Majalisa Ta Dauki Matakin Farko na Tsige Gwamna Fubara, Ta Jero Tuhume Tuhume
- Majalisar dokokin jihar Rivers ta aikawa Gwamna Simi Fubara da mataimakiyarsa da sanarwar aikata ba daidai ba
- Sanarwar ta bayyana cewa majalisar jihar ta dauki matakin ne bisa tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999
- Ana zargin Fubara da karkatar da kudin jama’a da kuma hana majalisar dokokin jihar gudanar da aikinta yadda ya kamata
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Rivers - Majalisar dokokin jihar Rivers ta fara aiwatar da matakan tsige Gwamna Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa, Ngozi Odu, bisa wasu tuhume-tuhume.
Sanarwar da majalisar ta fitar ta nuna cewa an dauki wannan mataki ne bisa doka, bayan da kotun koli ta amince da matsayin wasu ‘yan majalisa 27 masu biyayya ga Nyesom Wike.

Asali: Facebook
Jaridar The Punch ta ruwaito cewa a makon da ya gabata Wike ya bayyana cewa ba laifi ba ne a tsige Fubara idan har ya aikata abin da ya sabawa doka.

Kara karanta wannan
Lokacin matasa ya yi: Atiku ya yaba da yadda matashiya 'yar bautar kasa ta soki Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Idan mutum ya aikata abin da zai sa a tsige shi, to a tsige shi."
- Nyesom Wike
Zarge-zargen da ake yi wa gwamna Fubara
Sanarwar da majalisar dokokin Rivers ta fitar ta nuna cewa an tuhumi Gwamna Siminalayi Fubara da cin gashin kansa wajen kashe kudin jama’a ba tare da bin ka’ida ba.
Sauran laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa sun hada da hana majalisar gudanar da aikinta yadda ya kamata, da kuma nada mukarrabai a gwamnatin jihar ba tare da tantance su ba.
Baya ga hakan, ana kuma zarginsa da hana albashin wasu ‘yan majalisar Rivers da suka fito daga bangaren da ba na sa ba.
Har ila yau, majalisar ta bayyana cewa gwamnan ya saba ka’idojin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya gindaya kan yadda ya kamata gwamnan jiha ya tafiyar da mulki.
Zargin da ake yi wa mataimakiyar Fubara
Majalisar dokokin Rivers ta kuma zargi mataimakiyar gwamnan, Ngozi Odu, da mara wa Fubara baya wajen aikata wadannan abubuwa da suka ci karo da doka.
Ana zargin Ngozi Odu da taimakawa wajen nada jami’an gwamnati ba tare da tantance su ba, wanda hakan ya saba wa tanadin doka.
Haka zalika, majalisar ta ce mataimakiyar gwamnan na da hannu a kin biyan albashin wasu jami’an majalisar dokokin jihar.
Wannan mataki, a cewar majalisar, ya kara dagula al’amura a jihar, domin an hana wasu daga cikin jami’an gwamnati hakkokinsu.
Majalisa ta bukaci Fubara ya maida martani
A ranar Litinin, Kakakin Majalisar Dokokin Rivers, Martin Amaewhule, ya aika da wasikar tuhume-tuhumen da ake yi wa Gwamna Fubara da mataimakiyarsa.

Asali: Facebook
Majalisar ta bayyana cewa an yi zarge-zargi ne bisa tanadin dokokin Najeriya, kuma ana bukatar gwamnan da mataimakiyarsa su mayar da martani kafin a dauki mataki na gaba.
Wike ya gargadi gwamna Fubara
A wani rahoton, kun ji cewa ministan Abuja, Nyesom Wike ya ce yanzu gwamna Siminalayi Fubara ya fara ganin sakamakon abin da ya yi a Rivers.
Nyesom Wike ya yi magana ne yayin da majalisar jihar ta hana gwamna Fubara damar gabatar da kasafin 2025 yayin da ya je majalisar.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng