Dalilan Manyan 'Yan Siyasa da Suka Caccaki El Rufa'i kan Komawa Jam'iyyar SDP

Dalilan Manyan 'Yan Siyasa da Suka Caccaki El Rufa'i kan Komawa Jam'iyyar SDP

Sauya sheƙar tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, daga jam’iyyar APC zuwa SDP da kuma kiran da ya yi ga shugabannin jam’iyyun adawa su haɗa kai, ya jawo ce-ce-ku-ce.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kaduna - Wasu 'yan adawa ba su ji daɗin tayin da tsohon gwamnan ya yi masu ba, saboda ana ganin ya sauya sheƙa ne saboda buƙatarsa, ba don kishin ƙasa ba

Kaduna
Yadda wasu 'yan adawa suka soki sauya shekar El-Rufa’i zuwa SDP Hoto: Nasir El-Rufa’i
Asali: Facebook

TABLE OF CONTENTS

Legit ta tattaro martanin wasu daga cikin 'yan siyasa da masu ruwa da tsaki a Kaduna kan kiran jama'a su dunguma cikin SDP domin kayar da gwamnatin APC a zaben 2027.

1. Yadda Sule Lamido ya caccaki El-Rufa'i

Tsohon gwamnan Jihar Jigawa kuma jigo a jam’iyyar PDP, Sule Lamido, ya yi watsi da kiran Nasir El-Rufa’i, yana mai cewa ba shi da wata hujja da zai ce ‘yan adawa su bar jam’iyyarsu

Kara karanta wannan

El-Rufa'i: "Kwangilar Tinubu Uba Sani ce ya karbo domin karya ni a siyasa"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

BBC Hausa ta ruwaito cewa Lamido ya zargi tsohon gwamnan da sauya sheka saboda son zuciya, tare da bayyana cewa hakan ba zai sa a tumbuke gwamnatin APC a 2027 ba.

Ya kara da cewa:

"Yanzu ba don raini ba, saboda Allah, ya zai kalle mu a PDP ya ce zai kira mu wata jam'iyyar siyasa. Jam'iyyar da muka yi ta PDP ita ce ta haife shi."
"Duk rikicin da PDP take ciki, a nan aka haife shi. Idan ya ce PDP ta mutu to a nan ne asalinsa, nan ne aka haife shi."

Haka nan, Lamido ya soki salon mulkin El-Rufai, yana mai cewa shugabanci ya kamata ya kasance bisa hakuri da kishin kasa, ba bisa son rai da fushi ba.

2. Buhari ya badawa El-Rufa'i kasa a ido

Jim kadan bayan ya sauya sheka zuwa SDP tare da neman manyan 'yan siyasa su bi shi, Nasir El-Rufa'i ya ce sai da ya samu albarkar tsohon shugaban kasa kafin ya fice daga APC,

Kara karanta wannan

'Ka yi kadan': Sule Lamido ya mayar da martani ga El-Rufai game da kalamansa

Wannan ya jawo martanin Muhammadu Buhari, inda ya nesanta kansa da sha’awar wata jam’iyya da ba APC ba har abada, kamar yadda The Cable ta wallafa

Sanarwar da mai magana da yawun shugaban kasar, Garba Shehu ya fitar ta ce:

""Ni dan jam’iyyar APC ne, kuma ina so a rika kiran ni da haka. Zan yi iya kokarina wajen kara karfafa jam’iyyar ta kowane hali."

3. Omokri ya fusata da kalaman El-Rufa'i

Tsohon mai taimakawa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan, Reno Omokri, ya yi kakkausar suka kan sauya shekar El-Rufai.

Ya ce tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ci gaba da kasancewa mai biyayya ga APC, wanda hakan ya saba da ikirarin El-Rufai cewa yana da goyon bayan sauya shekarsa.

Omokri ya ce:

“Ra’ayina kan Janar Muhammadu Buhari ya sauya zuwa mafi kyau bayan da ya fitar da sanarwa yana jaddada biyayyarsa da kuma amincinsa ga jam’iyyar APC, ya na nesanta kansa daga Nasir El-Rufai.”

Kara karanta wannan

El Rufa'i ya fadi matsayarsa kan takara da Tinubu a zaben 2027

4. APC ta yi wa El-Rufa'i tatas

Jam’iyyar APC ta yi watsi da sauya shekar El-Rufa’i, tana mai bayyana hakan a matsayin wani lamari da bai taka kara ya karya ba.

Nasir
'Yan adawa sun soki El-Rufa’i Hoto: Nasir El-Rufa’i
Asali: Facebook

Sakataren APC na Kaduna, Yahaya Pate, ya ce jam’iyyar ba ta damu da wannan mataki na El-Rufa'i ba, yana mai cewa:

“Ba mu damu da sauya shekar tsohon gwamna Nasir El-Rufai ba... Abin da ya fi damun mu shi ne mu ci gaba da tabbatar da nasarar jam’iyyar a Kaduna da kuma tabbatar da nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Uba Sani a 2027.”

5. Ra'ayin matashin PDP kan shigar El-Rufai SDP

Matashin dan siyasa kuma tsohon mai neman kujera a majalisar dokokin Kano, Adnan Mukhtar TudunWada, ya shaidawa Legit.ng cewa.

"Ina ganin shigar El-Rufai SDP ba ya yi ba ne don talaka, sai dai don ba shi da makoma a APC.
Mutumin da ya ce dole mulki sai ya koma Kudu, duk da cewa ba abu bane rubutacce a tsarin mulki, ai shi mulki adalci ake bukata ko daga ina mutum yake."

Kara karanta wannan

Siyasa mugun wasa: El Rufa'i na fatan Atiku da Obi su hade da shi a SDP

Ya kara da cewa:

"Sannan da Tinubu ya ba shi mukamin Minista, me yasa bai yi watsi da shi ba? Wannan duk ihu ne bayan hari.
Ya fara wannan surutan ne da sukar gwamnatin Tinubu saboda bukatarsa ba ta biya ba a APC, kuma PDP ba guri ba ne."
"Ba El-Rufai ya kamata abi ba. Nima ina goyon bayan hadakar jam’iyyun adawa, amma ba irin wacce El-Rufai yake so ba, ta jawo mutane su bi shi ."

Uba Sani ya yi martani ga El-Rufa'i

A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya jaddada cewa burinsa shi ne gudanar da mulki yadda ya dace, ba biye wa surutan da wasu 'yan siyasa ke yi ba.

Duk da cewa bai ambaci suna ba, furucin gwamnan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Nasir El-Rufa’i, ya zarge shi da amfani da ‘yan sanda don tsoratar da magoya bayansa.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng