El Rufa'i Ya Aika da Sako ga Tinubu kan Dakatar da Zababben Gwamnan Ribas

El Rufa'i Ya Aika da Sako ga Tinubu kan Dakatar da Zababben Gwamnan Ribas

  • Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bayyana matakin da gwamnatin tarayya ta dauka a Ribas a matsayin haramun a dimokuradiyya
  • Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, ya ayyana dokar ta-baci a Ribas saboda abin da ya kira barazanar tsaro sakamakon damalmalewar siyasar jihar
  • El-Rufa’i ya bukaci Tinubu da ya janye matakin dakatar da zababbun jami’an gwamnati, yana mai cewa hakan ya saba wa kundin tsarin mulki

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya bukaci Shugaba Bola Tinubu da ya janye hukuncin dakatar da zababbun jami’an gwamnati a jihar Ribas.

El-Rufa’i ya ce dakatar da gwamna da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya ya saba doka, kuma hakan barazana ce ga tsarin dimokuradiyyar Najeriya.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da 'shugaban riko' na jihar Ribas, bayanai sun fito

Tinubu
Tsohon gwamnan Kaduna ya zargi Tinubu da yi wa kundin tsarin mulki karan tsaye Hoto: Nasir El-Rufai/Sir Siminalayi Fubara/Bayo Onanuga
Asali: Facebook

A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na Facebook, El-Rufa’i ya nuna adawarsa ga matakin da shugaba Tinubu ya dauka, ya na mai cewa bai da wata madogara a kundin tsarin mulki.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, kundin tsarin mulkin Najeriya bai ba shugaban kasa ikon cire zababbun jami’ai a matakin jiha ba, domin hakan na rage karfin tsarin dimokuradiyyar tarayya.

El-Rufa’i ya kafa hujjar haramcin matakin Tinubu

El-Rufa’i ya ambaci hukuncin Kotun Koli a shari’ar Dariye da Antoni Janar na Tarayya, wanda ya haramta dakatar da zababbun jami’ai, wanda ke gaskata cewa tsarin ya saba doka.

Ya jaddada cewa matsalar tsaro da gwamnatin tarayya ta bayar a matsayin dalilin daukar matakin, abu ne da za a iya shawo kansa ta hanyar ayyana dokar ta baci a jihar.

Nasir
El-Rufa'i ya shawarci Tinubu kan dakatar da gwamnatin Ribas Hoto: Nasir El-Rufa'i
Asali: Twitter

Tsohon gwamnan ya ce:

"Tabbas, matsalolin tsaro da Shugaban Kasa ya ambata a jawabinsa su na bukatar kulawa matuka da matakan gaggawa don dakile barazanar."

Kara karanta wannan

Gwamna Fubara ya ɗauki matakin ƙarshe, ya fice daga gidan gwamnatin jihar Ribas

"Za a iya ayyana dokar ta-baci domin bai wa hukumomin tsaro ikon daukar matakan da suka dace domin shawo kan matsalar."

"Tinubu ya wulakanta dimokuradiyya" Inji El-Rufa’i

El-Rufa’i ya kuma gargadi cewa rusa tsarin dimokuradiyya saboda matsalar tsaro babbar barazana ce ga tsarin dimokuradiyya da rusa tsarin mulki.

Ya tunatar da Tinubu yadda ya soki tsohon Shugaban kasa, Goodluck Jonathan kan ayyana dokar ta-baci a Arewa maso Gabas duk da ba a cire zababbun jami’ai ba.

El-Rufa’i ya bukaci Tinubu ya sake shawara

Ya bukaci shugaban kasa da ya sake nazari kan matakin da ya dauka a Jihar Ribas domin tsare kundin tsarin mulki da bin doka da oda.

El-Rufa’i kara da cewa:

"Wannan lamari yana bukatar sake tunani domin gyara barnar da aka yi wa al’ummar jihar Ribas."

Tsohon gwamnan ya kuma bukaci sauran jama'a masu kishin kasa da masu ruwa da tsaki su fito fili su soki wannan abin da ya kira tauye kundin tsarin mulkin kasa.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Jonathan ya dauko zancen tsige Tinubu kan dakatar da Gwamnan Ribas

Ribas: An dawo da batun tsige Tinubu

A baya, mun wallafa cewa tsohon hadimin Shugaban kasa, Goodluck Jonathan shawara, Dr. Reuben Abati, ya caccaki shugaba Bola Tinubu kan sanya dokar ta-baci a jihar Ribas.

Abati ya bayyana cewa Shugaban Kasa ba shi da ikon dakatar da zababben gwamna ko ‘yan majalisar jiha, saboda haka ya bukaci 'yan majalisa da su tsige Bola Tinubu a cikin gaggawa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng