2027: Matasa Sun Kaucewa Tafiyar El Rufai a SDP, Sun Kama Peter Obi da Gwamna Bala

2027: Matasa Sun Kaucewa Tafiyar El Rufai a SDP, Sun Kama Peter Obi da Gwamna Bala

  • Matasan Neja Delta da ke Kudancin Najeriya sun ayyana cikakken goyon bayansu ga shirin haɗewar Peter Obi da Gwamna Bala Muhammed na Bauchi
  • Shugaban matasan Neja Delta (NDYC), Israel Uwejeyan ya ce akwai haske a yunkurin haɗa kan Obi da Gwamna Bala duba da gogewarsu
  • Ya bayyana cewa manyan jiga-jigan biyu suna da kwarewa a harkar shugabanci, haɗin kai da ƙoƙarin kawo sauyi mai amfani

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Niger Delta - Matasan yankin Neja Delta sun yi na'am da yunkurin haɗaka tsakanin Gwamna Bala Muhammed na jihar Bauchi da Peter Obi gabanin zaɓen 2027.

Kungiyar Matasa ta yankin Neja Delta (NDYC) ta bayyana goyon bayanta ga shirin hadin gwiwar Gwamna Bala da tsohon dan takarar shugabancin kasa na LP, Obi.

Peter Obi da Gwamna Bala.
Matasan Neja Delta sun goyi bayan hadakatar Peter Obi da Gwamna Bala Hoto: Mr. Peter Obi, Bala Muhammed
Asali: Twitter

Shugaban kungiyar, Israel Uwejeyan, ne ya bayyana matsayarsu a wata sanarwa da ya fitar, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Bayan El Rufai ya yi fatan ya dawo SDP, alamu sun nuna Peter Obi na shirin canza jam'iyya

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Matasa na goyon bayan Peter Obi da Gwamna Bala

Ya ce wannan haɗaka ta dogara ne kan mutunta juna, maslahar ƙasa, da ƙoƙarin ceto Najeriya, wanda hakan ka iya zama wani haske da kyakkyawan fata ga ƴan Najeriya..

A cewar NDYC, Gwamna Bala ya kasance mai himma wajen hadin kan kasa da kyakkyawan shugabanci, yayin da Peter Obi ya zama abin misali kan rikon gaskiya, tattalin arziki, da shugabanci mai sauya rayuwa.

Kungiyar ta bayyana cewa haɗin kai tsakanin wadannan shugabanni biyu alama ce cewa lokaci ya yi na gyara a harkokin siyasar ƙasar nan.

Ta kuma jinjinawa Gwamna Bala Mohammed bisa kiran da yake yi na siyasa ba tare da gaba ba, haɗin kai, da tsarin mulki da ke bai wa kowa dama.

Kungiyar NDYC ya shawarci ƴan Najeriya

NDYC ta bukaci dukkan ‘yan Najeriya masu kishin kasa, musamman matasa, da su marawa wannan sabon yunƙuri baya, wanda da alama zai kawo ci gaba da tsarin bunkasa kasa.

Kara karanta wannan

Mene ake kitsawa?: Barau ya gana da Baffa Bichi da tsohon kwamishinan Abba

Ƙungiyar ta ce:

“A daidai lokacin da Najeriya ke bukatar shugabanci nagari, mai hangen nesa da kishin jama’a, haɗakar wadannan shugabanni biyu masu ƙwazo da jini a jika na iya zama alheri ga miliyoyin ‘yan kasa.
"Gwamna Mohammed ya kasance jajirtacce wajen hadin kai da kyakkyawan shugabanci, yayin da Peter Obi ya nuna nagarta, ƙwarewa a fannin tattalin arziki, da shugabanci mai canza rayuwar al’umma.
“Haɗuwarsu alama ce da ke nuna lokaci ya yi na yin garambawul a siyasar Najeriya, kuma yanzu PDP ta tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa tana da nufin kawo sauyi."
Bala Muhammed da Peter Obi.
Matasan Neja Delta sun karkata akalarsu zuwa tafiyar Peter Obi da Gwamna Bala Hoto: @SenBalaMohammed
Asali: Twitter

Ƙungiyar matasan ta kuma caccaki tsohon mataimakin shugaban kasa, Alhaji atiku Abubakar, wanda a cewarta burinsa ya karɓi madafun iko don amfanin kansa.

Peter Obi na shirin komawa PDP

A wani labarin, kun ji cewa alamu sun nuna cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi ya fara karkata hankalinsa kan yiwuwar komawa jam'iyyar PDP.

Kara karanta wannan

Rashin tsaro: Shugaban Amurka, Trump ya samu izinin kakaba takunkumi ga Najeriya

Ganawar da Obi ya yi da shugaban ƙungiyar gwamnonin PDP kuma gwamnan Bauchi, Bala Muhammed, na cikin yunkurinsa na tuntuɓar manyan PDP kafin yanke hukunci.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng

iiq_pixel