Kwanaki da Sauya Shekar El Rufa'i, Ana Ganin Alamun Rigimar Takarar Shugaban Kasa
- Tsohon dan takarar jam’iyyar SDP, Adewole Adebayo, ya yi watsi da batun kawancen jam'iyyu, tare da bayyana aniyar tsayawa takara a 2027
- Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i wanda ya koma jam'iyyar a kwanakin nan ya yi batun samar da hadaka domin fatali da APC a zabe mai zuwa
- Duk da kin amincewa da hadakar jam’iyyu, Adebayo ya jinjina wa El-Rufa’i, yana mai bayyana shi a matsayin ɗan kishin kasa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja — Adewole Adebayo, dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar SDP na shekarar 2023, ya bayyana kudirinsa na sake tsayawa takara a 2027.
Jawabinsa na zuwa ne yayin da ake fuskantar sauye-sauyen siyasa, musamman bayan tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya fice daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa SDP.

Asali: Facebook
A zantawarsa da Arise TV a ranar Juma'a, Adebayo ya bayyana cewa jam’iyyar SDP ba ta wata tattaunawa da wata kungiya game da hadaka da wata jam’iyya kan 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Dan takarar SDP ya magantu kan hadakar jam'iyyu
Jaridar The Cable ta wallafa cewa Adebayo ya jaddada cewa SDP za ta ci gaba da zaman kanta tare da aiwatar da manufofinta gabanin zaben 2027, ba wai shiga hadaka da wasu jam'iyyu ba.
Ya fadi haka ne a lokacn da ake rade-radin cewa tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, na iya komawa SDP ko a samar da hadakar jam'iyyu.
'Dan takarar SDP bai karbi shawarar El-Rufa’i ba
Tsohon gwamnan Kaduna, El-Rufa’i, ya bayyana bukatar hadaka domin kawar da gwamnatin Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Sai dai Adebayo ya yi watsi da wannan shawara, yana mai cewa shugabancin SDP bai fara gudanar da irin wannan tattaunawa ta kawancen jam'iyyu ba.

Kara karanta wannan
'Ku biyo ni TikTok': El-Rufai ya bude shafinsa, ya tara dubban mabiya cikin sa'o'i 24

Asali: Facebook
Ya ce:
"Batun hadaka ba shi ne manufar jam’iyyarmu ba; watakila wasu na tattaunawa a waje. "Ba mu da wata matsala a cikin jam’iyyarmu.
Lokacin da ake bayar da mukamai, ba mu shiga ciki ba, mun tsaya a inda muke. Idan kana da tsayayyen tsari, mutane za su zo gare ka.
Abin da muke kokarin yi shi ne tabbatar da cewa matsalolin da suka tilasta wasu barin jam’iyyarsu ba su shafi SDP ba."
Tsohon dan takarar SDP ya nanata bukatarsa
Adebayo ya bayyana cewa manufarsa ta sake tsayawa takara a 2027 ba sabon abu ba ne, kuma ‘yan jam’iyyar sun sani tun tuni.
Ya ce:
"Duk wanda ke shigowa jam’iyyarmu ya san cewa zan tsaya takara a 2027. Ko ‘yan jam’iyyata sun sani. Akwai tsarin girma a jam’iyya."
"Idan ka shigo SDP, za ka zo ne domin koyon tsarin jam’iyyarmu. Watakila ka riga ka san siyasa a wani wuri, amma idan ka zo, za ka fara daga tushe kamar kowane mamba."
'Dan takarar SDP ya yabi El-Rufa’i
Duk da cewa ya yi watsi da batun hadaka, Adebayo ya yaba da sauya shekar El-Rufa’i zuwa SDP, yana mai bayyana shi a matsayin “kwararren mai gudanarwa.”
Ya ce:
"Ina ganin El-Rufa’i a matsayin mutum mai basira da hazaka idan aka ba shi aikin shugabanci. Duk da cewa yana da rauninsa."
"Dalilin da ya sa na karbe shi cikin jam’iyyarmu shi ne saboda ina ganinsa a matsayin ɗan Najeriya mai kishin kasa, mai kwazo da aiki tuƙuru a lokacin da ba mu da mutane masu inganci a gwamnati."
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng