Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da Mutanen Buhari Sun Tunkari Tinubu da Murya Daya

Fubara: Atiku, El Rufai, Obi da Mutanen Buhari Sun Tunkari Tinubu da Murya Daya

  • Wasu 'yan adawar siyasa sun yi taron manema labarai, sun ce sanya dokar ta baci a Rivers bai dace da kundin tsarin mulki ba
  • Manyan 'yan adawar sun bukaci majalisar dokokin Najeriya da kotun tarayya su rushe dokar ta baci da Bola Tinubu ya sanya
  • Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, Babachir Lawal da Yunusa Tanko sun halarci taron a Abuja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Wasu fitattun mutane da ‘yan siyasa daga sassa daban-daban na Najeriya sun gudanar da taron manema labarai a ranar Alhamis, 20 ga Maris, 2025.

Sun gudanar da taron ne domin su nuna adawarsu ga ayyana dokar ta-baci da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi a Jihar Rivers.

Kara karanta wannan

Fubara: Bayan majalisa, gwamnoni sun kalubalanci Tinubu kan rikicin Rivers

Atiku
Manyan 'yan siyasar Najeriya sun kalubalanci tinubu kan dakatar da Fubara. Hoto: Haladu Mohammed Musa
Asali: Facebook

Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i ne ya wallafa matsayar da suka yanke a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewar jagororin, wannan mataki ba ya bisa doka, kuma ya ci karo da kundin tsarin mulkin Najeriya.

Sun ce ba daidai ba ne Shugaban Kasa ya dakatar da Gwamnan jihar, Mataimakinsa, da kuma Majalisar Dokokin jihar ba tare da bin matakan doka ba.

Zargin Tinubu da take kundin tsarin mulki

Jagororin sun bayyana cewa matakin da Shugaban Kasa ya dauka ya saba wa kundin tsarin mulkin Najeriya, musamman sassa kamar haka:

1. Bin haramtacciyar hanyar cire gwamna

Sashe na 188 na kundin tsarin mulki ya fayyace cewa idan za a tsige Gwamna, dole ne a bi tsarin shari’a da Majalisar Dokoki ta jihar ke jagoranta.

A karkashin haka suka ce ba a ba Shugaban Kasa ikon tsige Gwamna ko dakatar da Majalisar Dokoki ba.

Kara karanta wannan

Rivers: Atiku ya sauya salo, ya roƙi ƴan Najeriya bayan Tinubu ya sanya dokar ta ɓaci

2. Amfani da sashe na 305 ba bisa ka’ida ba

Sun ce wannan sashe na kundin tsarin mulki yana bada dama ga Shugaban Kasa ya ayyana dokar ta-baci ne kawai idan akwai babbar barazana ga tsaro ko hadarin da zai iya ruguza kasa.

Saboda haka suka ce a halin yanzu, babu yaki ko wani rikici mai yawa a Rivers da zai sa a dauki irin wannan mataki.

3. Kin bin ka’idojin amincewar majalisa

Sun bayyana cewa dole ne a sami amincewar kashi biyu bisa uku (2/3) na ‘yan Majalisar Dokoki ta kasa kafin dokar ta-baci ta tabbata.

Jagororin siyasar sun ce idan ba a samu amincewar 'yan majalisar ba, to matakin zai zama haramtacce.

Atiku Abubakar
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: PDP Official
Asali: Facebook

Zargin gwamnatin tarayya da fakewa da siyasa

Shugabannin sun ce matsalar Rivers ba ta da nasaba da tsaro, sai dai yunkurin gwamnati na kwace iko da jihar.

Kara karanta wannan

Gwamna ya maida martanin barazanar dakatar da shi kamar yadda aka yi a Ribas

Sun ce matsalar ta samo asali ne daga sauya sheka da wasu ‘yan Majalisar Dokokin jihar suka yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC, abin da ya janyo rikici na siyasa.

Sannan sun kuma ce gwamnatin tarayya na amfani da wannan rikici a matsayin dalilin kwace iko da jihar ba tare da bin doka ba.

Bukatun shugabannin ga gwamnati da majalisa

Shugabannin sun bukaci:

1. Shugaba Tinubu ya janye dokar nan take kuma ya maido da Gwamnan Rivers, Mataimakinsa, da Majalisar Dokoki.

2. Majalisar Dokoki ta kasa kada ta amince da wannan mataki, kuma ta kare tsarin mulkin Najeriya.

3. Kotuna su gaggauta soke wannan matakin da Bola Tinubu ya dauka domin hana irin hakan a nan gaba.

4. ’Yan Najeriya su tashi tsaye domin kare dimokuradiyya da hana wannan yunkurin juyin mulki ta hanyar siyasa.

Kara karanta wannan

Wuri ya yi wuri: An daka wawar kayan abinci a motar Majalisar Dinkin Duniya a Borno

Shugabannin da suka hallara taron

Vanguard ta wallafa cewa manyan ‘yan siyasa irin su Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai, Emeka Ihedioha, Babachir Lawal, da Dr Tanko na Obidient Movement sun halarci taron.

Tsofaffin ministoci a gwamnatin Muhammadu Buhari; Rotimi Amaechi da Kayode Fayemi sun bada hakurin rashin halartar zaman.

Haka zalika Legit Hausa ta samu labarin zuwan Babachir David Lawal wanda ya rike matsayin sakataren gwamnatin tarayya a mulkin.

Sun ce za su tuntubi Majalisar Dokoki domin hana amincewa da dokar, domin kare dimokuradiyya a Najeriya.

Sanata zai yaki bukatar Tinubu a majalisa

A wani rahoton, kun ji cewa Sanata Seriake Dickson na jihar Bayelsa ya ce zai yi mai yiwuwa wajen yaki da dokar ta baci da aka sanya a jihar Rivers.

Sanatan ya ce zai hada kai da Sanatoci a zauren majalisa domin tabbatar da cewa bukatar shugaban kasar ba ta samu amincewa ba.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel