Gwamna Ya Maida Martanin Barazanar Dakatar da Shi kamar Yadda aka Yi a Ribas

Gwamna Ya Maida Martanin Barazanar Dakatar da Shi kamar Yadda aka Yi a Ribas

  • Gwamnatin Jihar Osun ta soki Ajibola Basiru bisa kiran da ya yi na ayyana dokar ta-baci a jihar, kamar yadda Shugaba Bola Tinubu ya yi a Ribas
  • Kwamishinan Yaɗa Labarai da Wayar da Kan Jama'a na jihar, Kolapo Alimi, ne ya bayyana rashin jin daɗin gwamnatin bayan kalaman Ajibola Basiru
  • Basiru, wanda shi ne Sakataren APC na ƙasa, ya jinjinawa matakin da Tinubu ya ɗauka, sannan ya bukaci a aiwatar da irin wannan mataki a Osun

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Osun - Gwamnatin Osun ta soki Sakataren jam’iyyar APC na kasa, Ajibola Basiru, bisa kiran da ya yi ga shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya ayyana dokar ta-baci a jihar.

Wannan kiran ya biyo bayan matakin shugaba Tinubu na ayyana dokar ta-baci a Ribas tare da dakatar da gwamnan jihar, mataimakiyarsa da ‘yan majalisar dokoki na watanni shida.

Kara karanta wannan

El-Rufa'i ya aika da sako ga Tinubu kan dakatar da zababben gwamnan Ribas

Jihar
Gwamnatin Osun ta fusata kan kiran a samya dokar ta baci a jihar Hoto: Gov Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Jaridar The Guardian ta ruwaito cewa jigon APC din ya bukaci Shugaban kasa da ya fadada wannan mataki zuwa Jihar Osun.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci a yi hakan ne saboda matakin Gwamna Ademola Adeleke na hana sababbin shugabannin kananan hukumomi da kotu ta mayar su ci gaba da aikinsu.

Gwamnatin Osun ta soki sakataren APC

Premium Times ta wallafa cewa Kwamishinan yada labarai da wayar da kan jama'a na Jihar Osun, Kolapo Alimi, ya bayyana bukatar Basiru a matsayin ganganci da rashin tunani.

A wata sanarwa da ya fitar, ya ce:

“Gwamnatin jihar ta dauki wannan kira a matsayin rashin tausayi, son zuciya da kuma sabawa doka, duba da cewa akwai babban bambanci tsakanin abin da ke faruwa a Ribas da kuma Osun.”

Gwamnatin Adeleke ta gargadi jam'iyyar APC

Gwamnatin Osun ta yi gargadi ga Basiru da jam’iyyar APC da kada su haddasa rikici da rashin zaman lafiya a jihar don kawai su samu mulki ta karfi da yaji.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da 'shugaban riko' na jihar Ribas, bayanai sun fito

Ademola
Gwamnatin Osun ta zargi 'yan APC da rashin bin doka Hoto: Gov Ademola Adeleke
Asali: Facebook

Sanarwar ta kara da cewa:

“Dole ne a fahimta cewa ba Basiru kadai ba ne ke da wannan tunanin rashin kyau, illa gaba dayan ‘yan jam’iyyar APC da mabiyansu a Osun, wadanda kullum burinsu shi ne shirya makirci da dabaru domin su karbi mulki ta bayan fage.
“Amma da ikon Ubangiji da goyon bayan al’ummar jihar Osun, duk wani shirin da ake yi domin hana gwamnati mai ci yin aikinta ba zai yi nasara ba.”

Gwamnatin Osun ta shawarci shugaba Tinubu

Gwamnatin Osun ta bukaci shugaba Bola Ahmed Tinubu da ya yi watsi da wannan kira na wasu ‘yan jam’iyyarsa da ke son kawo tarnaki ga zaman lafiya a jihar.

A cewarsa:

“Duk wani mai bibiyar siyasar Osun zai fahimci cewa jam’iyyar APC a jihar ba ta da farin jini, karbuwa da kuma dabarun siyasa da za su ba ta damar kayar da Ademola Adeleke a kowane zabe.
Wannan ne ya sa su ka koma amfani da dabaru marasa kyau domin su samu mulki ta bayan fage.

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya ɗauki matakin ƙarshe, ya fice daga gidan gwamnatin jihar Ribas

Ana son sa dokar ta-baci a Osun

A baya, mun wallafa cewa jam’iyyar APC ta nuna cikakken goyon bayanta ga matakin shugaba Bola Ahmed Tinubu na ayyana dokar ta-baci a Ribas, kuma a bukaci a fadada zuwa Osun.

Shugaba Tinubu ne dai ya ayyana dokar ta baci tare da dakatar da gwamna, mataimakiyarsa da 'yan majalisar jihar saboda yadda rashin jituwa a tsakaninsu da matsalar tsaro.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel