu, ya gargadi jagora, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, da kada ya yi gaggawar shiga haɗakar jam'iyyun adawa.
Asiwaju Shittu, wanda tsohon darektan kwamitin kamfen Kwankwaso ne a zaɓen 2023 ya bayyana haka ne yayin da yake zantawa da manema labarai a Abuja a karshen mako.

Asali: Twitter
Ya ce yin gaggawar haɗa kai da wata jam’iyya ba tare da cikakken tsari ko shiri ba, na iya zama matsala kamar yadda ya faru gabanin zaɓen 2015, rahoton Leadership.

Kara karanta wannan
Sanata Kalu ya watsa wa matasan Arewa ƙasa a ido, ya yi maganar karawa da Tinubu a 2027
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ba a so a maimaita hadakar 2014
Jigon NNPP ya ce bai kamata a sake maimaita kuskuren da aka yi a 2014 ba, lokacin da aka yi gayyar jam’iyyun adawa cikin gaggawa domin kawar da tsohon shugaba Goodluck Jonathan.
A cewarsa, a lokacin an ƙulla wannan haɗaka ne ba tare da tantance cancantar wanda za a tsayar a matsayin ɗan takara ba.
"Sakamakon hakan ya kasance bala’i domin mun ƙare da wani da ya fi Jonathan muni," in ji shi.
Asiwaju ya ba Kwankwaso shawara
Ya bukaci Kwankwaso da ya nazarci al’amuran siyasa sosai kafin ya yanke shawara kan ko zai shiga wata kawancen siyasa gabanin 2027.
A cewarsa, tsohon gwamnan Kano ya zama babban jigo a siyasar Najeriya, amma bai kamata ya bari gaggawa ko yawan magoya baya su rinjaye shi ba.
"A yau, kowa na son Kwankwaso ya kasance a gefensa. Yana da farin jini, amma dole ne ya yi taka-tsan-tsan. Wanene za a tsayar takara? Menene manufofin haɗakar?
"Shin akwai cikakken tsari a haɗakar da ake shirin yi ta ƴan adawa? Wadannan tambayoyi dole ne a amsa su kafin a ci gaba da shirye-shirye," in ji Shittu.

Asali: Facebook
Abubuwan da ke karya haɗakar siyasa
Ya kuma bayyana cewa mafi yawan haɗakar jam’iyyun adawa a Najeriya suna gazawa ne saboda rashin ingantaccen tsari, rashin ƙwararrun ‘yan takara, da rashin manufa.
A ƙarshe, ya yi kira ga Kwankwaso da ya sanya muradun al’ummar Najeriya a gaba fiye da lissafin siyasa.
A cewarsa, tarihi zai fi tunawa da Kwankwaso bisa kyawawan shawarwari da ya yanke fiye da yin gaggawar haɗaka da wasu ƴan adawa maras inganci.
NNPP ta sake taso Kwankwaso a gaba
A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar NNPP ta tsagin Agbo Major ta jaddada raba gari da Madugun Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso da ƙungiyar TNM.
Tsagin NNPP ya aika wasiƙa zuwa ga INEC tare da tura kwafinta ga sufetan ƴan sandan Najeriya domin sanar da shi cewa babu ruwan jam'iyyar da su Kwankwaso.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng