Sakon Kwankwaso ga Jagoran Kwankwasiyya, El Rufai da Atiku kan Zaben 2027
- Jigon jam'iyyar APC a Kano, Musa Iliyasu Kwankwaso ya bukaci ‘yan adawa su daina sukar Tinubu, su ba shi dama ya gyara kasa
- Kwankwaso ya ce sukar da Atiku Abubakar, Nasir El-Rufa’i da Rabiu Kwankwaso ke yi wa Tinubu ba daidai ba ne, kuma tana hana ci gaba
- Ya bayyana cewa ko da sun kafa kawance, ‘yan adawar ba za su hana jam'iyyar APC lashe zabe a 2027 ba saboda karancin farin jini
- Kwankwaso ya yaba da matakin Tinubu na ayyana dokar ta baci a Jihar Ribas, yana ganin hakan ya ceci dimokuradiyyar kasa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Kusa a jam’iyyar APC, Musa Iliyasu Kwankwaso ya shawarci yan adawa game da zaben 2027.
Kwankwaso ya bukaci shugabannin adawa su ba shugaba Bola Tinubu dama ya magance matsalolin kasar ba tare da suka ba.

Kara karanta wannan
Rikicin Ribas: An ƙara samun bayanai kan dalilin shugaba Tinubu na dakatar da gwamna

Source: Facebook
Musa Kwankwaso ya shawarci gungun yan adawa
Kwankwaso wanda shi ne Daraktan Kudi na hukumar Kogunan Hadejia Jama’are ya bayyana haka ga manema labarai a Kano ranar Juma’a, cewar Arise News.
Kwankwaso ya ce:
“Maimaikon su ci gaba da sukar shugaba a kan kowace doka ko mataki, Atiku, El-Rufa’i da Kwankwaso su bari ya fuskanci matsalolin kasa.
“Tinubu ya sha wahala wajen gyara kasa; sukar da ake yi masa ba adalci ba ne, kuma tana janyo tarnaki, ya kamata a dakatar da hakan."

Source: Facebook
'Ba za ku iya da Tinubu ba' - Kwankwaso
A cewarsa, kawancen da Atiku, El-Rufa’i da Kwankwaso suka kafa ba zai hana APC ci gaba da mulki a 2027 ba domin ba su da karfin siyasa.
Kwankwaso ya shawarce su da cewa da sun yi hakuri sun bar Shugaba Tinubu saboda ya ci gaba da ayyukan alheri da yake yi domin inganta Najeriya da tattalin arzikinta.
Ya kara da cewa:
“Atiku, Kwankwaso da El-Rufa’i ba za su hana APC nasara a matakai daban-daban a 2027 ba saboda ba su da karfin siyasa.
“Kun ga cewa ‘yan majalisar dokokin Jihar Ribas guda 27 dukkansu ‘yan APC ne, duk da haka shugaba ya ceci jihar da kuma dimokuradiyya."
Daga nan sai ya yaba wa shugaba Tinubu bisa ayyana dokar ta baci a Jihar Ribas, yana ganin hakan na da matukar amfani ga dimokuradiyya.
Ya ce matakin ya yi daidai duba da rigimar siyasa da ta ki ci ta ki cinyewa wanda hakan zai dakile abin da ka iya biyo baya.
Sai dai Legit ba ta da labarin rinjayen APC a majalisar dokokin Ribas domin 'yan majalisar sun karyata zancen barin PDP.
Kwankwaso ya magantu kan fitar idin Aminu Ado
Kun ji cewa kusa a jam'iyyar APC a Kano, Musa Ilyasu Kwankwaso ya bayyana matsayin Muhammadu Sanusi II Sarkin gwamnati da Aminu Ado Bayero Sarkin a cikin al'umma .
Kwankwaso ya bayyana cewa mutane sun fi son Aminu Ado Bayero saboda amincewarsu da shi, yayin da gwamnati ta nada Sanusi a matsayin Sarki.
Tsohon kwamishina a Kano ya ce babu wata matsala, kowa yana da Sarki nasa, kuma Aminu Ado zai fito filin idi karfe 7:00 na safe ranar Sallah.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

