Gwamna Fubara Ya Ɗauki Matakin Karshe, Ya Fice daga Gidan Gwamnatin Jihar Ribas

Gwamna Fubara Ya Ɗauki Matakin Karshe, Ya Fice daga Gidan Gwamnatin Jihar Ribas

  • Dakataccen gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara ya tattara kayansa ya bar gidan gwamnati da ke Fatakwal da safiyar yau Laraba
  • Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da sabon shugaban rikon Ribas ke shirin kama aiki bayan Bola Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci
  • Rahotanni sun nuna cewa duk da wannan sauyi, al'ummar Ribas sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum kamar ba a yi ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Rivers - Bayan ayyana dokar ta-baci a Rivers da shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi, an tabbatar da cewa dakataccen gwamna, Siminalayi Fubara, ya bar fadar gwamnati da ke Fatakwal a safiyar Laraba.

Majiyoyi sun ce Fubara ya fice daga fadar gwamnati yayin da sabon mai kula da jihar, tsohon hafsan sojan ruwa, Admiral Ekwe Ibas (ritaya), ke shirin kama aiki a matsayin gwamnan riko.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya sa labule da 'shugaban riko' na jihar Ribas, bayanai sun fito

Gwamna Fubara
Gwamna Fubara ya bar gidan gwamnatin Ribas da safiyar ranar Laraba Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Gwamnatin Tinubu ta canza dakarun tsaro

Da wakilin Daily Trust ya kai ziyara fadar gwamnatin jihar a safiyar Laraba, ya lura da cewa an sauya duka jami’an tsaron da ke kula da wurin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Akalla motocin yaki guda uku watau APC ne aka jibge a kofar shiga, domin tabbatar da tsaro a wurin.

Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya tabbatar da cewa an sauya jami’an tsaron da ke fadar gwamnatin da wasu wadanda ke karkashin umarnin gwamnatin tarayya.

Fubara ya bar gidan gwamnatin Ribas

“Gwamna Fubara ya bar fadar gwamnati a safiyar yau. Sabon mai kula da al'amuran Ribas da aka naɗa bai iso ba tukuna.
"Amma ana sa ran zai iso kowanne lokaci. An sauya dukkan jami’an tsaron da ke Fadar Gwamnati. Yanzu haka komai na tafiya lafiya, babu wata matsala,” in ji majiyar.

Mazauna Ribas sun ci gaba da harkokinsu

Duk da canjin shugabancin da aka yi, mazauna birnin Fatakwal na ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

Kara karanta wannan

Majalisa ta hargitse ana shirin tattauna maganar dakatar da Gwamna Fubara

Babu wata alamar tashin hankali ko barazana ga zaman lafiya, domin mutane sun ci gaba da rayuwarsu kamar yadda aka saba.

Gwamna Fubara.
Gwamna Fubara ya fita daga gidan gwamnatin Ribas bayan dakatar da shi Hoto: Sir Siminalayi Fubara
Asali: Facebook

Sai dai wasu 'yan jihar na ci gaba da tattauna batun dokar ta-bacin da aka kafa, tare da bayyana ra’ayoyi daban-daban.

Jiya Talata, shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci a Ribas, yana mai cewa an dauki matakin ne saboda barnata bututun mai da kuma gazawar masu ruwa da tsaki wajen shawo kan rikicin siyasa.

Sabon mai kula da Ribas zai kama aiki

Tun bayan wannan sanarwa, an kara yawan jami’an tsaro a wuraren da ake ganin suna da muhimmanci a birnin Fatakwal da kewaye.

Ana sa ran sabon shugaban riko na jihar, Ekwe Ibas, zai fara aiki da zarar an kammala duk wasu shirye-shirye na mika mulki, Punch ta ruwaito.

Abubuwan sani game da sabon shugaban riƙo

A baya mun kawo maku muhimnan abubuwa da ya kamata ku sani game da mutumin da Bola Tinubu ya naɗa domin ya kula da harkokin jihar Ribas.

Kara karanta wannan

Tsohon hadimin Jonathan ya dauko zancen tsige Tinubu kan dakatar da Gwamnan Ribas

Tinubu ya naɗa tsohon hafsan sojin ruwa da ya yi rataya domin ya jagoranci gwamnatin rikon ƙwarya bayan dakatar da Gwamna Simi Fubara.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng